Siyasar Kasa Ba Ta Dauke Hankalina  Wurin Tafiyar Da Gwamnatin Sakkwato Ba---Tambuwal

Siyasar Kasa Ba Ta Dauke Hankalina  Wurin Tafiyar Da Gwamnatin Sakkwato Ba---Tambuwal

 

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa tafiyar da gwamnatinsa bai samu cikas ba domin yana cikin siyasar kasa dole ne a yi tsammanin shigarsa a harkokin siyasa a matakin kasa in bukatar hakan ya taso ganin ya taba zama mutun na uku a tsarin shugabancin Nijeriya.

Tambuwal a hirarsa da jaridar daily trust ya ce "ina matukar kokarina a matsayina na gwamnan Sakkwato kan aikin da aka daura min, ba wani hauji a gwamnati dake samun ci baya saboda shiga ta harkokin siyasar kasa, wannan shi ne abu mafi muhimmanci, in akwai yakamata su fitar da shi fili a sani."

Tambuwal ya ce a halin yanzu da ake samun cigaban wayewar zamani kana iya gudanar da gwamnati ko ba a ganinka a zahiri, hakan duniya ta sa gaba a yanzu, komi na tafiyar da gwamnati a Sakkwato ba abin da yake ja baya.
Tambuwal ya yi tambaya ga masu korafin yawonsa, shin akwai abin da ya tsaya? ya ce ya tabbata yana iya kokarinsa a matsayinsa na gwamnan Sakkwato a lokacin da ya bayarda hankalinsa ga wasu abubuwa da suka shafi kasa.