Sanata Wamakko Ya Tura Sako Ga 'Yan Siyasar Sakkwato Da Suka Yi Zamansu Abuja

Sanata Wamakko Ya Tura Sako Ga 'Yan Siyasar Sakkwato Da Suka Yi Zamansu Abuja

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya tura Sako ga 'yan Siyasar Sakkwato da suka yi zamansu Abuja ba su dawowa cikin al'ummar da suka zabe su alhali mutane na cikin bukatar tallafi ga wakillan nasu.
Sanata Aliyu Wamakko a wurin kaddamar da rabon takin zamani buhu dubu 100 ga manoma a kyauta wanda gwamnatin jiha ta samar ya nuna damuwarsa ganin halin da mutane suke ciki amma wakilan da suka zaba sun wofantar da su.
Ya ce wakillan da Sakkwatawa  suka zaba su dawo su taimaki al'umma ana bukatar abinci da sauran bukatun rayuwa.
Sanata Wamakko ya yabawa gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto kan aiyukkan cigaba da ta samar a cikin kwana ki 100 na mulkinta. 
"Gwamnatin Ahmad Aliyu ta yi abubuwan cigaba da ba a yi zato ba a cikin kwana 100 kamar samar da hanyoyin mota da samar da ruwan sha da bunkasa harkar noma a jihar, ni manomi ne Kuma makiyayi sanya ni na na albarkaci rabawa manoma taki a kyauta abin farinciki ne gare ni Amadu Alu ya gode," a cewar Sanata Wamakko.