2023:Wike Ya Ajiye Goyon Bayansa Ga Ta Tambuwal Ya Shiga Neman Tikitin PDP

2023:Wike Ya Ajiye Goyon Bayansa Ga Ta Tambuwal Ya Shiga Neman Tikitin PDP

 

Gwamnan Rivers Nyesome Wike ya ajiye goyon bayansa ga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya shiga neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP.

Wike a 2019 ya goyi bayan Tambuwal kuma ana ganin yanda suke dasawa sabanin yanzu da suka fito neman tikiti daya wanda ake gani dukkansu dagaske suke yi.

Wike ya aiyana zai yi takararsa a garin Makurdi cikin jihar Benue bayan ya yi zama da masu ruwa da tsaki a ranar Lahadi.
Ya ce in ya samu nasara zai dawo da tsaro da bin doka a cikin Nijeriya. 
Ya ce shi kadai ne ke iya kwatar mulki ga hannun APC don haka a bashi dama.