ƘUNCIN RAYUWA: Labarin Tausayi

ƘUNCIN RAYUWA: Labarin Tausayi

ƘUNCIN RAYUWA
Ruƙayya Ibrahim lawal
08109634202

Tsakar gidan cike yake maƙil da mata, sun yi zaune jugum-jugum, sai wani Magidancin dake zaune a gefe suna gaisawa da wata Dattijuwa. Da alama dai gidan mutuwa ne.
Wata matashiya 'yar shekaru ashirin da uku ce ta fito daga cikin ɗaki bako Hijab a jikinta, tafe take tana layi, har ta iso inda suke. Ta cacumi wuyan wancan mutumin cikin muryar 'yan maye take cewa "Na tsane ka Abba! Sai na kashe ka kamar yanda ka yi silar mutuwar Mahaifiyata." Mutane ne suka taso aka rirriƙe ta, da ƙyar aka janye ta daga cukuikuyar da ta masa. Har zuwa lokacin bai ce komai ba girgiza kai kawai ya yi, ya fice daga gidan yana zubda ƙwalla a ransa ya na cewa 'Shi ya sa yana da kyau idan kana Sara ka dinga duba bakin Gatari, na ɓata rawa ta da tsalle ga shi yau ina nadama mara amfani, Kaicona!.'

"Zaliha kina cikin hayyacinki kuwa? Abbanki ne fa kika ma haka." Wata daga cikin manyan matan gurin ta faɗa.

Zara'u ce ta miƙe ta janye Zaliha zuwa ɗakinsu, yayin da take faɗar "Ki bar ni da mutumin banza sai na koya masa hankali."

Kwantar da ita kan gado Zara'u ta yi ta ce "Shii! Don Allah ki yi shiru Zaliha, me ya saka kika sha kayan maye ana tsakiyar karɓar gaisuwar mutuwar mahaifiyarki? Shin baki yi imani da ƙaddara ba ne?"

Kai kawai ta girgiza ta kwanta sai barci. A haka aka watse taron addu'ar Ukun Hajiya Fahima mutane nata tsinewa hali irin na Zaliha da ta mayar da kanta 'yar maye.

Ranar a gidan Zara'u (Ƙawar Zaliha tun suna primary) ta kwana, domin ba zata iya barin ƙawarta a wannan yanayin ba.

Ƙarfe goman dare Zaliha ta farka daga dogon barcinta. Ganin haka ya saka Zara'u ta matso ta ce "Zaliha kin tashi?" Ba ta jira amsa ba ta ce "Dama ina so mu yi magana ne."

Gyara kishingiɗarta ta yi sannan ta ce "ina jinki."
"Zaliha ki ji tsoron Allah ki daina wannan shaye-shayen naki, baya daga cikin ɗabi'u nagari. Shan kayan maye haramun ne kin sani sarai kuma.
Amma don Allah meye dalilin da ya saka kika jefa Rayuwarki cikin wannan mummunar ɗabi'ar?." Zara'u ta ƙarashe zancen da tambaya. 

Hawaye suka fara bin kuncinta yayin da ta buɗi baki ta ce "Zarah ki mun alƙawarin ba wanda zai ji sirrina, ke ce mutum ta farko da zan bayyanawa mummunan sirrin gidanmu."
Gyaɗa mata kai kawai ta yi alamun ta yi alƙawarin.
Ita kuwa ta ci gaba da cewa "Damuwa da ƙuncin rayuwa ne ya jefa ni a halin shaye-shaye da ƙarancin shekaruna, amma Mahaifina shi ne silar komai shi ya sa ba zan taɓa yafe masa ba har Abada."
Sauke ajiyar numfashi ta yi sannan ta ci gaba "A yanda aka san Uba nagari ba zai juri ganin an wulaƙanta masa 'ya ba ta hanyar ke ta mata haddi, sai ga shi nawa Mahaifin shi ne mutum na farko da ya keta mun haddi."
Zara'u ta zazzaro ido tare da rufe baki, alamun abun ya firgitata matuƙa.
Zaliha bata damu da hakan ba ta ci gaba da ba ta labarin cikin Muryar kuka.
"Wannan mummunan labarin ya fara ne a lokacin da na kammala ƙaramar sakandare kafin in ci gaba da karatu, watarana Ummanmu ta yi tafiya ta kwana biyu, ina kwance a ɗakina ya shigo, kamar yanda ya sabar mana da guduna na zo na rungume shi ina faɗar 'Abbana sannu da dawowa.' Shi ma ya rungume ni sosai a jikinsa yana faɗar 'Yawwa sweet daugtherna' cikin wata iriyar murya ya yi zancen. Da farko ban damu ba kasancewar kowa yasan gidanmu ya san wannan daɓi'ar gidanmu ce abbanmu ya sangarta mu da yawa. Sai dai me? Jin da na yi ya na ƙoƙarin wuce gona da iri ya saka hankalina ya tashi. A nan na yi ta roƙonsa ina ba shi haƙuri cike da tashin hankali, amma hakan bai saka Abbana ya tausaya mun ba duk da ƙananun shekaruna a lokacin, ya manta cewa ni 'yar cikinsa ce kuma ta fari a gunsa. Sai da ya cika burinsa a kaina sannan ya fita."
A ranar na ci kuka har na ba uku lada, na yi ta tsinewa halinsa, tun daga ranar na tsane shi, haka na hanawa ƙannena kula shi kamar yanda muka saba. Ummanmu da ta dawo ta tarar da sauyi a cikin gidan, inda ta tarar na daina kula Abba ko gaida shi ma bana yi sai harararsa kawai nake, ta yi faɗan ta gaji har dukana sai da ta yi amma a banza. Tun daga lokacin ya maida ni tamkar matarsa, ko da yaushe sai ya ƙirƙirarwa Ummanmu tafiya har ta rashin dalili, idan ta tafi sai ya zauna da ni. Na rasa yanda zan yi, rayuwata ta shiga ƙunci ga shi gidanmu muna da wadata ba rashin ci, sha bare sutura amma sai daɗa lalacewa na ke. In gajarce miki labarin bayan kamar wata shida ya na tare da ni watarana na samu sa'arsa na fasa masa kai da kwalba na zazzage shi tare da ja masa Allah ya isa. Tun daga ranar ne ya daina kula ni sai ya koma kan ƙanwata mai bi mun Zainab dama mu Uku ne 'yan mata, mu kaɗai kuwa iyayen namu ke da.
Ita ma Zainab haka ya maida ta tamkar yanda ya mun, sai muka zama mu biyu ne a gidan masu hantararsa. Ummanmu da ta ga abun bana ƙare ba ne. watarana ta ritsa mu a ɗaki kan cewa lallai yau sai mun gaya mata gaskiya. Sai da fatarmu ta yi laushi  tukunna muka faɗa.
Hankalinta ya tashi matuƙa da farko ta so ta ƙaryata mu, akan cewa mijinta Salihi ne ba zai taɓa aikata haka ba, bayan ta yi dogon nazari sai ta yanke hukuncin gwada shi.
Watarana bayan ta tabbatar masa da ta yi tafiya ta juyo sai kuwa ta kama shi dumu-dumu yana aikata alfasha da 'yar cikinsa Zainab. Suma ta yi a ranar."
Shiru ta yi tana sauke ajiyar zuciya, ita kuwa Zara'u kuka take sosai, wannan rayuwa dame ta yi kama? 'Yar cikinka zaka haiƙewa? 'Duniya ina zaki damu?' Ta faɗa a ranta.
Bata gama jimami da mamaki ba ta jiyo muryar Zaliha na ci gaba da labarin.
"To tun daga lokacin ne rayuwar gidanmu ta shiga ƙunci, Ummanmu ta daina kula shi, muma ƴaƴansa haka, hakan ya saka shi yin fushi ya tsallake mu ya koma Abuja ya yi zamansa. A Lokacin ne muka shiga tashin hankali fiye da da, ga shi ya riga ya saka ni makarantar kwana kafin ya tafi, wai don ya mun wulaƙanci. Abincinmu ya zo ya ƙare, sannan tun da ya tafi ko ƙwandalarsa bai turo mana ba, hakan ya saka Ummanmu ta yanke shawarar Fara sana'ar kayan sanyi na sha don dogaro da kai. Ai kuwa wannan sana'ar ta rufa mana asiri sosai tunda har zuwa lokacin ba wanda ya gano ɓarakar dake cikin gidan."
Tana zuwa nan ta yi shiru.
"Sai me ya faru?" Zara'u ta tambaya.
"A wani hutun ƙarshen shekara lokacin ina aji Biyar, na dawo gida na tarar da mummunan labarin da ya gigita duniyata, wai masu garkuwa da mutane ne suka zo har gida a zatonsu Abba yana nan, domin ya zo kwasar sauran abubuwansa, kwana ɗaya ya yi ya juya, a ranar da ya tafi suka zo, ganin ba su tarar da shi ba, bayan suna da yaƙinin ya zo, hakan ya saka suka ɓalle ɗakinsa suka saci abinda ya rage, sannan suka yi garkuwa da autarmu Fatima.
Tun a ranar Umma ta kira shi a waya ta sanar masa amma ko gezau bai yi ba, sai ma tsaki da ya ja ya kashe wayar.
Bayan kwana biyu suka kira suka nemi kuɗin fansa Naira miliyan Goma, ganin ba za su samu ba, aka yi ta ciniki har suka dawo miliyan Biyar daga nan ba ragi.
Ana tsaka da hakan ne na dawo na tarar da wannan tashin hankalin. Ummanmu ta sayar da duk wani abu da yake nata ne, ta haɗa da jarin sana'arta amma ko rabin kuɗin bata haɗa ba. Ga shi daga ita sai ƙaninta suka rage a familynsu duk sun mutu.
 A kwana na biyar suka yi barazanar za su kashe ta idan aka ƙara kwana biyu ba'a fanshe ta ba. A nan hankula suka ƙara dugunzuma. Da ƙyar da siɗin Goshi aka haɗa kuɗin. Kawu Mus'ab ya kai inda suka kwatanta masa ya ajiye, sai cewa suka yi gobe ya dawo ya ɗauki yarinyar. Hakan aka yi washegari ya koma sai gawarta ya tarar, sun haiƙe mata daga ƙarshe suka kashe ta. Mun ci kuka har mun gode Allah sannan mun tsinewa Abbanmu ba adadi mun yi nadamar fitowa daga tsattsonsa. Ummanmu ta kuma kira ta sanar masa mutuwar Fatima nan ma ya ƙi zuwa, ga shi har lokacin bai saki Ummanmu ba.
Bayan komai ya lafa Umma ta lallaɓa ni na koma makaranta, don na ci gaba da karatuna sai dai damuwa ta hanani karatu, ana cikin hakane wata 'yar ɗakinmu a makaranta Abida ta ba ni totolin watarana ta ce na sha zan ji sassaucin wutar dake ruruwa a zuciyata ba musu na shanye kwalbar tas, tun daga lokacin ne kuma da na fara tunani sai na ɗaga bakin kwalba, har zuwa yanzu da na kasa dainawa."
Hawaye Zara'u ta goge ta ce "Ki yi haƙuri ƙawata komai ya yi zafi maganinsa Allah, amma ki daure ki daina wannan ɗabi'ar, wannan halin da kika jefa kanki ne ya sanya damuwa ta yiwa Umma yawa har ta kamu da ciwon zuciya ya yi ajalinta. Ga shi ke kanki likitoci sun tabbatar da kina dab da kamuwa da ciwon Hanta, ga kanki da ya fara taɓuwa. Abba kuwa ya ga sakayyar jefa ku da ya yi a cikin *ƘUNCIN RAYUWA* tunda a yanzu banda wannan gidan ba abinda ya rage masa ga raini na har Abada da ya shiga tsakaninku, idan duniya ta ji wannan al'amari tabbas sai ta tsine masa."

Daga haka suka rufe babin maganar, Zarah ta kwanta don yin barci.

Ita ma Zalihan kwanciya ta yi, sai dai ba barcin take ba, kawai tana kwance ne tana tunanin rayuwarsu ta baya mai cike da farinciki da kuma yanda a yanzu farinciki ya yi bankwana da gidan.

Washegari Zainab ta dawo gidan, dama bata nan tana gidansu ƙawarta tun lokacin da ta tabbatar da zuwan Abban nasu ta bar gidan, sai yau ta dawo a tunaninta ya tafi.

Da misalin ƙarfe goma na safe Abban ya shigo gidan.

Su Zaliha suna daga ɗaki suka jiyo muryarsa yana gaisawa da Gwaggwo (Yayarsa da ta zo daga Jos).

Zainab dake zaune ta tasa kofin shayi da biredi a gabanta tana karyawa, ta jiyo  muryarsa.

Ɗan saurarawa ta yi kaɗan domin ta tabbatar da abunda kunnenta ya jiye mata.

Yanzu kam ta samu tabbacin shi ɗin ne don haka ta Zabura da ƙarfi ta miƙe tsaye tare da duban Zaliha ta ce "Yaya dama wannan Mutumin bai tafi ba?"

Gyaɗa mata kai kawai Zaliha ta yi, tare da miƙewa ita ma suka ɗunguma zuwa waje.
Dama tun ƙarfe 8:30 Zara'u ta fice zuwa gida.

Zainab ce ta nufe shi gadan-gadan tana faɗar "Me kake zaman jira a nan har yanzu? Ina tunanin ka zo ne domin ka tabbatar da mutuwarta domin cimma muradanka to ai....."

"Ya isa haka Zainab!" Gwaggwo Mariya ta daka mata tsawa sannan ta ɗora da cewa "Mahaifinku ne, duk lalacewarsa dai baku da wani uba a nan duniya bayan shi, ki sani hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar."

Zaliha ce ta yunkuro ta tari numfashi Gwaggwon tasu da cewa "Gwaggwo ki bar ta ta faɗi son ranta ƙila hakan ya saka ta huce raɗaɗin zafin kisan mummuƙen da ya mana."

Tsawa ta daka masu dukkansu sannan ta nuna masu Wuri tare da basu umurnin zama.

Zainab da take ji tamkar ta damko wuyan Mahaifin nasu saboda tsananin jin haushinsa, ta zauna tana huci kaɗan-kaɗan, zalihar ma zama ta yi.

Gwaggwo ta ce "Kabiru! Ina so ka nutsu ka saurare ni sannan ka gaya mun gaskiyar lamari, shin abinda na ji Zaliha tana faɗa jiya gaskiya ne?"

Abban nasu da tun fitowarsu daga cikin ɗakin ya yi shiru tare da sadda kai ƙasa tamkar Munafuki sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, irin kallon nan mai nuni da neman ƙarin bayani.

"Jiya na fito daga banɗaki da dare na jiyo Zaliha tana bawa ƙawarta labarin abinda ya shiga tsakaninku, shin hakane?" Gwaggwon ta kuma tambayarsa tana tsare shi da ido.

Sosai ya fahimci me take nufi don haka ya kuma sunkuyar da kai ƙasa ya ce "Gaskiya ne yaya abunda kika ji ba wai ba inke na aikata shi, sai dai sharrin shaiɗan ne, da kuma shawarar Aboki."
Tsit gurin ya yi suna saurarensa.

"Komai da ya faru rubutacciyar ƙaddara ce da ba mai iya kankareta a rayuwar wannan Ahali, sai dai a silar shan giya ne. A wancan lokaci watarana ayyuka suka mun yawa kaina ya ɗau zafi sosai, damuwa ta shige ni, shi ne Alhaji Sadam ya bani barasa ya ce In sha zan samu relief, da farko har zan yi gardama ya dage, don haka na sha, tun daga lokacin shan barasa ya zame mun ɗabi'a daga na kwaso pressure ta sai na sha, duk wannan abun da ake iyalaina ba su sani ba, domin ban taɓa sha a gida ba sai a guest house ɗina. A cikin haka ne watarana na nufo gida ba tare da na gama warwarewa da mayen ba, dalilin hakan yasa na yi sha'awar 'yata Zaliha har na kusance ta a cikin yanayin. Da na dawo hayyacina na yi na dama sosai, sai dai kuma bayan kwana biyu na komawa turkena mai taɓo domin ban daina shan Barasa ba. Har zuwa lokacin dana gudu Abuja damuwa tamun Katutu, hakan ya saka na riƙi wannan sana'a ta shan Barasa fiye da baya, haka kuma na tsunduma cikin aikata alfasha, a nan na fara banzatar da dukiyata ina bawa yanmata.
A shekarar baya da ta gabata ciwo mai tsanani ya kwantar da ni, a garin da ba nu da kowa da zan kira nawa sai Abokai, a lokacin ne kaɗai na ji na yi nadamar ƙetare iyalaina dana yi, bayan an kai ni Asibiti likitoci suka yi gwaje-gwajensu suka tabbatarwa Abokan nawa na kamu da ciwon  Hanta ne, sai dai ciwon sabo ne a lokacin don haka suka ɗora ni akan magani. A haka na ƙarar da duka dukiyar da ta rage mun gun neman magani. Amma na sani duk daren daɗewa watarana zan mutu, kuma ina ji a raina wannan ciwon ne ajalina domin kuwa duk wanda ya ƙetare iyakokin Allah dama ƙarshensa nadama."

Yana zuwa nan a labarinsa ya yi shiru, tsakar gidan ya yi tsit na 'yan wasu daƙiƙu.

Zaliha da Zainab ko kaɗan ba su ji tausayinsa ya ɗarsu a ransu ba, dalilin ke nan da ya saka ko da ya nemi yafiyarsu suka kasa yafe masa.

Gwaggwo Mariya da jikinta ya gama yin sanyi ƙalau, ta kalli ƙaramin ƙanin nata ta ce "Ga irinta nan, ƙalubalai ga ire-irenku masu bin zuga da shawarar Abokanai, ga shi silar hakan ka gurɓata Addininka da tarbiyyar yayanka. Shin ina hankalinka ya je ka manta da faɗar Allah maɗaukakin sarki a cikin suratul Ma'ida aya ta 90 'bismillahir-rahmanirrahim, Ya ayyuhalladhina Amanu Inna mal Khamru Wal Maisiru, Wal Ansabu,  Wal Azlamu Rijisun min Amalish-shaiɗan, fajtanibuhu La'alla kum Tuflihun.
Ma'ana
Ya ku waɗanda suka yi Imani, haƙiƙa giya, da caca, da gumaka, da kibiyar neman sa'a, Ƙazanta ne daga cikin ayyukan shaiɗan, ku nisance su ko da za ku samu rabo.' haka kuma Manzo (s.a.w) ya ce "Mutum uku ba su shiga aljanna, Mai saɓawa iyayensa, da mai kwankwaɗar Giya, da mai Gori."

Shiru ta yi na wasu 'yan daƙiƙu, sai a lokacin Zaliha ta cafe zancen da faɗar "Tabbas ka kassara mana rayuwa ta dalilin ƙetare iyakar Allah." Wasu hawaye ne masu zafi suke bin kuncinta.

Shi kam Alhaji Kabiru ba baki sai kunne, hawaye kawai yake.

A nan dai Gwaggwo ta sulhunta su, ta ƙara neman masa gafara a gurin ƴaƴansa, sannan ta tunatar da su akan yarda da ƙaddara yana daga cikin shika-shikan Imani.
A haka suka watse kowa zuciyarsa ba daɗi, bayan kwana biyu da yin wannan zancen, ciwon Alhaji Kabiru ya tashi kuma ya tsananta, haka a ka ɗauke shi zuwa Asibiti rai a hannun Allah.

Yayarsa ce ke jinyarsa, duk ya kumbure cikinsa ya cika kamar zai fashe, duk mai imani idan ya ga halin da yake ciki sai ya tausaya masa. ƴaƴansa ko Asibitin basa zuwa sai sun ga dama bayan ya yi jinyar sati ɗaya ya ce ga garinku.

A lokacin ne ita kuwa Zaliha   taɓuwar kan nata ya ƙaru, sai faɗar ta ke "Abba ka mutu mun huta, idan ka isa ka gaida Umma ka ji tsohon najadu?" Ganin hakan ya saka a ka miƙata asibiti mafi dacewa da ita.

Ƙarshe