ANA BARIN HALAL....:Fit Ta 30

ANA BARIN HALAL....:Fit Ta 30

ANA BARIN HALAL....:

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE


*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*

08064586559


*PAGE* 30

**********
Gaskiya rashin iyaye wani abu ne mai ciwo da babu kwatankwacin shi, duk da babu sabo ko shaƙuwa a tsakanina da Alƙali, amma tabbas rashin shi ya buge ni, bugu ma bana wasa ba, domin ɗan zaman da nayi da shi a halin rashin lafiya na kwana biyu, sai naji kaman tunda na fara rayuwata muke tare, naji ciwo naji ciwon rashin mahaifina, ina tsaye duk iyalen Baba Alƙali suka shigo asibitin, kowa ka gani kuka yake, Aunty umatiti ne ta rungumeni tana kuka, amma haka dai ina tsaye ban iya komai ba, gari ya fara haske sai ga yayah rabiu ya iso duk a firgice, wurina ya taho ya riƙoni jikin shi, sai lokacin naji nayi wani ajiyar zuciya, wanda ya ɗan lafar da turirin da zuciyana yakeyi, yayah rabiu ne ya taya ƴan'uwa na da maxajen su aka gama komai aka ɗauki gawan Alƙali sai bauchi.

Yayye na babu wanda bai ƙira wayana ba, amma nakasa iya ɗauka, nidai har zuwa wannan lokacin babu wani kalma da ya fito daga bakina, babu wani hawaye da ya zubo daga idona, ganin bana ɗaukan wayan ya saka yaya rabiu ya amshe wayata ya kashe, don ko ƙiran A.G ma kaɗai ya isa a kashe wayan, muna isa ƙofar gidan naga mutane maƙil a ƙofar gidan, haka dai muka sauƙo iyaye mata da yayye na suka shige cikin gidan,  mu kuma muka fara ƙoƙarin fito da gawan, ana fito da shi ƴaƴan shi da ƙannen shi suka shige da shi cikin gida, amma ni sai na tsaya a waje tare da yayah rabiu da su yayah hassan da hussain, muna tsaya anan waje muna ta gaisawa da jama'a, duk da dai ni kan kaina a sunkuye yake a ƙasa sai su yayah ne ke amsa gaisuwan, muna haka chan wani ƙanin mahaifinmu ya fito daga cikin gida wurin da ake yiwa Baba Alƙali wanka, har inda muke tsaye yazo ya tsaya,   "mukhtar ka shigo kayiwa mahaifinka addu'a",  kallon shi nayi zuciyata tana wani irin tafasa, wai na shigo nayiwa mahaifina addu'a? Yana raye basu yi sanadin na shigo ba sai da ya bar duniya? Aiko bazan shiga ba, girgiza kai nayi alaman a'a, duk kallo na suka tsaya sunayi, daga nan naga yayah hassan ya wuce zuwa gidan mu, haka mutane suka taro a kaina suna magiyan na shiga, amma tunda na sauƙe kaina ƙasa ban sake ɗagowa ba, ballantana wani yayi tunanin zan ji kunyar shi nayi abunda suke so, bawai ban yafewa Alƙali bane ko banji nasihar shi ba, a'a gidan ne kawai da sukayi sanadin rashin shiga na tun yana da rai nake jin bazan shiga ba, ae baya raye, abunda suke ƙulafucin an bar musu,  kafaɗa na naji an dafa, ko ban juyo ba nasan hannun goggo ne, lokaci ɗaya na sauƙe ajiyan zuciya, batace mun uffan ba ta saka hannunta ta riƙoni har zuwa cikin gidan inda aka keɓe ta varender baya na side ɗin Alƙali, binta nayi babu musu har inda gawan yake, bayan mu kuma yayu na suke biye da mu, ko wanne a cikin su ka kalli fuskan shi kuka yakeyi amma banda ni.

Har gaban gawan mahaifina goggo ta mun rakiya, dukkan ahalin shi suna wurin, matayen shi, ƴaƴayen shi maza da matan su, yayunshi da ƙannen shi, jikokin shi da aminan shi duk suna wurin, da yake wurine mai gurman gaske, hatta surakunen shi suna tsattsaye a wurin, tsugunar dani goggo tayi a gefen yayuna maza wanda suke durƙushe a daidai kanshi suna mishi addu'a.
Addu'a sosai goggo ta mishi, ta ƙira sunan shi ta tabbatar mishi da duk wani abu daya faru ta yafe mishi, hajiya da wasu daga jama'an wurin sai da sukayi kuka lokacin da ta ɗago hannuna ta ɗaura a kanshi, tace, "Abdullahi rahmar Allah ta isar maka har kabarinka, halayen ka nagari, da jinƙan ka da kyautatwa talakawa dana ƙasa  da kai Allah ya kai rahmar kabarinka , Allah ya haɗaka da mala'ikun rahma, Allah ya baka ikon amsa tambayoyin kabari, ga ɗanka Mukhtar ya yafe maka, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, sai lokacin naji kukan gaske mai ƙarfin gaske yazo mun, abunda ya tokare ni a ƙirjina naji ya wuce kaman na haɗiye abu, ina kuka ina mishi addu'a, gaba ɗaya iyalen shi sai suka fashe da kuka, lokacin da nace na yafe mishi Allah ya jiƙanshi, sai naji yayah safiya ta runguma ni tana Alhamdulillahi, Allah ya maka albarka mukhtari, wannan lokacin dai nima dawowa nayi layin ƴan'uwa na mata, don da ƙyar su yayah hassan suka ɓanɓareni daga jikin gawan Baba nah lokacin da za'a fitar da shi, nayi kuka kaman numfashi na zai ɗauke.

Muna futowa aka saka shi a motan ɗaukan gawa, haka dukkan mu ƴaƴan shi da ƙannen shi muka shige wannan motan, ina zaune dai-dai ƙafafunshi, sai hawaye nake sharewa, mu muka sakashi a kabarin shi, muka kuma zuba mishi ƙasa, lokacin da aka kammala komai aka fara shirin juyowa sai naji hankalina yayi masifaffen tashi, tunani na yanzu fa za'a zo fara mishi tambaya, kuma tsakanin bawa da ubangiji shi kaɗai yabarwa kanshi sani, tsakanin bawa da bawa shine abun tsoro, Baba nah ya samu yabo a wurin jama'a, tou tsakanina da shi fah sai Allah ya iya kama shi fah? Duk da naji a zuciyata ni na yafe mishi, kuma dama ban tashi da wannan ciwon azuciyata ba saboda uwa ta gari danayi dace da ita, amma sai naji tsoro ya kamani, bansan lokacin da nasake furta, "Baba nah nayafe maka, na yafeka Babana har abadan",  da sauri naji wani ƙanin shi ya rungumo ni yana kuka, sai yayah rabiu ma ya kamoni yana kuka muka fara tafiya, muna zuwa wurin shiga mota Alhaji Inuwa ya riƙo ni muka shi motan shi, nayi kuka a motan kaman zan shiɗe, bai bani haƙuri ba bai kuma hanani ba, sai baya na dayake ɗan bubbugawa kaɗan kaɗan har muka isa gida.

Nidai ban sake jin sha'awan na shiga gidan ba, don ko gaisuwa da ake shiga ayi acikin gidan wa iyalenshi ni ban shiga ba, inda Alhaji Inuwa ya zauna nan muka zauna nida ƴan'uwa na da suke taya ni jimamin rashin da aka mun, nidai ko kallon mutane bana yi, na sunkuyar da kaina ƙasa ina yiwa mahaifina addu'a.

Wuraren bayan sallan la'asaar sai ga A.G nawa ya iso tare da barr Ahmad, wanda ranan shine rana ta farko da muka fara haɗuwa da shi, kawai dai munyi sabo ta waya ne, tun isowar A.G naji wani sabon kuka ya taho mun, shima zuwa yayi ya riƙe hannu na, da ƙyar bakin shi ya furta, "sorry" daga nan bai sake iya yace komai ba, sai hawaye da yake ta sharewa.
Bayan anyi sallan ishaa muka shige cikin gidan mu wurin Goggo na, lokacin da mukaje na kalleta sai naji wani sabon tausayinta ya kamani, Allah sarki Goggo dukkan ƴaƴanta yau sun zama marayu babu iyaye maza, goggo na taga rayuwa a cikin rayuwarta, gaba ɗaya sai naga ta zabge wanda har girmanta ya bayyana kanshi sosai, kanta a ƙasa ta amsa gaisuwan mu, ina hankalce da ita yadda duk bayan wasu mintuna sai ta goge hawaye a idon ta, gefen ta na koma na zauna, a hankali na saka hannu na riƙo nata da ta ɗaga zata share hawayenta, kasa ɗagowa tayi ta kalle ni tayi, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗa na tana kuka,  "sannu mukhtar, sannu da rashin da aka yi mana yau, na tausaya maka na tausayawa kaina auta nah, zuciyata tana mun ciwo auta na, baka san daɗin mahaifi ba, baka raɓe shi ba har ya bar duniya, wannan wacce irin rayuwa ne muke ciki? Allah ya jiƙan Alƙali, Allah ya gafartawa malam Garba, Allah ya kai hasken kabarin su gabaki ɗaya",  rungumeta nayi ina kuka a hankali, shiru parlon yayi banda sheshsheƙan kukan mu dukkan mu baka jin komai, a hankali A.G yazo ya rarrashi goggo tayi shiru, sannan ya riƙo hannuna muka fice a parlon muka wuce gidan su, nidai ranan sai bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni.


********
Bayan anyi bakwai kowa ya watse, a washe garin rasuwar kuma yayah sanie ya iso, da yake raunin shi mai yawa ne, kuka ya dinga yi kaman mace, kada ki manta Ayshaa kinsan ko ba matsayin mahaifina Alƙali yake ba dama ɗan'uwan Baban su ne, saboda haka sun haɗa abu dayawa da Alƙali wanda dole suji mutuwar shi, don ko irin yadda aka tarwatsa rayuwar mu aka raba tsakanin mu yaci ka tausaya mun wannan rashin, ballantana kuma suma Bappan su ne kuma mijin mahaifiyar su, kuma mahaifina, Ayshaa ranan da Alƙali ya rasu sai Allah ya haɗa idanuna da wannan mai tuwon gidan alƙali wanda ta kwaɗa mun itace a baya, ganina a cikin gidan duk sai ta ruɗe, ranan uku tazo zata shiga gidan har ƙasa ta kai tana gaishe mu, nidai amsa mata kawai nayi na juyar da kaina, gashi ta manyanta lokacin, don ta kai goggo a shekaru, dama lokacin mijinta ya rasu ne tafara aiki a gidan mu, tun bayan anyi auren Alƙali da maman su umatiti kaɗan tazo gidan, shiyasa nasu ya zamo ɗaya, domin kowa gwana ce a munafurci, wajen zuwa tsubbu kuma nasu yazo ɗaya da mahaifiyar su Tijjani, don a wurin tane muka samu ƙabarin yadda akayi aka shiga tsakanin Alƙali da goggo, da ni kaina,, zanin Goggo da tayi shanya suka yanka, akwai wani malami ko bokan su zance a garin Dass, shi ya musu aikin da aka shiga tsakanin Baba Alƙali da Goggo na har abada, alokacin har abun cikin sai da akayi aikin rabasu, wato ni, kuma ta zaga ta gayawa maman su umatiti, ita dai tace neran ta bazaiyi kuka a wurin neman asiri ba, amma tunda sun fara ita zata taimaka musu da bakinta, kuma haka akayi ga asiri ga munafurci da akai ta haɗawa Goggo har sukayi nasara ba don Allah ya fi son su ba, sai don jarabawa na dana Goggo a haka yazo, su kuma Allah yana musu talala.


Bayan anyi arba'in ɗin Baba na suka ɗago maganan rabon gadon shi, haka suka tsaya tsawon sati guda suna harhaɗa abun da ya bari, nidai babu irin neman da basuyi mun ba amma naƙi zuwa, lokacin da Yayah safiya ta matsa mun da ƙira sai nace na wakilta mijinta a nawa, don ko dasuka nemi goggo itama baya na ta bi, yayah auwal nema da ya ƙirani bayan arba'in nake gaya mishi yadda mukayi da su, shiru yayi kaman baxai ce komai ba, sai chan daga baya yace,  "auta kodai baka yafewa Baba bane"?
"Subhanallahi, yayah ae ni ban taɓa riƙe shi da zafi a zuciyata ba, kullum goggo kyawawan halayen shi take sanar mun har na girma, bata taɓa aibanta shi ba yayah, ko ita tace mun ta yafe mishi ballantana ni da yayi sanadin zuwa na duniya? Wallahi ba haka bane, kawai dai naga saboda gado dama suka raba ni da shi, tou ni narayu da wuya da daɗi, gado kuma suje ni sadaka ma zanyi wanda zai isarwa Alƙali har kabarin shi".
Ajiyan zuciya yayah ya sauƙe, sannan yamun fatan alkhairi sosai, ya kuma mun nasiha, wanda kullum tsakanin mu sai ya mana.


Lokacin da aka gama rabon gadon shi kowa ya tashi da abunda Allah ya hukunta iya rabin shi ne, Alƙali jinya ta cinye kuɗin shi, sannan kadarorin shi su Tijjani sun sayar, abun da yayi saura gidan shi ne, sai wasu filayen shi da suke chan bayan gari, sai motocin shi guda biyu, sai wani gidan hayan shi ɗaya da yake dutsin tanshi, haka aka raba gado kowa ya karɓi rabon shi, lokacin da mijin yayah safiya ya ƙirani, tare mukaje da yayah Rabi'u, bayanin komai ya mun, ya kuma gaya mun abunda yake nawa rabon, acikin gidan mu side ɗin Baba na shine ya tashi a rabo na, sai kuɗin da aka sayar da wannan gidan da motocin Baba da filayen shi aka raba mana, kuɗin na barsu hannun mijin yayah safiya nace ina son a nemi inda babu ruwa a yi, ko da a masallaci ne ko kuma ƙauyen da suke buƙatan ruwa, ina so yazama sadakatul jariwa wa Baba nah, shi kuma gidan na barwa yayah umatiti, saboda nasan basu da ƙarfi ita da mijinta, yanzu haka ma baya komai, side ɗin Baba kuma parlor ne babba da bedroom da toilet, sannan kuma parlon ma  akwai wani toilet a ciki da kuma ƙaton store, sai sama kuma ɗakuna biyu ne da ƙaton kitchen da store shima a wurin,   kuma akwai fili a wurin, duk nace na bar mata, ɗago kai yayah safiya tayi tace,   "mukhtari fushi kake da Baba ne  wanda har baka son gadon shi"?
Jujjuya kaina nayi alaman a'a,  "fushi kuma yayah? Na isa nayi fushi da mahaifina nayi kuma tunanin gamawa da duniya lafiya? Waneni yayah, nidai kawai a zuciyata naji ina so na sadaukar mishi da dukiyan, gidan kuma ummatiti ta fini buƙata, ina tausayinta da yadda rayuwa ta juya mata, gashi bata aiki sai ɗan sana'an da take taɓawa, kuma gidan haya suke har yanzu, wannan wurin kuma zasu iya fitar da ƙofar su daban basai sun shiga ta gidan ba, nima kuma Allah zai buɗa mun wani lokacin",  ina gama faɗin haka ta fashe da kuka tace,  "tabbas Alƙali yayi gaskiya, gashi ba'aje ko ina ba komai ya fara nuna kanshi, Mukhtar Allah ya saka maka da alkahiri, tabbas ka taimaki umatiti, domin duk gidan mu ita da Tijjani suka fi kowa shan wahala, shi yaƙi tsayawa yayi karatu ko yayi wani sana'a, duk kuɗin Baba ya tsole mishi ido, gashi kuma yadda rayuwa ta mai da shi".

Haka muka gama rubuta duk yar jejeniyan da zamuyi, aka tsayar da magana kuma za'a samu lawyer da alƙalin da ya mana rabon gadon.


********* lokacin da saƙo ya isarwa umatiti, kawai sai gata a gidan mu ita da mijinta da ƴar'uwar ta, sun yi kuka sunyi godiya wa goggo, don son samu bana nan, naje wurin A.G baida lafiya, tou na tafi duba jikin shi, a wurin suka ƙira mahaifiyar su, wanda lokacin suna takaba, duk da sun fita arba'in, amma ba kowa bane yake sakewa ya fito, kuka maman su tai tayi tana neman gafarar goggo, daga nan kuma tayi ta godiya tana saka mun albarka.
 Daga gefe na koma umatiti ce ta ƙirani tana kuka tana mun godiya, mijinta ma karɓa yayi yai godiya, sannan mamanta ma ta karɓi number wayana tayi ta neman gafara na tana kuma bani haƙuri, kafin kice me magana ya zagaye gidan Alƙali, ƙannen mahaifina duk sai da sukaje sukayi wa goggo godiya, sannan suka karɓi number na sukayi ta mun godiya, har hajiya sai da ta kirani tayi ta saka mun albarka, nidai har nafara jin kunyar ɗaukan baƙon number, a haka dai naga wata baƙuwar number ta shigo mun, ina ɗauka kuwa ashe Tijjani ne, kin san meya ce mun"?

Girgiza kawai nayi alaman a'a ina share hawayena, murmushi yayi yacigaba


*AUNTY NICE*