MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 33 Zuwa 35

MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 33 Zuwa 35

MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 33 Zuwa 35

Page 33----35

 

 

Shema'u na zaune ta zubama Bilkisu ido sai kallonta take, ba ƙaramin mamakin halin da ya sakata cikin wannan yanayi take ba, duk da tasan kaɗan daga matsalar Inna Huraira batai tsammanin matsalaice ta sakata cikin wannan halin,amma  dai bari ta jirata ta tashi taji gaskiyar lamarin daga bakinta. Ganin tana zaune haka ba wani abu sai tunanin zuci yasa ta jawo wani littafi dake gefen Bilkisun ta soma karantawa,sai tun a shafi na farko ta ɗago ta kalli Bilkisun domin ganin abin da ke cikin littafin, murmushi tayi taci gaba da karantawa tana mamakin yaushe Bilkisu ta ƙware da iya tsara kalamai haka ? Bama kamar gunda taga ta saka cewa "Ka taimaka ka dawo gareni ko kafafuwana kunnuwa tare da zuciyata su sami salamar rayuwa cikin aminci, Ibnah rashinka kusa dani ya jefani makarantar gararanba wadda kullum sai zuciyata ta wahala gangar jiki tayi nauyi." Sosai Shema'u ke dariya ashe Bilkisu munafukace ta iya soyayya irin wannan baka ganewa ko a fuskarta ? Cikin sauri taci gaba da karanta littafin wanda baki ɗaya duk kalamai ne masu ratsa zuciya ke rubuce cikinsa,ganin bata gama karantawa ba ga Bilkisun na niyyar farkawa daga barcin ta ɗauke littafin ta fice dashi daga cikin gidan.

 

 

 

Yana dawowa da madara a hannunsa da wani magani ya kwaɓa cikin ɗan kofi ya nufi gun magen, tana a yanda ya barta kuwa amma barci take ga alama na wahala ne, dan haka ya tadata ya kafa mata kofin saitin fuskarta, ai kuwa ta kama sha ba ƙaƙƙautawa sai da ta kusan shanye madarar kana ta janye kanta taci gaba da lashe bakinta. Sosai yake kallonta yana mamakin kansa domin shi bai wani damu da sabgar maguna ba balle har ya tsaya tarairayarta, asalima yasha korar ta wani soja dake zuwa ɗakinsa lokacin yana Nasarawa zaune amma yau shine da nemo mata abinci dasu magani ! Lallai  abin da mamaki .

 

Wayarsa ya janyo ya kira number ta Amma harta katse bata ɗaga ba, murmushi yayi mai sauti yasan tana can tana barcinta har yanzu kenan, a fili yace "Ibnah ba dama."

 

 

 

Malam Aminu komi ya kwance masa kai tsaye yake jin soyayyar Bilkisu na tasowa ta ƙasan zuciyarsa tana game dukkan ilahirin jikinsa, komi yake fuskarta yake gani, komi ya tsaya masa cak, yana jin ita kaɗaice wadda ta dace dashi a wannan rayuwar, domin komi nata yayi masa, sai dai bai san yanda zai yi ya gaya mata yana ƙaunarta ba, zuciyarshi ta bashi shawaran kai tsaye yaje ya faɗa mata yana sonta! Wata kuma tace ka dai je gun ƙawarta Shema'u ka aiketa da saƙonka sai yafi maka sauƙi, haka yayita saƙawa yana kwancewa har ya aminta da zai tari Shema'u da maganar domin ta shige masa gaba kan lamarin soyayyarsa da ƙawarta Bilkisu.

 

 

Cikin ƙwarin gwiwa irinta masu tabbas Huraira ta cigaba da zagin Aljanar tana tsine mata albarka, ita dai Aljanar kanta na ƙasa bata ce komi ba haka bata ɗago kanta ba. Huraira sai murna take a cikin zuciyarta tasamu magani mai ci dole ta rama duk  cuta da zaluntar da sukai  mata , bata manta wannan ja'irar Aljana itace kwanakin baya ta sata rawar indiyawa,dan mugunta ta dinga kifa mata mari, hada su sata rairo waƙar India to yau duk zata fanshe itama ta sata kuma ta kira mata munafukan wadannin yaran nan biyu dake wahal da ita taci ubansu la'ada waje suma.

Ta yi nisa a tunanin ramuwar gayyar da zata yi Aljanar ta soma rikiɗewa tana canza siffa zuwa ta mummunar baƙar halitta mai ƙaton kai hanci dauje baki buɗe haƙora cako-cako duk jini, idanunta sai zubar da jini suke gullama-gullama,baƙiƙƙirin babu kyan gani, wasu manyan tsutsotsi na fitowa daga inda Huraira ta bugeta da bulala, suna da ɗan tsayi da kauri sai dogon bindi ja amma su jikinsu fari ne, sunata shan jini kana iya ganin yanda jinin ke kwance cikin jikinsu jawur, hannuwanta ɗauke suke da wasu  ƙunbuna zaƙo-zaƙo ba kyan gani sai huci take irin na ɓacin rai da fusata. Jaruma Huraira kau duk abin nan bata kalli inda Aljanar take ba,hankalinta ya tafi kan irin izayar da zata ganama Aljanar ta huce takaicin muguntar da suka dinga mata a kwanakin baya, ganin kamar idan ta ɗauki layar a hannunta ta sake shafa kwallin zatafi luguiguita Aljanar yasa ta ƙara shafa kwallin ta ɗauki kullin maganin ta riƙe gam tana cewa a fili "Matsiyatan banza masu masifar ƙarya daga yau na zama malamarku duk inda kuka shiga ni zani in maganinku, Sai alokacin ta kalli wajen da Aljanar take tana cewa "Yau rawar ƴan Nijar zaki mun tafi saka nishaɗi ja'ira..........Maganarta ta tsaya miiyanta ya ɗauke sanda tai ido huɗu da mummunar halittar dake gabanta, sai yagar fatar jikinta take tana taunewa baji ba gani, ga wani baƙin jini dake zubowa daga ƙwala-ƙwalan idanunta ba kyan gani. Huraira taita maza ta sake riƙe maganin tace "Maza-maza ki koma siffarki ta farko bani buƙatar wannan mummunar siffar." Ita dai Aljanar abin ya kai ga farke cikinta tana zaro hanjinta tana ci cikin sauri ko kallon inda Huraira take bata yi ba, kwatsam ! Yaran aljanun nan suka bayyana gabanta suna zaro idanuwa waje da alamar mamaki suka kalli Huraira da fara shan jinin jikinta suka ce "Ke kam miya haɗaki da ƴar burguma uwar cin naman bil'adama? Zaro idanuwa waje Huraira tai tana haɗe miyau da ƙyal ta sake duban inda Aljanar take, kaɗan ya hanata faɗa ihu kuwa domin ta fafare cikin baki ɗaya ta cinye kayan cikinta ba saura sai ƙoƙarin yago cinyar ƙafarta take tana so taci, yaran suka kwashe da dariya suka ce "Tana gamawa naki kayan cikin zata cinye barta ke harma idan ba guduwa mukaiba  tana iya cinyemu "  sai ga zawo ziii yana zubowa daga zanen Huraira mai qarin tsiya, duk ya girme ɗakin, zuwa lokacin Aljana ƴar burguma ta cinye cinyoyinta tas, ta janyo watan aljaninguda ta danne ta ƙwaƙule masa ido guda ta lumba baka ta taune, Huraira sai ta fara rawar ƴan bori ai tana makyarkyata tamkar wadda tai wanka da ruwan sanyi cikin hunturun sanyi,hatta haƙoranta karkarwa suke yi, cikin azabar tsoro ta nufi kofa da nufin buɗewa ta fice, amma ina ƙofar ɗakin taƙi motsawa ,tana ta buga ƙofar ko wani zaiji ya buɗe mata amma tsit ba alamar kowa cikin gidan,ji tayi an fisgota kamar walƙiya ta ganta gaban Aljanar zuwa yanzu ta cinye yaron sai uban kansa dake gefe yana cewa "Wallahi tunda kika cinyemu itama ki cinyeta inba haka ba Sambatul zaman  zai ramamun." Huraira ta dubesa cikin tsoro tace "Mugun banza tunda ta cinyeka ina ruwanka da ni? Daman kaine rabonta ba ni ba." Ita dai Aljanar sai kallon Huraira take tana aiyana irin azabtar da zatai mata na duka da zagin da tai mata, Huraira ganin Aljanar na riƙe da ita kamar rai ɓace sai ta fara ƙoƙarin bata baki cikin tsoro take cewa "Na rantse da Allah Aljanu gareni masifarfu masu shegen neman magana idan anfi ƙarfinsu su rugabsu barnibda jidaji, amma idan zakimin Lamuni Allah hakan ba zata sake faruwa ba ." Bata gama maganarba taji saukar wani uban dundu a bayanta sai da ƙashinta yayi ƙara, ta kuwa ware bakinta ta kwaɗa ihu, haɗa cewa kiyiwa Allah kimun iya abin da nayi maki indai kina da tausai. Ai ga alama batajin yarenta dan haka sai Huraira ta koma yaren Gwari a tunaninta zata dace taji mi take cewa, ganin ba ta sauya zabi ba sai jibga da ranƙwashi take sha yasata yin yaren larabci da take jin su malam nayi da Bilkisu, tace cikin azabar zafin dukan da take sha  "La anta minna wa minkum, saffa-saffa ya akhee ." Wata mahaukaciyar dariya taji ɗakin ya amsa kuwwarta abin da ya tazara kenan ta fara ambatar "Kiyi mun rai daga yau ban sakewa dan Allah Dan uwayenku mamata." Kawai gani tayi ɗakin yayi ɗif ba haske ko rafin hannunta bata ita gani, motsin wani abu tadinga ji yana sukurniya kamar ɓeraye na shawagi ,ta zaro idanuwa waje tana cewa "Nashiga uku na lalace ni Huraira yau mi zan gani haka ? Kamar daga sama taji ance "Baki shiga uku ba dan yau sai munyi faɗa irin na masifa danben bala'i zagin tada gari Ni da ke idan nacinye ki shine zaki shiga goma bama uku ba masifarfiyar banza." Huraira sai hawaye tace "Wallahi banda masifa duk ƙarya ce da burga ko jariri bai kaini haƙuri ba." Buge mata baki akai tamkar leɓenta zai daɗi ƙasa haka taji , cikin wata bahaguwar murya akace "Huraira kince ke ce uwar tujara ko ? Tace "Wallahi bance ba idanma nace subutar baki ce kuma ƙarya ja'irin bakin nawa yake ma."  Bulala taji saukarta bayanta mai zafin gaske sai da ta gantsare cikin azabar zafin tace "Allah ya sakamun tunda kun san dai ƙarya na shirga ni banda masifa banda tujara saliha ce ni kuma a tambayi Malam ma."  Gaba ɗaya haske ya bayyana a ɗakin, sai taga wasu manyan ɓeraye nata cin wata irin daddawa suna dariya suna juyi, daga gefe kuwa Aljanar ce ta sauya kamanni zuwa na jikin alade fuskar zabo tana tsaye tana kaɗa bindinta hawayen jinin basu daina zubowa ba.

 

Huraira ta fara ƙoƙarin tunano addu'ar da Kuma ta koya mata idan zatavrafi ɗibar ruwan dare, aikuwa ta rage bakinta da karfi ta fara karanto addu'ar cikin farin ciki da ta tunota ayau , tasha don karanta addu'ar kwanakin baya tana mantawa yau dai Allah ya sota ta tuno ta, ta runtse idonta ta fara "Allahumma laka tur-tur wala war-war inga fau wa kar musake haɗuwa fid duniya." Dai-dai nan Malam yayi sallama  ya shigo gidan kai tsaye ya nufi ɗakin Huraira da kaya niƙi-niƙi yana hamdala .

Yana tura ɗakin komi ya ɓace sai Huraira dake tsaye tana sambatu, girgiza kai yayi ya aje kayan yace "Huraira lafiya kike tsaye kamar wadda taima Sarki ƙarya? Zai sake magana yaji wani wani mugun wari ya shige masa hanci kamar an kashe mushe, ya toshe hancinsa yana cewa "Huraira ɓera yayi mussai a cikin ɗakin nan ? Kallon jikinta tayi taga zawon da tayi ne ke warin, sai lokacin shima yabi ta da kallo ya gane ma idanunsa zawon dake jikinta harya kwarara ƙasa .

 

 

To masu karatu komi zai faru anan kuma ?

 

Malam Aminu zai gayama Shema'u abin da ke damunsa ?

 

Ya labarin Yah Malam ?

 

Duk kuci gaba da bibiyar alƙalamin Haupha