ANA BARIN HALAL..:Fita Ta 37
ANA BARIN HALAL..
*Page 37*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
A gaban gawan ƴar'uwata habiba na durƙusa, hannuna toshe da bakina, saboda bana son yi mata kuka akan gawanta, hannu nasaka na yaye mayafin da aka rufe fuskanta da shi, kyakkyawar fuskanta mai kama da na Abban mu shinfiɗe da annuri, ga wani fari da tayi na alaman babu jini a jikinta, fuskanta a ɗan kumbure kaɗan, wani abu ne naji ya bugi zuciyana, sai na dinga tunata a yadda muke da kafin komai ya lalace a tsakanin mu, wai yau habiba ce shimfiɗe a gabana tazama gawa? Duk sai naji nakasa riƙe kaina, ina kuka ina mata addu'a, har wani lokaci aka zo aka mata wanka aka shiryata, duk dai ina wurin, addu'a Abba ya shigo yayi mata, ranan dai kwana mukayi a zaune babu wanda ya samu daman runtsawa.
Washe gari dukkan yayun mu sun iso, yayah umar ne kawai ba'a bar shi yazo ba, zuwa lokacin duk nayi laushi bana iya komai sai dai hawayen da yake zuba mun, ina ganin mama tayi wanka a babyn habiba, ta bashi madaran da tun jiya ummie ta aika aka sayo da su glucose, ana bashi madaran hafsy ta goya shi a bayanta, ita dai mamie babu abun da take iya taɓukawa, wuraren tara na safe raliya suka iso, inaga daga ita har su yayan mu ko da asuba suka kamo hanya oho, shigowan ta ne ya sake hargitsa mu, domin rungume gawan tayi tana kua kaman ranta zai fita da ƙyar yayah muhammad yajata zuwa ɗakin mamie, ganin su ya saka mamin sake fashewa da kuka, shima yayah muhammad kukan ya fashe da shi yana zama a bakin gadonta.
Ana shirin fita da ita ƙarfe goma saura, sai ga Abba sun shigo tare da Aliyu, har gaban gawan Abba ya rakashi, ina kallon shi cike da jin haushin shi, yana ta share hawaye hannun shi riƙe da hanky, addu'a sosai ya mata, sannan naji yana cewa "habiba na yafe miki, Allah ya miki rahma, ya raya abunda kika bari, haƙurin ki da halayenki nagari, ya miki jagora har cikin aljannatul firdausi" daga nan ya fashe da kuka, har sai da Abba ya umurci yayah Ahmad ya fita da shi, gefe ɗaya kuma Mummyn shi ce zaune da wasu daga cikin ƴan'uwan shi mata, Addu'a sosai Abba yayiwa habiba shi da wani abokin shi da yayan mamie, Abba ya ƙurawa gawan ido na wani lokaci sannan yace, "haƙiƙah mutuwa xafin ta nada ciwo, mutuwa irin na ƙuruciya, habiba Allah ya gafarta miki, Allah ya baki ikon amsa tambayoyi, Allah yasa kinyi shahada, ni Usman mahaifinki na yafe miki duniya da lahira, ballantana ma baki mun komai ba, haƙuri da son zumunci duk naki ne habiba, Allah yasa kin huta," juyowa yayi idon shi akaina yace, "Aysha Allah ya ƙara miki haƙuri, tabbas kinyi rashin masoyiya, kinyi rashin twin sister ki", ta shi nayi da gudu na rungume Abba ina kuka, shima Abban kukan yakeyi, da ƙyar aka riƙeni lokacin da naga ana ɗaukan gawanta, yayuna ne da Aliyu da wasu daga dangin mu suka ɗauke ta, nidai farkawa nayi na sake ganina a ɗakin hajiya ummah, wato suna na sakeyi da aka fita da habiba.
Hawaye nima na share, ganin yadda Aysha take kuka kaman a yanzu ne aka mata wannan rashin, jikina duk a sanyaye na miƙa mata ruwa, karɓa tayi tasha sosai, sannan ta dube ni da idonta da suka chanja kala, tsabar rinewa da sukayi saboda kuka, "Aunty nice rasuwar habiba yana daga cikin mutuwa masu ciwo da aka mun a rayuwata, naji ciwon rashin ƴar'uwata, naji ciwon rashin masoyiyata, har gobe ina kokawa wannan mutuwan", ajiyan zuciya nayi na kalleta, "hajjaju ae mutuwace mai ciwo, rashin ɗan'uwa ae babban rashine, ballantana ke zafin har da raba tsakanin ku da akayi, Allah ya mata rahma", na faɗa, "Ameen ya rabbi, nagode Aunty nice, naji an fara ƙiran sallah, bari mu tashi muyi sallah, sai mu cigaba kafin nan ma zuciyata ta ɗan yi sanyi", miƙewa nayi na mata jagora har bedroom ɗina, tana shiga toilet na shimfiɗa mata sallaya na fice.
Bayan ta idar da sallah ne na kawo mata abinci, fuskan ta ɗauke da murmushi tace, "Aunty nice abincin nan zai samu shiga kuwa"? Nima murmishin nayi nace, "ae ko idan bakici ba bazan ji daɗi ba, gara ko kaɗan ne ki taɓa nasan dai kinci",
Rausayar da kanta tayi sannan ta jawo coolern abincin ta zuba kaɗan, nidai bance mata uffan ba, don halin da take cike Allah ne kawai ya bar wa kanshi sani, fuskanta da murmushi ta dubeni, "tare zamuci ko"? Murmushi nayi na gyara zama mukaci taren, bawai don ina jin yunwa ba, kawai dai ta samu sukunin ci, muna gamawa na tattare komai, wannan lokacin a ɗaki muka zauna, tana duba na da murmushi a fuskanta ta cigaba.
Bayan na tashi zaune na muka haɗa ido da Aunty Rakiya, Zama tayi a gefe na , "sannu Ayshaa, sannu ko", naji tana ta jero mun, ido na sun mun wani nauyi na riƙo hannunta, "Aunty an binne habiba ko"? Na faɗa idona suna zubar da hawaye masu zafin gaske, hawayen ta share itama, bata ce mun uffun ba ta jawoni kawai ta rungume, munyi kuka ba kaɗan ba, har zuwa wani lokaci tukun ta tashi ta haɗa mun ruwa mai zafi tace na shiga nayi wanka, bayan nayi wanka nayi brush, na ɗauro alwala na fito, tea mai zafi ta miƙa mun, kaɗa kai nayi alaman bazan sha ba, harara na tayi ta ɗaure fuskanta tace, "maza karɓa ki shanye ki bani cup ɗin," ganin fuskanta ya saka na karɓa ina hawaye na shanye, ina sha kuwa cikina naji yana wani uban kuka, haka dai na miƙa mata cup ɗin, sannan na wuce na saka kaya, chan ta dawo tace mu fita parlor.
Duk familyn su Abban mu suna zaune a parlor tare da hajiya ummah da taci kuka kaman yayah, sai cewa take, "usmanu na an mishi mutuwa, usmanu yayi rashi", haka dai duk muka gaisa dasu ina ta daurewa, amma kukan da hajiya ummah ta fashe da shine ya sakani sake fashewa da kukan, da ƙyar aka rarrashe mu, sannan na wuce parlon ummie na, achan na samu so zainab, hadiza, hafsy, ummtah da maryam da tun safe tazo, gefe ɗaya kuma Aunty B ne zaune tare da su Aunty j, gaisuwa mukayi sannan na wuce wurin ummie na, akan gadon ta na zauna gefenta, ɗago kai nayi don na gaisheta amma muna haɗa ido kawao sai na kasa, rungumeta nayi ina kuka, kuka mai ciwo da zafi nakeyi, bata hanani ba sai buga baya na da takeyi a hankali, da ƙyar nan ma Goggo maman zainab ta rarrashe ni, ban fita parlon ba sai na naɗe a jikin ummie kawai na kwanta, a hankali ina share hawayen da suka kasa tsayuwa.
Muna idar da sallan magarib muna zaune dukkan mu a parlon ummie, sai ga Yayah Ahmad da M.G sun shigo tare, nidai kallo ɗaya na musu na maida kaina ƙasa na cigaba da jan chasbi na, ummie aka ƙira suka gaisa, sannan ya matso har inda nake ya ambaci sunana, ban iya na amsa mishi ba sai kukan da naji kawai yazo mun, wanda ban san meyasa ba ko sunana aka ƙira sai dai naji kuka yazo mun, wai habiba dai, habiba tawa ce babu yau a duniya? Wayyo Allah mutuwa, ashe haka ciwon ta yake? Haƙuri sosai ya dinga bani, bayan ya mun gaisuwa, sannan yace mun Goggo tana mun gaisuwa insha Allahu gobe zasu shigo tare da Mummyn A.G, kai kawai na ɗaga mishi alaman amsawa, amma ban ɗago Kaina na dube shi ba, ya daɗe a wurin kafin ya miƙe ya fice.
Washe gari kuwa su mummyn A.G suka zo, macece ƴar gayun gaske, duk da ta fara nanyanta amma bazaki taɓa cewa ta haifi A.G ba, Abaya ce a jikinta baƙa marar kwalliya, sai glass fari a manne a idonta, daga gani na ƙara ƙarfin kallo ne, gefe ɗaya kuma Goggo ce, farar bafulatana, ita ta zama dattijuwa, duk da girma ya kama goggo amma akwai farin fatan nan da kyaun fuska, daga ganin ta macece da lokacin ƙuruciya tayi jiki da tsayi, masha Allah, yau kam naga inda M.G ya samo kyaun shin nan, don babu ƙarya Matar akwai kyau, ga fara'a,
mummy ko ina ganin idon ta sai da na runtse nawa idon, da sauri na sunkuyar da kaina ƙasa, domin sai naga kaman idon ,A.G na kallah, duk da Mummy baƙace, amma kyakkyawar mace ce, ga ido kaman wanda ta cire nata ta mannawa A.G, hattah lumshewan da yake dashi irin nata ne, sai dai hala farin fatan shi na mahaifin shine, doguwace kuma bata da wani jiki sosai, gefe ɗaya kuma Heedayah ce, itama kyakkyawa ce amma dai bata kama ƙafan A.G ba, duk da dai suna kama da A.G, amma ita bata kai shi fari sosai ba, amma sunyi kama, don hattah idonta irin na Mummy ne, irin na shi, haka kawai naji haushinta a zuciyata, wato akan wannan M.G ya share ni ko waya baya mun, sai naji bana son kallon fuskanta.
Bayan mun gaisa da sune dukkan mu a parlon ummie, sai mummy take miƙo mun wayanta, "Ga A.G ko dougter", a kunya ce na karɓi wayan, "Eesha sannu ko, sorry beauty, sannu da rashin da aka mana, wayan ki akashe tun ranan bana samunki, M.G kuma yace mun yazo kina ta kuka shiyasa ya kasa haɗamu, kiyi haƙuri Eesha, addu'a take buƙata, Allah ya jiƙanta ya raya abunda aka bari,", ina jin muryan shi sai naji rauni na ya ƙaru, hawaye kuma suka soma mun sintiri, ban san lokacin da bakina ya ambaci sunan shi ba, amma murya chan ƙasa wanda nayi imanin ko maryam da ta ke gefe na bata iya jiyo maganana, "A.G na rasa habiba, ta tafi ta barni da amanan babynta, bansan yaya zanyi na bashi kula ba, bansan yayah zanyi da ciwon rashinta ba, kadawo please", na faɗa sautin kuka na yana fita, a hankali naji hannun mummy shi ta rungumo ni jikinta, shi kuma daga wayan naji yana magana, haƙuri yake ta bani kaman zai mun kuka, a haka na miƙawa mummy wayan ina ƙara fashewa da kuka, rungumeni tayi sosai tana rarrashina, gefe ɗaya kuma su hafsy suna ta share hawayen su.
Ranan uku su Aliyu suka shigo bayan anyi addu'a tare da Yayah Ahmad da su M.G, ashe kullum da su ake zama bansani ba, sai lokacin naji su Aunty B suna faɗa, akan yadda Aliyu yayi laushi sai kuka yakeyi, hattah mummyn su jammy rasuwar ta bugata, gashi ƙannen mamie naji fir sunƙi basu yaron su gani, ganin kada abu yazama abun magana Mummyn ta share bata tanka musu ba, hatta Aliyun sun hanashi har sai da Abba ya musu jan ido tukun aka miƙa mishi ya mishi huɗuba ya mishi addu'a, tunda na ɗaga ido muka haɗa ido da su ban ƙara ɗaga kaina ba, don ko gaishe mu da sukayi idona yana ƙasa, kuma a washe gari M.G ya tafi, don naji Yayah Ahmad yana gayawa Ummie M.G zai koma gobe insha Allahu.
Nidai banje naga babyn ba sai ranan da akayi bakwai, wato ranan da aka raɗa mishi suna, kuma yaro yaci sunan Abba wato *USMAN* nan ma sai bayan magrib na shiga side ɗin mamie, wanda tun ranan da akayi rasuwan ban ƙara marmarin shiga ba, haka na daure muka shiga tare da su Aunty B, domin zasu mata sallama gobe zasu wuce idan Allah ya kaimu, zama nayi a ƙasan carpet da muka shiga parlon mamie, don dukkansu suna zaune a parlon, yaron yana hannun raliya tana bashi madara, kallo ɗaya na mishi na kawar da kaina, nayi-nayi na iya buɗe baki na gaida mamie amma na kasa, har sai da ita don kanta ta miƙo mun hannu, kuka naji yazo mun, wanda itama kukan ta fara, sannan raliya ta miƙo mun babyn tana cewa, "Adda gashi ki mishi addu'a ki zaɓa mishi sunan da za'a ƙira shi da shi," ta faɗa hawaye yana bin fuskanta, "wato Aunty nice idan kikaga mamie da raliya a lokacin zakiyi zaton har abada duk wani gaba yaƙare a tsakanin mu, amma ina kibar zuciyar da babu Allah a cikinta, " hannu na saka na amshi babyn da ya buɗe idon shi tar yana kallo, babu abun da yabari na kamanni da mahaifin shi, hatta baƙin fatan na Aliyu ne, don duk da jariri ne bai yi wani fari ba, ido na zuba ina ƙare mishi kallo, gefe ɗaya wani ƙaunar shi da tausayin shi na cika zuciyata, "SABEER" na ambace shi da shi muryana yana ɗan rawa, kuka mamie ta sake fashewa da shi tana furta, "Allah yasa ƙazamo mai haƙurin irin mahaifiyarka, Allah yasa ka amsa wannan sunan ɗan albarka", miƙewa nayi da shi a hannuna har gaban mamie, ƙasa na durƙusa na furta, "Mamie ki amince na tafi da shi don cika umirnin sisto", bata bani amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi ƙasa tana share hawaye, yayarta ce ta bani amsa da, "Aysha kiyi haƙuri ya ɗan ƙara tasawa, sai ki karɓe shi, yanzu idan ya tashi kuka da dare yayah zakiyi?" ido na ƙura mata bance komai ba, amma abun mamaki sai naji muryan mamie tace, "ta tafi da shi tunda ae ba nono za'a bashi ba, kuma nayi imamo da Allah ummie zata taimaka mata", tana rufe baki mahaifiyarta ta amsa da "a'a bazaiyiwu ace yarinya ƙarama ta riƙe ba, kawai ta dinga zuwa da safe tana amsan shi, amma bamda a tattara shi a miƙa mata, ke mai zaki gani zuciyarki tayi sanyi bayan shi"? Ta faɗa tana kawar da kanta gefe, babu musu na miƙa shi hannun sister mamie muka musi sallama muka fice a parlon.
Kullum safe kuwa sai na shiga side ɗin mamie na ɗauko ɗana, gashi mai haƙuri baida rikici, wuni mukeyi tare da shi, har su raliya suka koma kaduna, idan zanje makaranta ne kawai na kan bar shi hannun mamie, wataran ma mamah ce ko ummie suke riƙe shi, ita dai mamie har zuwa lokacin a sanyaye take.
Habiba tayi arba'in aka raba gadon abun da ta bari, sannan a ranan Aliyu da iyayen shi suka sake zuwa gidan mu gaishe da su Abba, a wannan ranan kam an bar su sun ɗauki sabeer, don har video call sukayi da jammy, duk da munsha video call tana ganin shi, Aunty nice zaki sha mamaki idan nace miki sanadin yaron nan har video call munayi da A.G? Murmushi nayi ina kallonta cike da mamaki, itama murmushin tayi ta cigaba da bani labari.
Ranan farko da muka fara, na dawo daga sch yana ta kuka, an rasa me ya same shi, sai na ɗauke shi inata jijjiga shi, lokacin wayan A.G ya shigo, a rikice na ɗauka, jin kukan da sabeer yakeyi yasa yace bari ya ƙirani video call ya rarrashe shi, hummm abun mamaki indai akan ɗa nane zan iya komai, ae babu shiri na ɗauki wayan da ya sake ƙirana video call, duk nayi sukuku doni, matso mishi da fuskam sabeer nayi, shi kuma yanata rarrashi, ranan naga ikon Allah kawai sai yaro yayi shiru yanata sauƙe ajiyan zuciya, murmushi A.G yayi yace, "yarona yana missing ɗinane, ko kuma Ammin shi bata iya bashi kulawa ba, yafi son na Abbin shi", tura baki nayi cike da shagwaɓa, sanan ya umurce ni na saka mishi yatsa a baki , ina saka mishi kuwa ya riƙe yana tsotsa idon shi a kaina, a haka har yayi bacci, ajiyan zuciya na sauƙe na maida kallona kan A.G, ido ya kashe mun yana murmushi, "yakamata na dawo na baku kulawa sosai ke da ɗanmu, don naga wannan rikicin uwa da ɗan duk A.G ne zai iya shanyewa," Murmushi na mishi lokacin, sannan nace, "saura kwana nawa kadawo"? Idon shi cikin nawa yace, "saura 2weeks oum sabeer", daɗi nake ji idan ya ƙirani da wannan sunan, amma sai na wani harare shi, dariya ya ɗanyi.
Lokacin da su Aliyu suka zo da mummyn shi takeyiwa Ummie maganan ya kamata su turo manya akan maganan Aliyu, ita dai Ummie bata ce komai ba sai murmushi da tayi, bata kuma gayawa kowa yadda akayi ba har bayan sati biyu da maganan, ana saura 2dys A.G ya dawo, iyayen Aliyu suka zo wurin Abba da maganan Aliyu ya dawo da maganana, a haka ma basu san da wasiyan Habiba, kawai da so da ƙauna da Aliyu yake mun da iyayen shi ne, anyi dace kuma ranan da sukazo Yayah Muhammad yana nan, don yazo weƙend.
*AUNTY NICE*
managarciya