Ƙaddarar Rayuwa Ce Ta Sanya Ni Rawa A Gidan Gala----Tahir Fagge

Ƙaddarar Rayuwa Ce Ta Sanya Ni Rawa A Gidan Gala----Tahir Fagge
 
...na yafe wa duk waɗanda suka zage ni
 
Dadadde  a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Tahir Fagge, ya bayyana cewa rashin kuɗi ne ya same shi, tare da  rashin lafiya, shi ya sa da aka neme shi aka bashi kuɗi ya je ya yi rawa a gidan Gala domin yiwa kansa magani.
 
Cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC tayi da shi, Tahir Fagge ya ce mutane ba sa fahimtar ƙaddara, wacce duk arzikin mutum ko talaucinsa bai wuce ƙaddarar rayuwa ta same shi ba, domin yace ya kasance yana fama da ciwon zuciya, kuma ba shi da kuɗin magani.
 
“A lokacin idan na yi wa (Ali Nuhu) magana zai ba ni kuɗin, amma sai na ji kunya. 
Domin  da farko shi ne ya ga wata waya a hannuna, sai ya ce ba zai yiwu ba, suna da rai ina riƙe irin wannan wayar, sai ya yi waya aka kawo min wata."
 
“To wayar na sayar na sayi magani; Sai kuma na ji nauyin in sake komawa."
 
“Lokacin da nake bukatar kuɗi Naira naira dubu 265, na je wajen Rarara ya ba ni dubu 20, Mai Shadda ya ba ni dubu 20, sai Abdul Amart ya ba ni dubu 15."
 
“Ina cikin wannan yanayi ne sai yaran nan (Ƴan Gidan Gala) suka zo suka same ni suka ce sun sanya sunana a matsayin babban baƙo, za a bude gidan wasa, nan take suka ba ni dubu ɗari da hamsin.
 
“Dana je, ina zaune, sai suka ce akwai waƙar Bazar Kowa wadda Lilisco ya hau, sai suka ce don Allah in hau in kwatanta wa yaran saboda ba su san waƙar ba. Shi ne na hau waƙar, sai kuma aka sa wata ta Hamisu Breaker, shi ne fa aka riƙa yaɗa bidiyoyin nan.” Inji shi.
 
Daga ƙarshe Tahir Fagge ya ce ya yafe wa duk waɗanda suka zage shi, ko ya yada bidiyon ko ya yi suka kansa.