Alkawarin Aure: Kotun Musulunci Ta Dauki Wani Mataki Kan Shari'ar Hadiza Gabon 

Alkawarin Aure: Kotun Musulunci Ta Dauki Wani Mataki Kan Shari'ar Hadiza Gabon 
Kotun Shari'a dake zamanta a Magajin Gari Kaduna ta ɗage zaman shari'ar Fitacciyar Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, 2022. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun ta ɗauki wannan matakin ne domin bangarorin biyu su je su yi sulhu tsakaninsu a wajen Kotu. 
Idan baku manta ba, Bala Usman, wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a gaban Kotu bisa zargin ta saɓa alkawarin auren da ta masa bayan kashe mata N396,000.
 
A cewarsa ya jima yana soyayya da jarumar har ta masa Alƙawarin aure. Zargin da Gabon ta musanta da cewa ba ta taɓa ganin shi ba a rayuwarta. 
Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, a ranar Laraba, ya ɗage zaman bayan wani babban Lauya, Suleiman Lere, ya roki Kotun ta bashi lokacin ya shiga tsakanin mutanen biyu domin sulhu.
Lauyan mai ƙara, Barista Nuruddeen Murtala, ya yi na'am da shirin sulhun da babban Lauyan ya kawo, inda ya ƙara da cewa Sulhu alkairi ne da Allah SWT ke so saboda haka basu da jayayya. A ɓangarensa lauyan wacce ake ƙara, Barista Mubarak Sani, ya amince da shirin sulhun amma ya nemi Kotu ta fara sauraron shaidun da ɓangaren masu kara suka yi alƙawarin zasu gabatar.