Yaki da Rashin Tarbiyya: Gwamnatin Kano Ta Hana Fim na 'yan Daba da Daudu

Yaki da Rashin Tarbiyya: Gwamnatin Kano Ta Hana Fim na 'yan Daba da Daudu


Gwamnatin jihar Kano ta kafa sabuwar doka ga masu shirya fina-finai a fadin jihar baki daya. 
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya fim da ke nuna dabanci ko kuma harkar 'yan daudu a jihar. 
Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan ta'addanci da ake samu a tsakanin matasa a birnin Kano.
A 'yan kwanakin nan an samu rasa rayuka da dama sanadin ayyukan 'yan daba a birnin Kano da kewaye. 
Har ila yau, a Kano ana yawan samun 'yan daudu da ke kawo cikas musamman a kokarin hukumar Hisbah na gyara tarbiyya.
Har ila yau, shugaban Hukumar tace fina-finai a Kano, Abba El-Mustapha ya tabbatar da daukar matakin a shafinsa na Facebook. El-Mustapha ya ce sun dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da al'umma ke yi kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar daudu a jihar Kano. 
Abba El-mustapha ya bada wannan umarni ne jim kadan bayan ganawa da ya yi da manyan ma'aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano.