Darakta a Kannywood, Aminu S. Bono ya rasu
Fitaccen daraktan shirya finafinai a masana'antar Kannywood, Aminu S Bono ya rasu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa Bono ya rasu ne jim kaɗan bayan ya dawo gida daga gurin aiki ba tare da wani ciwo ba.
A wani bayani da aka wallafa a facebook, an ce za a yi jana'izar Bono a gobe da safe.
Allah Yai masa rahma, Ya kula da bayan sa, Ameen.