Ba zan sake tikar rawa a cikin Fim ba har abada-----Ali Nuhu

Ba zan sake tikar rawa a cikin Fim ba har abada-----Ali Nuhu
Ba zan sake tikar rawa a cikin Fim ba har abada-----Ali Nuhu
 

Shahararren dan wasan Hausa da ya dade a masana'antar yana jan zarensa wanda a yanzu girma ya zo diyansa da ya haifa sun girma waton Ali Nuhu ya ce ya yi ritaya da rawa har abada ba zai kara yin rawa a cikin shirin Fim ba.
 
Jarumin Kannywood Ali Nuhu Ya bayyana cewa shifa yanzu ya daina  yin Rawa kuma ba zai kara ba.

 
 Sai Dai Kuma Yayi Wani Jirwaye Mai kama da Wanka Inda ya bayyana Cewa Batun Inyi Rawa Ina Rausayawa,   kada kugu Shi ne na bari amman zan iya rangaji kadan kadan.
Managarciya na ganin kamar tauraron ya fahimci yanda girma ya zo masa da shekarunsa da suka tafi don haka yakamata ya jingine harkar samartaka irin wanan ta masu kananan shekarru ganin yanda a yanzu matan da ke shigowa a harkar wasan kusan ya haife su.
Harkar wasan kwaikwayo lamari ne da ake shiryawa da yin abin da zai kayatar da wuya a kayatar da mai kallo sa'ar mahaifinka ya rika tikar rawa tare da kai a matsayin masoya, wannan zai iya zama daga cikin wasu dalilai da ya sanya dan wasar ya ga dacewar jingine tikar rawa irinta samari 'yan bana bakwai.