Ɗan majalisar PDP Ya Bai Wa Jami'an Tsaro Kayan Aiki, Ya Tallafawa Mata

Ɗan majalisar PDP Ya Bai Wa Jami'an Tsaro Kayan Aiki, Ya Tallafawa Mata
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomi Yabo da Shagari, Umar Yusuf Yabo, ya bayar da tallafin babura 200 ga hukumomin tsaro da wasu mutane a mazaɓarsa. 
Ya kuma baiwa mata 2,000 jari tare da gina famfunan ruwa 50 da kuma injinan samar da wutar lantarki mai karfin 2.5KVA guda 50 ga manoma da masallatai a yankunan biyu. 
Bai tsaya iya nan ba, Dan majalisar ya kuma raba kayan makaranta 500 da litattafan rubutu 5,000 ga daliban firamare, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake jawabi a wurin taron wanda ya gudana a garin Yabo ranar Litinin, Yusuf ya ce wannan tagomashin na cikin alkawuran da ya yi wa al’ummar mazabar a lokacin kamfe. 
"A lokacin yakin neman zabe, na yi wa al’ummarmu alkawarin kawo sauyi mai kyau domin Yabo/Shagari ta rasa wakilci na gari a zauren majalisar wakilai na tsawon shekaru da dama."
"Sabida haka abin da kuke gani yau ba komai bane illa mafarin kyawawan abubuwan da ke kan hanya." 
A cewarsa, kowacce daga cikin mata 2000 za ta samu tallafin Naira 50,000, inda ya kuma kara da cewa, akwai wasu mata 50 da za a ba su kyautar firiza kowace ɗaya.
A rahoton The Sun, ya ci gaba da cewa: "Na kuma miƙa koken matsalar wutar lantarki ga majalisa saboda yankunan Yabo da Shagari sun jima cikin duhu tsawon shekaru. Na muku alƙawarin hasken wutar lantarki zai dawo nan bada daɗewa ba."