Abubuwan Da Ke Kawo Cibaya A Arewacin Nijeriya---Gwamnan Katsina

Abubuwan Da Ke Kawo Cibaya A Arewacin Nijeriya---Gwamnan Katsina

 

A wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta na zamani, an ji Umaru Dikko Radda PhD ya na bayani kan rashin cigaban yankin Arewa. 

A faifan da ya fito daga shafin Mahadi Shehu, an ji Dikko Radda ya na zargin son kai a matsayin abin da ya jawowa ‘Yan Arewacin Najeriya koma-baya. 
Gwamnan jihar Katsina ya amsa tambaya ne a game da abin da ya zama tarnaki da dabaibayi ga yankin duk da adadin al’umma da yawan kuri’ar zabe. 
“Hadin-kai ne, babu hadin-kai a Arewa, kowa shi kadai yake aiki. A Arewa kowa ta kan shi yake yi, babu wanda ya damu da ya al’umma za ta kasance. 
Kowa ta kan shi yake yi, babu shugabanci, babu wanda ya isa a ce shi kadai ne idan ya yi magana za a saurare shi a Arewar nan, don haka babu jagoranci. 
Saboda haka abin da mu ke bukata shi ne jagoranci, girmama manya da kuma daukar matsaya da za ta yi aiki a kan duk wani mutumin da yake a Arewa.” 
Dikko Radda ya bada misali da Yarbawa wanda ya ce idan su ka tafi Landan ko wata kasar waje, sai sun zama silar jawo ‘yanuwansa zuwa kasashen ketare.