Daga Aminu Abdullahi Gusau.
An bayyana Alhaji Abdullahi Abubakar A .A Gumbi a matsayin jagora na gari maihalin 'yan mazan jiya.
Hakan ya fitone daga bakin shugaban kungiyar neman hadin kan matasa ta kasa watau United Nigeria youth a turance, kwamred Haruna Shehu a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Sokoto.
Ya kara da cewa sakamakon kokarin da Alhaji Abdullahi yake yi na ganin sai ya kauda bangar siyasa a tsakanin matasa ta hanyar Samar musu da aikin yi, hakan ya sanya jama'a da dama suka rika jinjina masa.
Haruna Shehu ya ce Alhaji Abdullahi ya samarwa matasa da dama aikin yi musamman aikin jami'an immigration, watau masu kula da harkar shigi da fice ta kasa, da aikin 'yansanda da sauran aikin kaki da dai sauransu.
Ya ce a halin da ake ciki yanzuma wasu da dama suna nan suna karbar horo a jihar zamfara a halin yanzu, ya kara da cewa ya dace masu hannu da shuni su rika daukar darasi daga gareshi .
Da yake amsa tambayar wakilinmu daya daga cikin matasan da suka amfana da samun wannan tallafi na aiki, duk da cewa yace yana bukatar a sakaya sunan sa ,ya ce babu abinda zai ce sai godiya sakamakon yadda a baya yaketa gararanba, wajan neman aiki amma abin yaci tura, yace amma ta hanyar wannan bawan Allah "Na sami aikin " in ji shi.
Sai dai Haruna Shehu bai tsaya nan ba in da ya bayyana cewa mafi yawan matasan arewa suna rasa aikinyi ne saka makon rashin masu tallafawa, ya ce da ana samun jagorori irin Alhaji Abdullahi Abubakar da wuta ta mutu, saboda mafiya yawan matasan Arewacin kasan nan ba zasu shiga bangar siyasa ba.