Bangarori Uku Ne Ke Jayayyar Shugabancin APC A Sakkwato

Bangarori Uku Ne Ke Jayayyar Shugabancin APC A Sakkwato

 

A jiya Alhamis babbar kotun kasa a birnin tarayya a Abuja ta daga sauraren karar da ke gabanta kan wane ne shugaban APC a jihar Sakkwato har sai yanda hali yayi. 

A yanzu bangarori uku ne ke fadin su ne shugabannin jam'iya a jihar ta Sakkwato.

Bangare na farko shi ne wanda shugaban jam'iyar na rikon kwarya Alhaji Isah Sadik Acida ke jagoranta, wannan bangare suna karkashin jagoran APC a Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda kusan kashi 80 na magoya bayan jam'iyar suna yi ne saboda soyayyar da ke tsakaninsu da shi, kuma shi ne ke dauke da nauyin jam'iyar a jiha, za a yi mamakin kiran wasu shugabannin APC ba wadanda Wamakko ya aminta da su ba.
Akwai bangaren Mainasara Abubakar Sani karkashin jagorancin Sanata Abubakar Gada, sai kuma bangaren Sirajo Abubakar dake biyayya ga dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Abdullahi Balarabe Salame tare da hadin guiwar kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Aminu Muhammad Acida.
Bangaren Sirajo Abubakar ne ke jayayya da bangaren Mainasara Sani  kan shugabancin jam'iyya a jihar Sakkwato, a bangare guda kuma bangaren Isah Sadik Acida na ankarar da kotu kan wadannan masu jayayyar ba wanda yake da gamsassun hujjojin zama shugaban jam'iya a jiha.
Bangaren Isah Achida sun shiga shari'ar ne a matsayin masu sha'awa domin su an karar da kotu cewa masu jayayyar da juna su biyu ba wanda yake shugaban jam'iya, don haka a jingine hukuncin farko da aka yi.
  A halin da ake ciki shari'ar na gaban kotun daukaka kara don haka alkali ya roki masu korafi su shigar da maganarsu a can.