Dalilan Mu Na Son Shugabancin Najeriya Ya Dawo Arewa Maso Gabas A 2023--- Dattawan PDPn Yankin

Taron ‘ya’yan jam’iyyar PDP ya fitar da takardar bayan taro wanda Dakta Ali Bappayo Adamu ya sanyawa hannu a madadin kungiyar Dattawan shiyar.

Dalilan Mu Na Son Shugabancin Najeriya Ya Dawo Arewa Maso Gabas A 2023--- Dattawan PDPn  Yankin
Rikicin Neman Shugabanci a 2023
 

 

Sakamakon zaman kungiyar zauren Dattawan yankin Arewa maso gabashin Najeriya da suka yi kan tirka-tirkan son a bai wa yankin takarar shugabancin kasa dan ceto kasar daga halin da ta fada ya nuna cewa dan PDP daga yankin ne zai iya ciro wa Najeriya kitse a wuta.

 

Dattawan kungiyar PDP na shiyar, sun yanke hukuncin da bayyana ra’ayoyin su da kuma bayyana dalilan su da suke ganin ya dace a bar yankin ya fitar da dan takara kuma daga jam’iyyar su ta PDP.

 
Taron ‘ya’yan jam’iyyar PDP ya fitar da takardar bayan taro wanda Dakta Ali Bappayo Adamu ya sanyawa hannu a madadin kungiyar Dattawan shiyar.
 
Dattawan Sun roki da a duba yankin na arewa maso gabas ne a bar shi ya tsayar da dan takara  daga jam’iyyar PDP saboda arewa maso gabas nan ne yanki da bai taba yin shugaban kasa bat un lokacin mulkin su Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 1960 lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai.
 
 A cewar su tun lokacin aka bar arewa maso gabas a baya domin ba ta sake samun dan asalin ya zama shugaban kasa ba har a lokacin da siyasa ta sake dawowa mulkin a shekarar 1999.
 
Suka ce Abubakar Tafawa Balewa, ya yi iya kokari a lokacin da aka ‘yanta kasar daga hannun turawan  Ingila a shekarar1960, bayan kuma akwai mutane hazikai da suka dace su zama shugaban kasa daga yankin amma ba’a ba su damar ba.
 
Sun koka kan yadda a Shekaru da dama ‘Ya’yan yankin kudancin kasar sun rike shugabancin kasa inda Olusegun Obasanjo, ya yi shekara takwas Goodluck Ebele Jonathan, shi ma ya yi shekaru bakwai, sannan sai Marigayi  Umaru Musa Yar adu’a, wanda ya yi shekara uku, wanda shi dan arewa maso yamma ne ba dan arewa maso gabas, sannan duk wannan yawan shekarun da PDP tayi tana mulki yan kudu ne suke yi ba yan arewa ba
 
Sun kara da cewa tsananin bala’in da yankin ya fada wannan dan yankin  na arewa maso gabas zai iya shawo kan matsalar kasancewar sa dan asalin yankin wanda yasan matsalolin kuma zai iya magance su.
 
A yanzu haka wannan shiya na cikin halin kunci na rashin tsaro na yan bindiga da makamantan su kuma ya girgiza tattalin zarzikin  kasar nan ba iya yankin kadai ba kuma har ya tsallaka zuwa wasu sassan yankin kudanci kasar nan.
 
Takardar ta kara da cewa yana da kyau jam’iyyar PDP tayi taka tsantsan wajen tuntuba da karbar shawarin masu ruwa da tsaki da ya kamata domin bai wa jam’iyyar ta PDP damar kada jam’iyya mai mulki a lokacin zabe.
 
Sannan suka ce dan takarar ya zama fitacce a ciki da wajen Najeriya wanda kuma bai da matsala ta banbancin addini ko na bangaranci.
 
Daga nan sai takardar tace muddin jam’iyyar PDP tana son cin zabe a 2023 dole sai ta tsayar da dan takarar da yake da wannan cikar ka’idoji, gaza fitar da shi kuma zai zama koma baya da kasa tabuka komai har jam’iyya mai mulki ta koma kan karagar ta na mulki.
 
Daga Habu Rabeel, Gombe.