Ɗa Ga Shugaban Ƙasa Buhari Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Ya Koma PDP
Ɗa Ga Shugaban Ƙasa Buhari Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Ya Koma PDP
Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Daura Da Sandamu Da Kuma Mai'adua A Jihar Katsina Kuma Ɗa Ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Honarabul Fatuhu Muhammad Daura Ya Ba Da Sanarwar Ficewa Daga Jam'iyyar APC.
Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Da Ya Rubuta Wa Majalisar Tarayya Domin Sanar Da Zauren Majalisar Matakin Da Ya Dauka Daga Ranar 13 Ga Watan Yuli, 2023.
Honarabul Fatuhu Muhammad Ya Ce Ya Jingine Katinsa Na Jam'iyyar APC Mai Lamba KT/DRA/10/0002.
Daga Karshe Ya Yi Godiya Ga Jam'iyyar APC Bisa Damar Da Ta Bashi Da Ya Wakilci Kananan Hukumomin Daura Da Sandamu Da Kuma Mai'adua A Zauren Majalisar Dokokin Tarayya.
managarciya