Daga Awwal Umar Kontagora, Minna.
Kungiyar kwankwasiyya Nation Ward ta yabawa jam'iyyar NNPP da kungiyoyin goyon bayan takarar shugabancin kasa, na Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, bisa yadda suka jajirce wajen ganin an zabi Kwankwaso a shugabancin kasar nan. Sakataren jam'iyyar NNPP ta jihar Neja, Kwamared Garba Muhammad Kwabo ne yayi yabon a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam'iyyar bayan bude sakatariyar da sanatan yayi yau laraba a minna.
Kwabo, ya cigaba da cewar jam'iyyar NNPP tazo dan kawo sauyi a salon shugabancin kasar nan musamman jihar Neja da ta samu jarabta tun daga kan mulkin jam'iyyar PDP, na tsawon lokaci da kuma kudar da jama'ar jihar ke sha a yanzu na talauci, rashin tsaro da rashin aikin yi ga jama'a.
Wajibi ne duk mai son cigaban jihar nan, ya tabbatar yayi anfani da kuri'arsa wajen ganin an kawar da jam'iyyun nan daga karagar mulkin jihar nan dan ceto rayuka da tattalin arzikin kasar nan. " Muna bukatar canjin gwamnati da irin salon da yan jari hujja suka karfafawa jihar nan, ya kamata duk wani mai kishi ya tabbatar yayi anfani da damarsa wajen anfani da kuri'arsa idan lokaci yayi dan samar da gwamnati mai kishin kasa", inji shi.
Da yake karin haske, daya daga cikin jigon jam'iyyar a yankin kananan hukumomin Rafi, Munya da Shiroro, Hon. Ahmad Awaisu, ya bayyana bude sakatariyar jam'iyyar da Sanata Kwankwaso yayi a yau tamkar wani sauyi ne aka kaddamar ga tsarin dimukuradiyyar jihar nan.
Jam'iyyar mu tana da yan takarkaru daga kan shugabancin kasa, sanatoci da majalisar wakilai da ta jiha har kan kujerar gwamna, wanda ina da tabbacin idan muka samu nasarar wannan babban zaben mai zuwa, za a samar da gwamnatin da al'ummar jihar nan zasu yi na'am da shi.
Hon. Awaisu, ya nemi matasa da su kaucewa shan kayan maye, anfani da makamai a lokacin da hukumar zabe ta bada damar fara yawon neman zabe, domin matasan nan su muke tsammanin zama shugabannin nan bada jimawa ba.
Jam'iyyar dai ta gudanar da sabon zaben fidda gwani na kujerar gwamna inda ta bayyana mamallakin jaridar Blueprint, Alhaji Muhammad Idris Malagi ( Kakaki Nupe), yayin da Alhaji Ibrahim Muhammad Sokodoke ( Talban Samarin Nupe) yake ikirarin shi ne halastaccen dan takarar kujerar gwamnan jihar da ya samu nasarar zaben fidda gwani inda yayi wa yan takarkaru biyu kaye.
Ta'addamar takarar kujerar gwamnan dai na daga cikin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP a jihar Neja, da ake kyautata zaton dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa zai walwale bayan wata ziyarar masu ruwa da tsaki a jihar Neja da ya fara yau.
Dukkanin yan takarkarun kujerar gwamnan da takaddama kan kujerar ba wanda ya halarci taron bude sakatariyar.