NDLEA Ta Kama Tsohon Soja Dan Shekara 90 Dake Kai Wa 'Yan Bindiga Kwayoyi A Sakkwato 

NDLEA Ta Kama Tsohon Soja Dan Shekara 90 Dake Kai Wa 'Yan Bindiga Kwayoyi A Sakkwato 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce dakarunta sun kama wani Soja mai ritaya ɗan shekara 90 bisa zargin kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi. 

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce mutumin mai suna Usman Adamu, ya shiga hannu ne a Mailalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni, jihar Sakkwato. 
The Cable ta rahoto kakakin hukumar na cewa an kama wanda ake zargin ɗauke da hodar Iblis mai nauyin Kilo 5.1kg.