Ƙaramar Hukuma Na Buƙatar Jami'an tsaro cikin gaggawa a jihar Kebbi
Yanzu haka dai maganar nan da nike daku wasu yankuna ko kauyuka da dama sun gudu sumbar kauyukansu saboda kisan kiyashi da ake musu ba daddaukawa.
Ƙaramar Hukuma Na Buƙatar Jami'an tsaro cikin gaggawa a jihar Kebbi
Mai girma Shugaban Karamar Hukumar Shanga Honarabul Aminu Muhammad Arzika Tafidan Shanga ya yi zama na musamman da dukkanin masu ruwa da tsaki na ƙaramar Hukumar a ofishinsa domin shawo kan matsalar tsaro wacce yanzu haka ta addabi wannan ƙaramar hukumar , inda suka tattauna kan cewa zama lafiya shi ne abin da muke bukatar ya wanzu a wannan ƙasa tamu ba tashin hankali ba "cewar Shugaban".
A cikin tattaunawar kuma an tattauna ne domin duba da nazarin ina ne matsalar take domin a samu damar magance ta, maimakon ayita kashin mutane ba-gaira-ba-dalili wanda ba shida amfani a cikin kowace irin al'umma.
Yanzu haka dai maganar nan da nike daku wasu yankuna ko kauyuka da dama sun gudu sumbar kauyukansu saboda kisan kiyashi da ake musu ba daddaukawa.
Muna rokon Allah ya bayyana muna inda matsalar take ya kuma bada ikon maganceta cikin sauki domin Shi mai ikone akan haka.
Haka ma ya nemi a kawo masu jami'an tsaro cikin gaggawa domin abin da ke faruwa ya kai masu maƙura suna buƙatar jami'an don wanzar da zaman lafiya a yankin.
managarciya