Daga Babangida Bisallah
An yi kira ga 'yayan jam'iyyar APC a jihar Naija, da su dunkule waje daya kar su bari zaben shugabancin jam'iyya ya raba kawunan su dan fuskantar zabukan 2023 mai zuwa.
Dan takarar shugabancin karamar hukumar Labun Honarabul Zakari Muhammad Kuchi ne yayi kiran ganin yadda aka tada jijiyar wuya a zabukan shugabancin jam'iyya a matakin gundumomi da kananan hukumomi.
Zakari Kuchi ya cigaba da cewar shugabanci Allah na bada shi ne ga wanda yaso kuma a lokacin da yaso, kuma ba yadda za a sanya sama da mutum daya su nemi matsayi daya a ce kowa ya yi nasara, dole wani ya samu, wani kuma ya rasa, dan haka wadanda suka samu nasara su rungumi kowa dan a gina jam'iyya tare.
Dangane da shugabancin jam'iyya da aka ba da kujerar ga yankin Neja ta Arewa kuwa, dan siyasar ya nemi 'yayan jam'iyyar da ke alhakin zabowa, da su rungumi hanyar sulhu tsakanin 'yan takarar kujerar, idan ma sulhun bai yiwu ba su bari a tafi zabe kuma a tabbatar an yi zabe cikin lumana ba tare da sanya bangar siyasa ba.
Ya cigaba da cewar, sanin kowa ne irin namijin kokarin da gwamnatin APC ta kawo a kasar nan wajen gina kasa da samar ma ta alkibla mai inganci tare da yaki da 'yan ta'adda da masu yiwa zaman lafiyar kasar zagon kasa, ba za a samu cigaba da wannan ginin ba, muddin kasa ba ta zaune lafiya.
Saboda haka wajibi ne ga 'yayan jam'iyya da su hada kai tsakanin su, sannan al'umnar kasa za su cigaba da ba su goyon baya. Kananan hukumomi su ne matakan da talaka ke takawa wajen samun biyan bukatarsa, idan mu ka samar da shugabancin jam'iyya mai kishin kasa, lallai za a samar da shugabannin masu kishin talaka da za su taka rawar gani a bangaren kananan hukumomi.
Honarabul Zakari Kuchi, ya nemi al'umma da su tabbatar da sun mallaki katin zabe dan fuskantar zabuka masu zuwa, kamar yadda gwamnati ke hankoro a zabukan 2023 zaben al'umma ne zai yi tasiri ba doki dora ko murdiyar zabe ba.
Kamar yadda hukumar zabe ke bayyana wa ga sakamakon sabunta rajistan zabe kusan arewacin kasar nan mu ke baya, lokaci yayi da manyan yankin mu, iyaye zasu falka daga dogon baccin da suke yi wajen wayar da kan al'umma muhimnancin katin zabe, domin da shi ne kawai za mu iya baiwa gwamnatin APC damar cigaba da ayyukan alheri da ta faro a kasar nan.