‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a shingen binciken ababen hawa

 ‘Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a shingen binciken ababen hawa
 
 
Sojoji biyu ne aka kashe da sanyin safiyar Laraba a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani shingen binciken sojoji da ke unguwar Imo/Abia iyaka na Ekenobizi a Umuopara a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia.
Jami'in soja da ya yi magana da manema labarai ya ce 'yan bindigar sun zo ne da karfen 6:18 na safe suna cikinmotar alfarma Lexus fara, ba a iya gane nambar motarsu.
Laftanal Kanal Jonah Unuakhalu a bayanin manema labaransa ya bayyana kawo harin da aka yi.
 
 
 Abbakar Aleeyu Anache