Zaben fidda-gwanin APC: A. A Jinjiri Ya Maka Bashir Machina Kotu

Zaben fidda-gwanin APC: A. A Jinjiri Ya Maka Bashir Machina Kotu

 
 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

 

 

Ga dukan alamu, zaben fidda-gwani da jam'iyyar APC na Sanatan Arewacin Yobe ya bar baya da kura, wanda ya jawo a ranar Jummu'a daya daga cikin yan takarar, Abubakar Abubakar Jinjiri, ke kalubalantar nasarar da Bashir Sheriff Machina ya samu zuwa kotu.

 
 
Hon. Machina wanda ya lashe zaben da kuri'u 289 a zaben, wanda kuma yake sa-toka sa-katsi tsakanin sa da shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.
 
 
Haka zalika, bayan da Lawan ya sha kasa a zaben fidda-gwani na shugaban kasa da APC ta gudanar, ya gamu da turjiyar Machina bisa kin janye masa ya ci gaba da jan zarensa a kan kujerar Sanatan Arewacin Yobe, duk da goyon bayan da yake samu daga uwar jam'iyyar APC ta kasa.

 
 
A. A Jinjiri ya na daga cikin jerin yan takarar da suka mika sunayen su domin kalubalantar zaben fidda-gwani a jihar Yobe, a gaban mai shari'a Fadima Murtala Aminu ta Babbar Kotun Tarayya (Federal High Court), da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
 
 
Da yake zanta wa da manema labarai a gaban kotun, Lauyan mai kara, Barr Usman Lukman Nuhu, ya bayyana cewa wanda yake wakilta ya na kalubalantar Machina, tare da uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta jihat Yobe, hadi da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), bisa rashin sanya sunan shi a cikin yan takara. 
 
 
Ya kara da cewa, an hana Jinjiri ya shiga cikin zaben fidda-gwani na Sanatan Arewacin Yobe, duk da kuwa yadda ya halarci wajen da aka gudanar dashi.
 
 
“Kuma nayi imani cewa kuna da kofi na takardar sakamakon zaben fidda-gwanin, wanda da kanku na san kun tabbatar babu sunan wanda nake bai wa kariya a takardar sakamakon zaben. " in ji shi.
 
 
Har wala yau, ya ce, kin saka sunan dan takara abu ne wanda ya saba wa dokar kundin tsarin mulki ta sashe na (84) da karamin sashe na (3 da 4) na dokokin zabe. 
 
 
Bugu da kari, akwai kararrakin zaben fidda-gwani guda bakwai wadanda ke kalubalantar sakamakon zaben fidda-gwanin da jam'iyyar APC ta gudanar.

 
 
Haka kuma, mai shari'ar ta ayyana ranar 21 ga watan July 21, 2022 a matsayin lokacin fara shari'ar.