Majalisar Dattijai Ta Yi Watsi Da Bukatar Buhari Kan Sake Gyaran Dokar Zabe

Majalisar Dattijai Ta Yi Watsi Da Bukatar Buhari Kan Sake Gyaran Dokar Zabe

Majalisar dattijan Nijeriya a ranar Laraba ta yi watsi da bukatar shugaban kasa ta neman sake yiwa dokar zabe ta 2022 gyaran fuska.

Kudirin dokar kan sake yi masa gyaran fuska sanatoci sun yi watsi da shi ne a lokacin da za a shiga karatu na biyu.

Kudirin ya tsallake karatu na farko duk da akwai managanar dakatarwa daga kotu.
Shugaban majalisa Ahmad Lawan ya kalubalanci hurumin kotu kan abin da ya shafi majalisa don sanatoci ne kawai ke da hurumin jefar da kudirin a gaban majalisa.
Sanatoci sun jefa kuri'ar dakatar da kudirin ka da ya shiga jerin wadanda za a yi wa karatu na biyu, hakan kuma ya tabbata.
Shugaban kasa Buhari ya aikawa majalisa ta yi wa dokar zaben gyaran fuska ta cire sashen da ya nuna duk wanda ke rike da kujerarar gwamnati dan siyasa da aka nada ko ma'aikacin gwamnati dake son ya shiga zaben wata kujera ta siyasa ya yi murabus wata shidda kafin ranar babban zabe na kasa.

Buhari ya nemi a yi wa dokar gyaran fuska domin ta ci karo da dokar kundin tsarin mulki da ya baiwa mutum damar ci gaba da aikinsa har sai sauran wata daya kafin zabe sannan ya yi murabus.