ƘADDARA TA: Fita Ta 14

ƘADDARA TA: Fita Ta 14

ƘADDARA TA:


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 14*


                  ~Uniform ɗin ta bata farin riga ne da zani baƙi da ɗankwali baƙi, jikinta a mace ta karɓa tana kuka tasa, share hawayen tayi ta zauna tayi tagumi tana hawaye, jakadiya ce ta shigo tace "duk ku fito zakuje kuyi girki"
kallonta tayi da ganin matar muguwa ce, a hankali ta tashi suka fita tareda salma, mayan tukwanen data gani su suka tsinka mata rai taya zasu fara wannan girkin?
ganin sun fara itama tasa hanu cikin lalacin data saba na rashin iya aiki, jakadiya ta daka mata tsawa tace "zakiyi aiki ne ko sai nasa an hukuntaki? nan ba gidanku bane sakin jiki zakiyi kiyi aiki"
jikinta yana rawa ta fara aikin duk da bada karfi ba har yanzu amma tana kokari sabida batason duka ko wani abin na wahala, rana ne ya fito sosai yana haska farin fatarta ga zafin wuta, ta gaji sosai kawai ta fara kuka tana aikin, bayan sun gama girki akace suje su ɗibo ruwa, sukaje dam na gidan sarkin suka fara ɗibo ruwa suna kaiwa drum ɗin da ake girki da ruwan ciki, ta gaji har jiri take ji ga yunwa da yake azazalanta, katon roban ruwa ne a kanta cike fam da ruwa ga dogari da bulala a bayansu duk wacce tayi abinda ba daidai ba saide taji saukan bulala a bayanta, tangal tangal take tafiya ruwan kamar zai kife, tana lumshe ido batasan lokacin data zube kasa tareda ruwan ba, jiƙata ruwan yayi, salma ta waro ido tana kallonta cikin tausayinta, bulala taji saukanshi a bayanta, ihu ta fara yana shoɗa mata dorina, da kyar ta tashi ta ɗau roban daya tsage jikinta a jiƙe da ruwa taje ta kara ɗibo wani ta ɗaura a kanta yana yoyo amma haka ta daure ta rike tana tafiya dashi, kafafunta da hannayenta kamar basa jikinta, da haka suka gama ɗiba ruwan aka raba musu kananan roba, ta kalli salma cikin yunwa da azaba har idanunta sun canja kala tace "me zamuyi da roba?"
tace "muje layin abinci kafin ya kare a kanmu"
salma ce a gaba ita kuma tana baya suka shiga layi, abincin kamar na cin jarirai kaɗan kaɗan suke zuba musu, tana tsaye tana jin jiri rana kuma har yanzu basu iso kansu ba, saida aka kusa su kafin akace abinci ya kare, salma wacce ta samu kaɗan tazo tace "kinga bamuzo da wuri ba har abinci ya kare"
tace "salma rikeni jiri nakeji"
riketa salma tayi suka koma ɗaki, abincin data samu tace "gashi kici"
tace "kefa?"
ta girgiza kai tace "ban kaiki jin yunwa ba kici"
karɓa tayi ta fara ci, babu daɗi abincinsu na kauye yafi wannan daɗi, bata koshi ba ko kaɗan, salma ta bata ruwa tasha sannan ta kwanta tana jin rashin lafiya yana shirin kama ta.

meenat ammi ce ta riketa suka tafi ɗaki, tace "ammi meyasa aka canjamin kaya zuwa wannan me dattin?"
ammi ta haɗa mata ruwan wanka da sabulai da shower gel masu tsada ta bata towel tace "shiga kiyi wanka ki tabbatar kin wanke kanki"
ɗaura towel ɗin tayi sannan ta shiga ciki, kwashe kayan ammi tayi ta fitar waje tace a ƙona, shiga toilet ɗin tayi da sauri meenat ta fara rufe jikinta, tsaki taja ta ɗau shampoo ta fara wanke mata gashinta da yayi datti, ruwan zafi sosai ta kara haɗawa tasa turaren wanka a ciki, da kanta ta cire kunya tayi mata wankan, datti sosai ta fitar a jikinta sannan tace "ki kara wanka saiki fito"
tace "to ammi"
cikin kunya ta gama wankan wai ammi taga jikinta, ɗaura towel ɗin tayi a kirji gashinta har gadon bayanta gashi baƙi ƙirin, ammi ta nuna mata stool tace "zauna"
zama tayi ta jona dryer ta fara busar mata gashin, saida gashin ya bushe sannan ta shafa mata man gashi me kyau sannan ta shafa mata lotion me kamshi, simple dogon riga ta bata me kyau pink tasa, turare ta fesa mata sannan tace "bari na kawo miki abinci"
fita tayi ta dawo da juice da kuma snacks dayawa tace "oya ci"
ci ta fara a hankali tana kallon Ammin, saida ta koshi tace "na koshi ammi ina wayata?"
tace "kina bacci aka shigo gidannan akayi sata kuma harda wayata da naki amma yayanki hameed ya siya miki sabo"
ɗaukan sabon iphone16 dake cikin kwali tayi ta mika mata, cikin jin daɗi tace "wayyo na gode"
buɗewa tayi tana murna, ammi tana kallonta tace "zansa ido akan ƴata da yaddan Allah babu me kara cutar da ita, sannan zanyi duk yadda nasan zan iya domin ɓoye mata abinda ya faru da ita, duk wanda naga kuma zai tuna mata sai inda karfina ya kare akan meshi"

hameed cikin farin ciki yake sabida meenat ta dawo, kallo ɗaya aneeta tayi mishi ta ɗauke kai, zama tayi akan kujera tana tunanin yadda zata fara sabon shiri, a hankali ya zauna a gefenta ji tayi ya rike hanunta yana wasa dashi, ɓata rai tayi, a hankali ya kwantar da ita akan kujeran kissing ɗinta zai fara ta bigeshi, abin ya isheshi haka ya gama iya hakurin da zai iya, danne hanunta yayi yana kokarin yi mata ta karfi, kokawa suka fara tace "ka sakeni bana sanka na tsaneka ka sakeni yarima"
murmushi yayi sannan ya kalli fuskanta da kyau, rike face nata yayi da karfi ya haɗa bakinshi da nata, zata rantse punishment yake mata domin huci yake, duka ta fara kai mishi a baya, hanunta ya rike ya ɗauko igiya ya ɗaureta tana jujjuya kai tana tureshi da kafarta cikin hasala ya ɗaure kafanta ya jata akan tile ɗin ya buɗe kofan bedroom ya wurgata ciki sannan ya rufe, fita yayi daga ɗakin kamar zai tashi sama, kaseem daya fito cikin sauri sabida ana nemanshi yaga yarima yana huci ya fita, shiru yayi ya kalli kofan ɗakin sannan ya kalli yarima daya bankaɗe kofar kamar zai ɓalla ya fita.
motarshi ya shiga da wani irin gudu yaja motan kamar zai ɓalla gate nasu ya fita daga gidan, Asmee da kallo ta bishi har ya fita a gidan, sai kuma ta kalli salma dake kusa da ita tace "wannan kuma waye shi?"
salma tace "wannan shine yarima hameed baya magana amma yana jin duk abinda ake faɗa"
tace "to meyasa baya magana? haka aka haifeshi?"
girgiza kai tayi tace "ba haka aka haifeshi ba yana magana amma ance faɗa yayi da ɗan uwanshi shine...."
shiru tayi ganin wata a bayanta, Asmee ta kalli wacce take bayansu itama tayi shiru sukaci gaba da aiki, kaseem ne ya fito da uniform a jikinshi amma fuskanshi babu walwala da alama yana cikin damuwa, da kallo Asmeeta ta bishi har shima ya fita, kallon salma tayi sannan ta juya baya taga babu kowa tace "wannan kuma waye?"
tace "wannan shima yayan meenat ne babban ɗan sarki sunanshi kaseem a duniya babu wanda yake so sama da hameed kullum zakiga yana tare da hameed ɗin kuma shi yake kula dashi sabida yarima hameed baida cikakken lafiya"
shiru tayi.

hameed gidansu alameen yaje, Allah yasa babu mama a falo kawai ya wuce ɗakin alameen, yana shiga kawai ya faɗa gado gefen alameen ɗin ya rufe ido yana hawaye, alameen dake bacci ya buɗe ido a hankali yana kallonshi, to yauma wannan aneetan ta kara ɓata mishi rai, shiru yayi mishi ya kara rufe ido yana baccinshi, saida yayi kuka me isanshi kafin ya fara bacci, bai koma gidan ba saida yayi kwana uku, ya manta da a kulle ya barta a ɗakin, shida alameen kawai suke zama baya son ma ayi mishi maganan gida sabida haushin komai yake ji.
sai a kwana na huɗu yaga daman komawa yayi kyau cikin black dress hanunshi rike da makulli yana juyawa alameen a gefenshi suna tafiya har wajen mota suka shiga yarima ne yake driving, gidansu sukaje, hon yayi aka buɗe gate ya shiga, fitowa sukayi tare Asmeeta wacce ta saba da wahalan gidan kallo ta bisu dashi kenan tun ranan daya fita bai dawo ba sai yau?
taci gaba da aikinta kawai, shiga ciki yayi alameen ya zauna a falo shi kuma ya wuce ɗakinsu, gabanshi ya faɗi ganin kofa a rufe, da sauri ya buɗe ya shiga, bedroom ɗin ya buɗe tana kwance kamar ta mutu, da gudu ya karasa ya ɗagata yana kwanceta, hanunta ya saki ya fara marin fuskanta a hankali sabida ta buɗe ido, a wahale ta buɗe ido tana kallonshi sai kuma ta kara rufewa, kwantar da ita yayi yaga hanunta da shatin ɗauri harma da kafanta, bathroom ya shiga ya haɗa ruwan zafi sosai a bathtub yazo ya ɗauketa ya shiga ya mata wanka, sannan ya fito da ita yasa mata kaya mara nauyi, fita yayi yaje kitchen ya haɗa tea baiga alameen ba kuma bai damu daya ganshi ba, kawo mata tea yayi tasha kaɗan sannan ta kwanta a jikinshi tana jin ciwo duk jikinta, magani ya bata na ciwon jiki sannan ya kawo mata abinci taci kafin ta kwanta ya rufata da bargo ya fita ya samu sultan ya dawo, rubutu ya mishi a waya kamar haka (a samo baiwa ɗaya tazo ta gyara ɗakinmu yayi datti)
bashi wayan yayi bayan ya karanta yace "to"
fita yayi domin duba baiwa, Asmeeta tana tsaye tana kallon meenat da alameen wanda suke rike da hanun juna suna hira suna zaga cikin cikin, banda hawaye babu abinda take yi, meenat fa matar hamma najeeb ce amma tasan yanzu ta mishi nisa zafi takeji idan tana kallonsu, meenat ce ta rungume Alameen cikin kewanshi da tayi tace "yaya shine baka kirana video call?"
riketa yayi yace "sorry baby"
rufe ido Asmeeta tayi zuciyanta yana bugu da sauri da sauri, ji tayi kishin da take taya yayanta yana ruruwa a zuciyarta, juyawa tayi a fusace zata koma ɗaki sukayi karo da sultan, da sauri tayi baya tace "sannu ban san kana bayana ba"
ya kalleta sannan ya kalli su meenat yace "meyasa kike kallonsu haka?"
tace "sabida naga abinda suke bai dace ba, ba aurenta yayi ba be kamata yana riketa haka ba"
murmushi yayi yadda take magana zuciyanta yana ci da wuta hamma najeeb nata take tausayi sabida ya faɗa soyayya da meenat tunda har ya iya ya furta tasan ya dami zuciyanshi ne, yace "to ai nan da kauye ba ɗaya bane sannan shi a matsayin yayanta yake sabida tun tana jaririya shi yayi renonta har ta girma"
shiru tayi a ranta tace "yanzu kuma matar wani ne kune baku sani ba"
yace "muje zakiyi aiki a ciki"
binshi tayi ganin ya shiga gaba, ciki ya shiga da ita, ɗakinsu hameed ya nuna mata yace "can zaki gyara yayi datti"
tace "to"
tafiya tayi tana kallon stair da kyar ta haura idonta a rufe sabida tsoro, ɗakin ta shiga da sallama, gani tayi babu wani datti amma wai a hakan datti suke kira, fara aikin tayi ta fara goge ɗakin da jikin kujerun da duk wani wajen da taga kura, shiga bedroom ɗin tayi batayi tsammanin akwai mutum ba, tsaki taja ganin babu wani datti kawai ta fara share kasan ba tareda ta kula akwai mutum kwance akan gadon ba, saida ta gama share kasan sannan ta hau gadon domin ta gyara ji tayi ta taka mutum, waro manyan idanunta tayi a firgice ta kalli Aneeta dake kwance akan gadon, sauka tayi aneeta ta tashi cikin masifa da ciwo da haushin da hameed yake bata tace "who the hell are you?"
shiru tayi tana kallonta sabida bata fahimci ma me take faɗa ba, ganin ta zuba mata wannan manyan idanunta masu kama dana aljanu dama ta tsaneta sabida itace ta dawo da meenat gidannan wanda koda yaushe tana fargaban meenat ta tuna abinda ya faru, tace "ba zakiyi magana ba kin zuba min wannan ƙazamin idanun naki?"
cikin rawan murya tace "da..da...dan Allah kiyi hakuri wallahi"
tsawa ta daka mata tace "kd wace irin ƴar kauye ce kazama? haka ake aiki ki hau gadon mutane babu excuse? shiyasa ko bayin gidanmu bana sarara musu sabida na tsani talaka idan kun samu waje kunada mugunta"
cikin masifa tace "out"
sam Asmee bata san me tace ba, ta kuma cewa "i say out"
bata fahimta ba ta tsaya kawai tana kallonta, da marin da ko hamma najeeb bai taɓa yi mata irinshi ba ta ɗauketa dashi, dafa kunci tayi da sauri ta ɓuya a bayan hameed daya shigo yanzu, tana huci tace "ba zaki fita ba?"
hanunta akan kuncinta tana kuka tace "zan fita"
fita tayi hameed ya kalli Aneeta wacce har jijiyan wuyanta ya tashi, komawa gadon tayi ta kwanta.
Asmee cikin kuka ta fita, a bakin kofa suka haɗu da meenat wacce ta shigo yanzu, da kallo ta bita ganin tana kuka kamar zata shiɗe, itama kallo ɗaya ta yiwa meenat ɗin ta fita daga ɗakin tana kuka, shiru meenat tayi jikinta yayi sanyi sai taji babu daɗi, taɓe baki tayi a ranta tace "ina ruwanki?"
wayanta ta fara latsawa ta zauna a sofa, sultan wanda ya rame sosai ya fito daga ɗaki ya zauna a gefenta yayi shiru, aje wayan tayi ta taɓa wuyanshi tace "ba rashin lafiya ba amma sultan me yake damunka? me kasa a ranka kake wannan raman? ba kace fadeel ya koma school bane ai zai dawo"
shiru yayi bai amsa mata ba, daga karshe ma kwanciya yayi ya ɗaura kanshi a cinyarta, shafa kanshi ta fara a hankali tace "akwai abinda yake damunka sultan ka faɗamin mana ba muna sharing matsalolin mu ba?"
cikin rawan murya yace "fadeel ba school yake ba barin gidannan yayi kuma na nemeshi sama da kasa ban sameshi ba"
shiru tayi, tana shafa kanshi tace "ina yaje?"
duk abinda ya faru tsakaninshi da Aneeta ya faɗa mata, salati ta fara jin abinda ya faru, tace "to meya hanaka faɗawa ya hameed ɗin gaskiya?"
yace "ba zai taɓa yadda ba domin a gabanshi abin ya faru"
tace "innalillahi mun shiga uku sultan yanzu ina zamuga fadeel? maraya ne shi gaba da baya mu kaɗai yake dashi, yanzu wani rayuwa zaiyi?"
kuka ta fara, shima sultan ɗin kuka yake yi.

ɓangaren hamma najeeb sam bai san ta inda zai fara siyar da gold ɗin ba, ya haɗu da ɓarayi suka sace gold ɗin ya mika komai wa Allah yayi niyan komawa gida dama bai ɗana arziki ba bale yaji zafin rashinshi, a ranshi yace watakila kuɗin ya zame mishi masifa shiyasa Allah ya hanashi amma yana addu'a idan har kuɗin alkhairi ne Allah ya kara bashi wasu gold ɗin, yanzu burinshi ya tara kuɗi a wannan dako da yakeyi domin ya samu ya koma kauye ya kula da matarshi da kuma kanwarshi da mimi, yana burin ya ɗan tara kuɗi kaɗan domin yayi musu siyayya sabida Ameena da yake ganin ba zata iya rayuwa da abincin da sukeci a kauyen ba, yana kewansu amma ya zama dole ya nemi kuɗi domin basu kyakkyawan rayuwa, da haka har yayi wata uku a karshen wata ya harhaɗa duk kuɗin daya samu ya shiga kasuwa ya siya musu kaya na yayi masu kyau, ya siya musu kayan abinci masu kyau da duk abinda yasan zasu buƙata, ya shirya tsaf domin komawa kauyensu, a tasha yake zaune yana jira motansu ya tashi, ji yayi ana ihu an kama ɓarawo ga mutane dayawa da suka taru suna dukan ɓarawon da mamaki yake kallon yaron baiyi kama ba sam da ɓarawo, fadeel wanda yake kuka yana rokon su kyaleshi najeeb yaji ya bashi tausayi da sauri yaje yana hanasu dukanshi, yace "ku tsaya mana kuji ta bakinshi tunda yace kuyi hakuri ku daina"
kallon fadeel ɗin yayi yana kuka sosai ya rikeshi, yace "meyasa kayi sata?"
yace "wallahi banida kuɗi ne kuma yunwa nakeji shine wasu sukace nazo nan nayi sata idan na sato dayawa zasu bani gold guda ɗaya saina basu abincin dana sata"
da mamaki yace "gold kuma? yara ne ko manya?"
yace "yara ne"
da sauri yace "zaka iya kaimu inda suke?"
yace "eh zan iya"
hakuri najeeb ya basu sannan ya biya kuɗin abinda ya sata hanunshi ya rike yace "muje ka kaini"
tafiya sukayi fadeel sai sharan hawaye yake yana tausayin kanshi, a wani kango suke suna shaye shaye toshe hanci najeeb yayi suka shiga, suna ganinsu suka ɗau jakan gold ɗin zasu gudu, da alama basu san darajan duwatsun gold ɗin ba, yace "ku tsaya ba abinda zan muku"
tsayawa sukayi amma a tsorace suke, yace "wannan jakan nawa ne kun kwace a hanuna ranan dana sauka a garinnan ku bani kafin na kira muku police"
yayi magana yana ciro karamin wayan daya siya, da sauri sukace "dan Allah yaya kada ka kira mana police wallahi zamu baka"
mika mishi sukayi ya karɓa yana murmushi yace "na gode amma meyasa kuke sata?"
duk suka faɗa mishi yunwa ne yasa suke sata, duk kuɗin da yake tare dashi ya cire ya basu suka karɓa suna godiya, kallon fadeel yayi yace "zamu tafi?"
a hankali yace "eh"
hanunshi ya rike suka fita, zamanshi a garin yasa ya gane ko ina, fadeel yace "aina ka samu duwatsun gold?"
yace "a ruwan garin mu"
tare dashi sukaje suka siyar, kuɗi ne makuɗai ya samu akan duwatsun, sujjada yayi ya godewa Allah daya bashi wannan arzikin a rana ɗaya, bayan sun fita ya cewa fadeel me ya kamata ya fara siya?
fadeel yace "ka fara siyan gida da mota sannan ka nemi sana'a me karfi"
murmushi yayi yana tuno irin rayuwar da zasuyi shida Ameena matarshi da kanwarshi Asmeeta.
tare da fadeel sukaje ya siya tsadadden gida da mota sannan a cikin kwana uku yasa hannun jari a company ɗin gold, gidan daya siya a unguwan masu hanu da shuni ne motar kuma fadeel ne yake ja sabida fadeel ya faɗa mishi duk abinda ya faru dashi hakan yasa yace fadeel zai zauna tare dashi, zai koma kauye ya ɗauko matarshi da kuma kanwarshi da ƴar kanwarshi wato mimi, cikin yaddan da yayi da fadeel ɗin ya danƙa mishi amanan komai da motan daya koya a wajen fadeel ya tafi yana me farin ciki da marmarin ganin sanyin idanuwanshi, ya zama cikakken namiji kyawunshi ya kara fitowa sosai ya kara kwarjini fiye da baya.
har ya isa kauyensu a hanyan shiga yaga wani tsoho yana zaune rike da kafanshi da alama ciwon kafa ne ya sameshi, fitowa yayi a motan yaje ya sameshi ya durkusa ya gaisheshi sannan yace "baba meya samu kafarka?"
ya nuna mishi ciwon da yake ƙafarshi sannan ya fashe da kuka me cin rai yace "ɗana ni nan da kake gani nasha wahala a rayuwata nayi kuɗi kuɗin da idan na faɗa maka yawanshi zakayi mamaki amma daga karshe yayana wanda na yadda dashi ya kwashe kuɗin da matarshi suka bar kasar nan, daga karshe saida na dawo kauye da shike ban taɓa haihuwa ba tunda nayi aure har matata ta mutu shiyasa na dawo nan ina noma to amma kafata taki har yanzu kafan ciwo yake yaki barina naje gona ance nazo na karɓi magani a wajen wani matashi anan amma nazo gidan babu shi mutane sunce tunda ya tafi birni bai kara dawowa ba"
da ganin jikin mutumin zaka san gaskiya yake faɗa domin kuɗi ya nuna a jikinshi, yace "sannu baba, idan babu damuwa zan ɗaukeka mu koma gidana a birni sannan zan kula da kai nine me bada magani a wannan kauyen kuma zan baka magani yanzu"
da mamaki yace "kaine me bada maganin?"
jijjiga kai yayi yace "nine"
hanunshi ya rike sannan ya karɓi fartanyar ya aje a gefe a hankali suke tafiya har suka isa wajen mota ya shiga, shima najeeb shiga yayi yaga motan maimakon ya wuce gida saiya wuce bakin kogi domin tsinko maganin da zai warkar da ciwon kafan, parking yayi yana kallon ruwan da yayi sanadiyar arzikinshi saida ya tsinki maganin kafin yasa a mota har zai tafi sai yaji ba zai iya tafiya bai kara taɓa ruwan nan ba domin bai san ranan da zai kara dawowa ba watakila idan ya tafi ya tafi kenan, fita yayi yaje wajen ruwan yasa kafa da hanu yana wankewa yana murmushi me sanyi, fita zaiyi ya taka dutse faɗuwa yayi, runtse ido yayi zai tashi wani abu yace ya ɗau dutsen daya takan, ɗauka yayi da mugun mamaki yake kallon katon dutsen asalin gold ɗin daya ɗauko, rufe ido yayi yace "ya Allah ka bani harma fiye da wanda na rokeka"
hawaye masu zafi suka fara wanke mishi fuska, a hankali yasa hanu ya ɗau ɗayan da kafanshi yake kai, zama yayi a wajen ya fara kuka da kyar ya lallashi kanshi ya koma motan, mutumin yace "ɗana kukan me kake?"
ya nuna mishi dutsen yace "wannan shine silan arzikina kuma Allah ya kara bani"
murmushi yayi yace "Allah ya baka ne sabida taimakon da kayi, a duk lokacin daka taimaki wani Allah zai taimakeka ta hanyan da bakayi tsammani ba, shekaru dayawa da suka wuce wannan ruwan turawa suna zuwa sabida dutsen gold da yake ciki, saida suka kwashe duwatsun gaba ɗaya kafin suka bar ruwan, har kwashe ruwan sunyi duka sabida basa so wasu su anfana dashi, Allah ne yaga zuciyarka me kyau ya baka wannan dutsen amma kullum ana zuwa ana dubawa babu ka godewa Allah domin babu ta yadda baya taimakon bayinsa"
yace "a kullum cikin gode mishi nake da akwai da babu"
har suka isa kofan gidansu ya tsaya da motan, mutanen gari suka fito suka taru domin ganin waye da wannan zazzafan motan da basu taɓa ganin irinshi a wannan kauyen ba?
fitowa yayi fuskanshi da farin ciki, lumshe ido yayi sai yanzu yake tuna daren daya kasance da matarshi, so yake ya kara koda sau ɗaya ne domin yayi kewanta sosai, tun daga bakin kofa ya fara kiran sunansu "Ameenah? Asmeetah? Mimi?"

_Jiddah Ce..._
 08144818849