BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUƘARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
FITOWA TA ISHIRIN DA UKU
~~~~Sai ƙarfe 10am sa'annan suka barmu shiga gurinsa zuwa lokacin su Mama sun iso , a tare dasu muka shiga yana kwance a saman gado idanuwansa rufe amman da alamu ba bacci ya keyi ba.
Kallo ɗaya na yi masa na gano ƴar ramar da ya yi daga jiya zuwa yau sai hasken daya ƙara , "hakan ma yafi kyau", na faɗa a saman leɓe na.
Hajiya Inna ce ta yi azamar isa gurin sa sannan ta riƙe masa hannu, sai lokacin ya buɗe idanuwansa karafff muka haɗa idanuwa ya sakarmin murmushi nima na mayar masa kana na yi azamar janye fuskata a kansa.
Kallon Hajiya Inna ya yi ya ce "Tsohuwa mai ran ƙarfe", "ƴar dariya ta yi me nuna tsantsar farin cikinta sannan ta ce "Shalelena, ya jikin naka?".
"Alhamdulillah ƴar tsohuwas."
Ɗan zaro idanuwa ya yi waje sannan ya yi azamar sanya hannu ya rufe bakinsa ya ce "Mama barka da safiya".
Dariya muka sanya mu dukan mu yayin da Mama ta gurgusa wurinsa ta ce "Alhamdulillah Haidar ya jikin , na jira ku ƙara gaisawa da Mama ne wai".
A haka muka wuni a asibitin ƙarfe 7pm suka bamu sallama muka koma gida gaba ɗayan mu, domin kuwa yaji sauƙi sosai sai ɗan abinda ba'a rasa ba.
Da daddare kuwa a Parlourn Hajiya Inna muna zaune muna fira, Ya Haidar ya kalli Baba ya ce "insha Allahu ranar monday za'a zauna kotu , tunda kaga matsalar data gitta itace tasa aka dakatar da'ita, kuma insha Allahu zan haɗa da wanda suka yiwa Baba duk a yi abin gaba ɗaya , jiya nasa DPO da kansa ya basu takardar sammaci, kuma an basu dama su nemi lauya."
Kallonsa Baba ya yi a sanyaye sannan ya ce "ni naso a ajiye maganar komai tunda har sunce sunyi nadama a basu dama ta ƙarshe, batun hukuncin abinda suka aikata ma Yaya kuwa hakan yana da kyau ayi masu hukunci dai dai da laifinsu gaskiya ne."
Hajiya Inna ta ce "hakan ya yi ai wallahi ni ba abinda zance dasu Murtala sai Allah ya yi min sakayya dasu , bansan me zuri'ata ta yi masu ba suke bibiyarta da sharri har haka ba".
Sai hawaye tarrrrrr..... Sosai take kuka wanda ya tayar da hankalin mu dukan mu.
Ban taɓa ganin kukan Baba ba balle na Ya Haidar ba, amman a ranar naga kukan su dukansu hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba, ko ba'a gayamin ba na tabbata mikin rasuwar marigayi ne ya ɓalle masu.
Sai gamu mu dukanmu muna kuka aka rasa me lallashin wani.
A wannan daren ma kam ba muyi bacci , yadda muka ga rana haka muka dare mu dukan mu, sai labarin yadda suka yi rayuwa da margayi Abban Ya Haidar take bamu, wani wurin mu dara wani gurin kuwa kuka muke yi.
Su Ahmad kaɗai ne suka samu bacci a ranar, hatta Mama a sashen Hajiya Inna muka kwana da ita zaune.
★★★★★★
Kotu ta cika maƙil da ɗan mutum domin kuwa kowa yana son yaji irin hukuncin da za'a yankewa waƴannan bayin Allah, bugu da ƙari jin cewar ƴaƴan babban mutum ne, kuma ƴan uwansa sune suka sace yaran domin samun kuɗin fansa.
Alƙali ne ya shigo cikin kotun lokaci ɗaya waƴanda ke zazzaune suka miƙe wa ƴanda basu samu gurin zama ba kuwa , suna a tsaye dama.
Sai da ya zauna kana a ka shigo dasu Baba Bello da Baba Murtala, kana daga bisani aka shigo dasu Baba Sunusi, su dukansu 31 sun samu halartar gurin sai kuma mata yensu da ƴaƴansu da sauran al'ummar gari.
Bayan angama zayyano masu laifukan da ake zargin su da aikata .
Ba tare da wani ɓata lokaci ba lauyan mai ƙara ya miƙe ya fara gabatar da hujjojin sa.
Na farko zargin da ake yi masu da kashe Alh Aminu Sulaiman Wurno, nan ya gabatar da recording ɗin muryar Hajiya Umma sannan aka gabatar da abinda ya girgiza al'umma , damu kanmu waƴanda ke zaune a cikin wurin , bakomai bane face CCTV Camera dake manne a jikin ɗakin margayi wacce ba wanda yasan da'ita sai mahaifinmu.
Lokaci ɗaya sai ga fuskokin su sun bayyana muraran, wallahi kowaye kai kaga yadda lokaci ɗaya Baba Bello da Baba Murtala da taimakon Baba Usman da Baba Amadu da Baba Sunusi suka yiwa Margayi yankan rago, sai hankalinka ya tashi.
Fiye da rabin al'ummar dake zaune a cikin wurin hawaye ne ke tarara a cikin idanuwanmu , dole ne hankalin mutum ya tashi idan har yaci karo da wannan mugun abun.
Hatta shi kansa alƙali hawaye ne ke tarara a cikin idanuwansa.
Waƴanda keda dakakkiyar zuciya ne kaɗai basu zubar da hawaye ba a lokacin, Ya Haidar kam ficewa ma ya yi daga cikin wurin hankalinsa a tashe yana me zubar da hawaye.
Kamar yanzu ne suke ai watar da abin hakan yasan ya zuciyoyin al'umma suka dugunzuma.
Har waƴanda ke zaune a ɗakunan su , suna kallon yadda komai ke gudana ta hanyar amfani da wayoyinmu na zamani da mafi yawan yanzu dasu ne ake amfani domin sau ƙaƙawa rayuwa.
Ganin yadda Ya Haidar ya fita ne ya sanyani miƙewa daga gurin da nake nabi bayan sa.
A harabar gurin na iskosa ya haɗa kai da gwiwa yana faman zubar da hawaye.
A karo na farko a rayuwata na sanya hannu na ɗago fuskansa na sakar masa murmushi kana na sanya hannuna ina ɗauke masa hawayen dake saman kuncinsa.
Ba tare dana ce dashi komai ba naja hannunsa ya miƙe tsaye muka koma ciki.
Muna gabb da shiga wurin na saki hannunsa , a tare muka shiga ya yi wurin zaman sa haka nima na yi nawa.
Anjima zazzaune kana alƙali ya ɗago da kansa daga duƙen da yake , nan al'umma suka sarara daga abinda suke yi kana ya yi gyaran murya ya ce "innalillahi wa innah ilaihirraji un!!!, Allah ya yi mana tsari da aikata dana sani, Allah ya kare mana zukatanmu da aikata ɓarna, Allah ya tsare mana imanin mu."
Kana ya koma sa hannu ya ɗauke ƙwallar data zubo masa cikin idanuwansa.
Ya koma ɗago kansa ya kai kallonsa kansu Baba Bello da kawunan su ke ƙasa gwiwowinsa duk a sanyaye, sai yanzu suke da sunsanin abinda suka aikata akan wani ɗan ƙaramin buri nasu , wanda a lokacin suke ɗaukesa *BABBAN BURI* amman yanzu da duniya ke neman juya masu baya suke ganinsa ƙarami.
Ya girgiza kai sannan ya juya ya kalli al'ummar dake zaune a wurin ya ce "ko lauyan waƴanda ake ƙara yana da abin cewa?".
Sosai kowa ya kashe kunne domin yaji me lauyan zai faɗa.
Miƙewa ya yi tsaye da alamu koshi kansa yaci kuka ya ce "ya megirma mai Shari'a ina neman afuwa da kuma neman wannan kotu mai adalci data yankewa waƴannan bayin Allah hukunci dai dai da laifinsu cikin ƙanƙanin lokaci, nagode".
Ya faɗa yana mai duƙawa alamun girmamawa sannan ya zauna a mazauninsa kansa a ƙasa.
Gyaɗa kai alƙali ya yi sannan ya ce "ko waƴanda ake zargi suna da abin faɗa?."
"Shuru ka keji ba wanda ya yi magana daga cikinsu........
ƳAR MUTAN