DUHU DA HASKE: Fita Ta 17
DUHU DA HASKE:
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 17*
~Waje Ameesha ta samu ta zauna domin jiri take ji, Imran yayi shiru shima ya zauna yayi tagumi, sautin kukan Anty ya karu fahad ma kukan yake.
"kuyi hakuri kowa da ƙaddaran da Allah ya ƙaddara mishi, zan baku shawara ku rinƙa bata magani akan lokaci sannan ku siya mata wheelchair ta yadda zataji sauƙin rayuwa babu tafiya"
hawaye ameesha ta share tace "babu wani taimako da zamu samu ta fara tafiya?"
yace "gaskiya babu ko ina zakuje ta riga ta kamu ba zata iya tafiya ba"
shiru sukayi, zai tafi ameesha ta ciro kuɗi a aljihu ta bashi, yace "a,a ki barshi Allah ya bata lafiya"
tafiya yayi, Imran ya ɗaura kanshi akan cikin umma yayi shiru, duk wajen babu wanda ya kara magana.
Abdool kula ya fara bata da ciwon ya hana ammi yi mata komai shi yake mata, duk abinda yasan zai sata farin ciki yinshi yake, tana samun farin ciki saide kullum idan sun kwanta da dare sai taji yana kuka ƙasa ƙasa, wannan kukan da yake ne yake taɓa mata zuciya, saide ta rungumeshi ta rinƙa taping bayanshi da haka yake samun sauki ya rage kukan har yayi bacci.
Ameesha ce take kula da umma su Imran suna zuwa school ta hanasu zaman gida, ta kwashe duk kayansu umma dana Imran sun mayar gidansu, makulli tasa ta kulle gidan sannan ta bawa Imran makullin tace "kun dawo gidanmu da zama daga yau,
acan zamufi samun sauƙin kula da umma tunda muna da yawa gani ga Anty ga fahad kuma gaka, idan kun tafi school na tafi wajen aiki Anty zata kula da ita"
ya karɓi makullin yace "to"
tafiya sukeyi akan mashin nata har suka isa gidan, umma tana zaune akan wheelchair da ameesha ta siya mata, tana ganinsu tayi murmushi ameesha ta karaso ta zauna akan cinyarta ta rungumeta, tace "umma kin fara samun sauki gashi har kin daina ramewa"
cikin maganan ta da baya fita tace "eh ameesha kulawanku ne yasa hakan na gode sosai"
murmushi tayi bata kara magana ba, Anty ta kawo musu abinci tace "to lokacin cin abinci yayi sai a sauko ko?"
sauka tayi daga ƙafan umma ta ɗau abincin ta fara bata, saida ta koshi ta bata magani, tare dasu Imran suka zauna suna cin abincin, umma tayi tagumi tana kallonsu, har yau basu dawo normal ba dauriya kawai suke yi, haɗa ido sukayi da ameesha tayi mata murmushi kawai,
washe gari akan mashin nata ta kaisu Imran school kafin ta wuce wajen aikinta, saide ta tarar da mummunan labari me company ɗinsu ya rasu, tun a ranan aka rufe company, jikinta a mace ta koma gida, koda ta shiga umma tana zaune a waje ɗaya kamar kullum, zama tayi a kasa kusa da ita ta ɗaura kanta a cinyar umma, hawaye masu zafi ya zubo mata, bata damu data share ba, umma ce ta ɗaga hanunta mai aiki ta fara share mata hawayen tana mata alaman kada tayi kuka, a hankali tace "umma komai yana daɗa lalacewa, numbern man baya shiga naso na kira miki shi kullum wayanshi a kashe, naje company ɗinsu ance basa zuwa daga shi har manal ɗin, duk inda nasan muna zuwa tare zan ganshi naje dan na sanar mishi rashin lafiyanki ban ganshi ba, sannan yau me company ɗinmu ya mutu an rufe company, ɗan kuɗin da nake samu ina siya miki magani muna cin abinci a ciki aina zan samu?"
kuka take yi sosai, umma sai shafa kanta take, da sauri ta ɗago kai ta share hawayen tace "ba komai ni ameesha zan kara neman wani aikin, ai niba raguwa bace ko umma?"
a hankali ta gyaɗa mata kai, murmushi tayi tana gyara fuskanta tace "nayi alkawarin zan kula dake har karshen rayuwata zan rinƙa siya miki magani har Allah yasa ki samu sauki, sannan ki kwantar da hankali man zai zo watarana kinji?"
jijjiga kai tayi, Anty tace "kin sata a gaba kuna kuka kin manta batada lafiya ne?"
tace "mun daina ai yanzu dariya zan sata"
dariya umma tayi itama ameesha tayi dariya, da dare bayan kowa ya kwanta tayi shiru tana zaune tana kallon umma suna bacci, sam bacci yaki ɗaukant, a hankali ta sauka daga gadon ta buɗe drower cikin sanɗa ta ciro hotonansu da man, fita tayi daga ɗakin ta koma falo ta zauna, kallon hoton take tana hawaye tace "rana ɗaya ka tafi ka barmu baka kara juyowa ba, na kira wayarka a kashe inaso na faɗa maka umma batada lafiya sosai"
Imran dake tsaye a kanta yayi gyaran murya da sauri ta ɓoye hoton tace "Imran bakayi bacci bane?"
saida ya zauna a gefenta yace "banyi bacci ba, taya zanyi bacci yayata idonta biyu tana tunanin mutumin daya tafi ya barmu?"
tace "bafa tunaninshi nake ba kawai de ina kallon hoto ne"
yace "tunanin mutum yake sawa a kalli hotonshi, nasan kinyi kewan babban abokinki da wuya ki manta shi, amma ki sani shifa bai damu ba, yana can yana tareda matarshi hala ma yanzu suna can suna romancing juna, ke kuma kinzo kina tunani, idan har munason ganin ya Abdool saide muje gidansu manal, sabida an tabbatarmin suna can da zama, saide ni bana bukatan ganinshi idan ke zakije bismilla"
da sauri tace "a'a babu inda zanje, tunda naji inda yake hankalina ya kwanta amma ba zanje ba Imran"
hanu ya mika mata yace "alkawari"
sarke yatsanta tayi cikin nashi tace "alkawari"
karɓan hoton yayi yace "good night jeki kwanta"
a hankali ta tashi ta tafi ɗaki, ba karamin daɗi taji ba da taji yana gidansu manal koba komai tasan inda yake, Imran tunda jimawa yasan Abdool yana gidansu manal yaki faɗa mata ne kawai dan yaga babu amfanin Abdool ɗin yanzu a wajenta, saide yaga bata bacci da alama tunanin inda yake takeyi, hakan yasa ya faɗa mata domin ta fara bacci kada ta kamu da depression, kwanciya yayi a falon yayi bacci.
yau tsawon wata biyar kenan babu man suma suna rayuwa basu damu da gashinshi ba, ameesha ce sanye da dogon riga jallabiya na mata, tayi kyau sosai tana shirya musu abincin rana tace "duk ku fito an gama"
shiga ciki tayi ta janyo umma daga kan wheelchair tana turata tace "umma yau nayi abinci me daɗi"
murmushin karfin hali umma takeyi amma yau tana jin jikinta sosai, su Imran sun fito suka fara cin abincin da Anty sai hira suke cikin nishaɗi, akan cinyan umma ta zauna kamar yadda ta saba ta fara jansu akan wheelchair tana turasu tare tana dariya a koda yaushe idan tayi hakan tana jin farin ciki mara misali, saida ta gama juyasu Imran yace "abincinku fa yana sanyi"
sauka tayi ta kawota wajen abincin ta zuba mata ta fara bata, a hankali Imran yayi mata raɗa a kunne "masu siyan gidan sun turo kuɗin na basu takaddun"
cikin ɓoyewa su umma maganan ta jijjiga kai sannan taci gaba da bawa umma abinci, saida ta gama tace "Imran zo muje mu siyo pure water"
da sauri ya tashi yace "to"
fita sukayi tace "kuɗin sun cika?"
yace "eh"
idonta cike da hawaye tace "yanzu Imran saida muka saida gidanku? nace maka mu saida namu amma kaki yadda idan umma taji ba zataji daɗi ba"
yace "Ameesha ya zama dole ne mu saida gidan zamu siya mata magani zamu kaita asibiti domin ina ganin yadda take runtse ido a koda yaushe tana jin ciwo, faɗa mana ne kawai batayi dan tadan babu kuɗi, bakya aiki, gashi abinci ya kare, kuɗin school fees namu zamu biya sabida har sun fara kori, ya zamuyi?"
share hawaye tayi tace muje mu siyo pure water mu dawo kada hankalinta ya kai wani abin, tare sukaje suna tafiya tana sharan hawaye yana bata hakuri har sukaje suka siyo, dawowa sukayi manal rike da ledan ruwan Imran kuma ya rike ledan kayan miya da suka siya, gani sukayi Anty tana kuka tana girgiza umma amma bata motsi, wurgi ameesha tayi da ledan shima Imran ya wurgar, tare sukaje suna girgizata "umma umma ki tashi"
a hankali ta buɗe ido ta kallesu cikin ciwo, da kyar tace "Abdulrahman"
ameesha cikin tashin hankali tace "umma" buɗe idonta ta kara yi cikin ciwo ta rike hanun Ameesha tace "Abdool kiramin shi"
da sauri tace "zanje na kira miki shi ki buɗe ido kinji? na miki alkwari zanje na kira miki shi"
a kiɗime tace "Imran kira napep"
da gudu ya fita zuwa kiran napep tare suka ɗagata suka shigar da ita napep suka shiga ameesha babu takalmi shima Imran haka, asibitin world care suka kaita, a hanya tana magana a hankali, Ameesha saida ta kai kunnenta wajen bakinta taji tace "Ameesha Abdool"
tace "zanje na nemo miki shi yau na miki alkwari umma"
suna shiga asibitin bakinta ya rufe bata kara magana ba sai kallon ameesha take, Imran yana damƙe da hanunta, emergency aka karɓeta Imran da ameesha hanunsu a cikin nata a hankali suka zame hanun lokacin da zasu shiga da ita, Imran ya zauna yayi shiru, ameesha tace "zanje na kira man, ka kula da kowa anan kaji?"
yace "ko zamuje tare?"
girgiza kai tayi tace "ka zauna ka kula dasu zanje kuma insha Allah zamu zo tare jikin umma yafi na kullum tsanani Imran ya zama dole naje na kira abdool"
Imran cikin yadda da magananta shima ya cire rai yau da umma yace "Allah ya tsareki ki dawo da wuri idan kina wuri kowa yafi samun karfin gwiwa"
jijjiga kai tayi
da wani irin gudu ta fita a asibitin mashin ta shiga ta faɗa mishi inda zai kaita.
manal tana zaune akan sofa tayi shiru ta ɗaga kanta sama tana kallon p.o.p na saman ɗakin, wando ne me taushi a jikinta da riga baƙi me guntu, tayi parking gashinta ta saki a bayanta, sosai tayi kyau ta kara zama fara sal, Abdool ne ya fito daga ɗaki yayi kyau shima cikin armless da gajeren wando baƙi, kallonta yayi yaga tayi shiru gaba ɗaya tana zama shiru a rayuwarta, rashin magana da take yi yake sata yawan ciwo a zuciya, idan tayi magana dashi kaɗan sai taga kamar tayi hira sosai, a hankali ya kwanta akan sofan da take ya ɗaura kanshi a cinyarta yayi shiru shima yana kallon saman ɗakin, kallonshi tayi tace "ka fito?"
jijjiga kai yayi yace "kina nan bakici komai ba kuma kin san bake kaɗai bace"
zatayi magana ya tashi yaje fridge ya ɗauko fruits yazo ya zauna kusa da ita ya fara bata, ture hanunshi tayi tace "na koshi"
yace "no banso baby na ta zauna da yunwa a cikinki"
dariya tayi tace "wai a kaina aka fara ciki ne honey?"
ya kara kaiwa bakinta yace "kici sabida ki haifomin kyakkyawan baby me kama dake, itama ta zama kamar balarabiya"
ammi ce ta shigo sanye da leshi fari tayi kyau, Ameesha tace "ammi wai nikam da gaske ina kama da larabawa?"
dum dum kirjin ammi yake duka, da sauri tace "A,a bakya kama dasu dani kike kama"
murmushi tayi tace "ammi ko lokacin da nake karama ance ina kama da larabawa a time ɗin saina fara tunanin waye balarabe a cikin ke da kuma dady, kuma akwai ranan da naje kai zane wani unguwa da baƙina suka sauka, motata tsaya na fito domin duba meya samu motan kin san yaran wai me suka cemin?"
girgiza kai tayi tana kura mata ido a tsorace, tace "wai balarabiyan mahaukaciya"
tashi ammi tayi a firgice tace "ke kuma me kika ce musu?"
ganin yanayin ammin tace "relax mana ammi ban kulasu ba kawai na tafi"
ajiyan zuciya ta sauke tace "kimin alkawari ba zaki kara zuwa wancan unguwan ba"
tace "nayi alkwari"
tafiya zatayi manal tace "ammi saura wata nawa kenan na haihu?"
Abdool yace "yawwa dama inaso nima na sani amma kunyan tambaya nake"
tsaki taja a ranta wato duk basuda kunya shi wai a haka kunya yake, tace "saura wata shida"
tafiya tayi, Abdool ya rungumeta yace "me kama dake nakeso ki haifamin"
a ranshi yace "idan bakya raye ba za'a manta dake ba"
tace "ni dai nafi son na haifi me kama da kai"
shafa fuskanta yayi a hankali ta lumshe ido, matsowa yayi kusa da ita sosai yana jiyo numfashinta, bakinshi ya ɗaura akan nata, kafin yayi komai yaji ta fara kissing tongue nashi tareda haɗawa da pinkish lips nashi, hanunta a kanshi tana wasa da gashinshi dake a kwance, hanunta yaji ta fara ɓalle bottle na riganshi tana shafa suman dake kwance a kirjinshi, kwantar dashi tayi akan sofan ta bishi har yanzu bakinsu a haɗe, rufe ido yayi ya zame a hankali ganin tana neman ta fitar dashi hayyacinshi, yace "no ammi zata iya fitowa"
girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace "ba kai ka fara ba?"
zaiyi magana ta rufe bakinshi da nata, zamewa yake yana dariya, wayarta yayi kara alaman message, ɗauka tayi tana rungume dashi baya ganinta ta buɗe tana karanta sakon, driver ne yayi mata text "yarinyar da kika nunamin hotonta gata nan tazo amma na hanata shiga ciki tana nan wajen compound"
gabanta ya faɗi ko da me ameesha tazo? tsaki taja a ranta tace koma menene abinda na sani shine babu wanda ya isa ya rabani da Abdool, da sauri tace "uhm ni kam yau exercise zanyi tunda kaki muyi"
yace "good girl exercise nada kyau ga me ciki, jeki zan biyoki bari nasa jallabiya"
tashi tayi tana tura baki ta fita, haɗe rai tayi ganin ameesha tana turesu tana cewa "ku barni man nakeson gani"
cikin takun isa ta karasa inda take tace "duk kuje ku barmu anan"
tafiya sukayi ta rike hanun Ameesha ta jata kusa da wani babban dutse dake cikin gidan tsayawa tayi tace "meya kawoki?"
tace "nazo wajen man ne"
murmushi tayi tace "man yau kaɗai yake dashi gobe ze tafi paris kuma zai jima acan har sai na haihu zai dawo me zakiyi mishi?"
tace "ummanshi ce babu lafiya jikinta yayi tsanani shine nake so na faɗa mishi"
tace "okay zan faɗa mishi jeki"
girgiza kai tayi tace "nafi son na faɗa mishi da kaina ki mishi magana please"
cikin kallonta na tsananin ɓacin rai tace "nace miki zan faɗa mishi fita"
girgiza kai tayi tace "ba zan fita ba ko kasheni zakuyi saina sanar mishi domin alkawari na yiwa umma"
hanunta ta rike da karfi tana janta tace "fita ki bar gidannan"
tirjewa ameesha take, Abdool ne ya buɗe kofan ya canja kaya zuwa jallabiya fari me taushi, kallonsu yayi da mamakin ganin ameesha a wannan lokacin, ganin haka manal tace "ki sakemin hanuna ameesha inada ciki ki sakeni kada naji ciwo"
cikin tsananin mamakin sharrin da take shirin yi mata tace "kece kika rikemin hanu ai kece zaki sakeni"
da karfi tace "Abdool kace ta sakeni"
Abdool zaiyi magana kawai ta saki hanun Ameesha tayi juyi ameesha kuma tana shirin riketa kawai ta zube akan babban dutsen dake wajen, zaro ido man yayi itama ameesha ta zaro ido tareda ɗaura hanu a baki, manal cikin azaba taji jini ya fara zuba daga jikinta a take jinin ya fara sauka har zuwa kasa, da kyar ta buɗe baki tace "man cikina"
cikin gudun da bai taɓa yiba yazo ya ɗagata yana cewa "manal?"
ameesha cikin tsoro tasa hanu zata taɓata ya tureta saida ta kusan faɗuwa, jijiyoyin kanshi suka tashi, yana zufa ya nunata da yatsa yace "stay away from my wife"
tace "man ka fahimta banyi mata komai ba"
yace "ina gani kika tureta kice baki mata komai ba? ameesha yaushe kika zama muguwa haka? ko dama kin ɓoye muguntanki ne lokacin da muke tare?"
zatayi magana yace "stay away!!!"
shiru tayi, yana rike da manal jini yana zuba ya kira waya yace "kizo gida yanzu yanzu"
lokacin da zasu shiga falon manal ta buɗe ido tana yiwa Ameesha kallo sannan tayi murmushi ta kashe mata ido ɗaya, shiga ciki yayi da ita ammi jikinta yana rawa tace "ina jinku na kasa fita abdoo"
kwantar da ita yayi ya fara safa da marwa a ɗakin, dr A'isha ce tazo gidan ameesha tana tsaye a inda suka barta har ta shiga, duba manal ta fara, jikinta a mace tace "tayi miscarriage"
Abdool cikin tashin hankali yace "dan Allah ki kara dubata inason cikin sosai dan Allah, kunsan inason cikin"
kuka ya fashe dashi, manal tasan yadda yake son cikin sabida Abdool yana matukar son yara, cikin kuka tace "ɗanaaaaa wayyo ammi ɗana"
kuka take yi sosai, Dr A'isha tace "saide hakuri dan cikin ya gama sauka tayi ɓari amma garin ya haka ta faru? accident tayi ne?"
manal kuka take yi Allah ya sani tana son cikinta amma a halin yanzu babu abinda take so kamar man ba zata yadda kowa ya shiga tsakaninsu ba, ya girgiza kai kawai yana kallon kofa inda ameesha take tsaye yana aika mata wani irin mugun kallo me cike da tsana, zatayi magana yace "shikenan kin zubar da cikin kin samu kwanciyan hankali? shikenan?"
girgiza kai take zatayi magana yace "fita kibar gidannan ameesha, ban taɓa zaton akwai mugunta koda kwayan zarra a zuciyarki ba, yau kawai sai naji na tsaneki, ki fita a rayuwata ki barni mana, ki barni dan Allah wallahi na tsanaki yanzu"
hawaye ta share ganin yadda yake magana cike da ɓacin rai a tsawace kamar ba man ba
tace "to shikenan tunda ka tsaneni amma nima inaso ka sani a yau naji na tsaneka kuma zan fita a rayuwarka"
hanunta ya rike da karfi ya fara janta yace "fita banson ganinki"
ammi tace "Abdool ka saketa"
cikin zafin da takeji tace "ka sakeni man"
janta kawai yake ammi tana binsu har bakin kofa taga ya buɗe kofan yayi wurgi da ita, faɗuwa tayi kasa cikin azaban daya ziyarci hanunta tace "wayyo hanuna"
ɗauke kai yayi ganin tana kallon hanun har ya fara jini tana kuka
yace "ko me kama dake banason gani, idan kika kara shiga rayuwata zan miki abinda harki mutu ba zaki manta ba"
da alama man yaji ciwon zubewan cikinnan, yana matukar son cikin, tashi tayi da kyar tana ciza baki, ta share hawaye a hankali ta tako zuwa gabanshi ta tsaya kusa dashi tana kallon cikin idonshi, zuciyanta a bushe ta fara magaan cikin rashin tsoro tace "In dai sunana Ameesha Ibrahim ƴar halak aka haifeni ba zina akayi aka samu ciki na ba, zan fita a harkanka Abdulrahman haruna lamiɗo, amma kafinnan inaso ka sani ba nice na zubar da cikin matarka ba, banzo gidannan sabida na ganka ko naga matarka ba, sannan ban san da wannan cikin da kuke magana akai ba, idan kuma ka ɗauka cewar nice na zubar to kayi duk abinda kaga zaka iya ka idan kaso ka kaini inda ba'a dawowa, sannan zan isar maka da sakon daya sa ameesha tasa kafarta ta shigo wannan gidan, ummanka ina nufin wacce ta ɗauki cikinka na tsawon wata tara ta haifeka ta raineka har ka zama mutum batada lafiya, idan kaga dama kazo idan kaga dama karka zo, ni na isa na kula da ita sabida kafi kowa sanin wacece ameesha banida raunin zuciya ko da kai ko babu kai zan iya komai"
juyawa tayi zata tafi a hankali ta juyo ta share hawayen daya wanke mata fuska tace "butulu"
tafiya tayi shima ya shiga gidan tareda rufe kofan, bata kara juyowa ba, zama yayi a jikin kofan ya haɗa kai da gwiwa a hankali ya fara raira kuka me sauti, baba megadi dake rike da sanda yazo wajenshi yace "Abdool ba kuka zakayi ba duk abinda ya faru da kai a rayuwa addu'a zakayi kaji?"
a hankali yace "to baba ya zanyi?"
a hankali baba yace "kayi hakuri duk abinda kaga ya faru to an rubuta zai faru babu wani wanda ya isa ya goge domin takaddan ba a hanun ɗan Adam yake ba yana hanun ubangijin mu, saide karfin addu'a yana iya canja ƙaddara"
cikin kuka ya tashi jikinshi a sanyaye yace "to baba na gode" shiga ciki yayi, manal ta rike ammi tana kuka kamar ranta zai fita, kukan azaban ciwon cikin dake addabanta a halin yanzu take da kuma soyayyan da take yiwa cikin, cikin azaba tace "man shikenan na rabu da cikina?"
zama yayi kusa da inda take kwance a kasa ya ɗaura kanshi a cikinta yayi shiru yana hawaye, ammi tace "kuyi hakuri duk abinda ya faru a ƙaddaran ɗan adam an rubuta zai faru ne babu wanda ya isa ya hana, amma duk wanda yayi kokarin canja ƙaddaran wasu to Allah ba zai barshi ba kuma ba zaiyi karshe me kyau ba, ba zai taɓa samun farin ciki ba a rayuwa ko kuma Allah ya haɗashi da ciwon da babu magani"
ɗip hawayen manal suka tsaya jin abinda ammi ta faɗa, a hankali ta ɗago dara daran idanunta da eyelashes ɗin suka jiƙe da hawaye, itama ammi kallonta tayi, da sauri ta ɗauke kai, man ya kalleta yaga jikinta yana rawa, idonta ya gama rikiɗewa yayi jajur a hankali ya ɗagata ya kaita ɗakinta, akan gado ya kwantar da ita, tayi shiru ta rufe ido, tashi yayi zai tafi ta rike hanunshi cikin wani irin raunataccen murya haɗe da ciwon data ji tace "ina zakaje ka barni Abdool?"
so yake yace wajen umma, sai yaji tace "zan mutu Abdool ni nasan ba zan jima a duniya ba, duk wanda na tarewa jin daɗi ko kuma na kuntata mishi nasan zan mutu na barshi, haka Allah ya rubuta abdool haka Allah ya yini, abdool ni nasan me nakeji a jikina, ba zan jima a duniya ba"
dawowa yayi ya rungumeta kawai zuciyanshi yana kara karaya
itama manal ita kaɗai tasan ciwon da takeji a jikinta da zuciyarta ko kaɗan ba pretending take da ciwon da take dashi ba
ciwonta na gaskiya ne babu karya a cikinta, wasu zafafan hawaye suna wanke kyakkyawan fuskanta tana kallon bayan abdool wanda shima hawaye masu raɗaɗi suke sauka a idonshi
a cikin ranta tace "Abdool kayi hakuri abdool ka yafeni nayi sanadin cikin dake jikina badan komai ba sai dan banso a rabani da kai, naraunata kaina, na tuba Allah, na tuba bazan iya rabuwa da kai ba zan iya yin komai dan na zauna da kai, manal meyasa kikazo duniya kika zama wa mutane masifa? kina yin abu kamar ba ƴar mutane ba, kamar aljani ne yayi cikinki, a hankali yake shafa bayanta jin sautin kukanta yana karuwa, sun jima a haka kafin taji ya saketa ya kwanta a gefe, rufe ido yayi bacci ya ɗaukeshi sabida zazzaɓi ne ya rufeshi, murmushi tayi tana kallon kyakkyawan fuskanshi, a hankali ta janyo blanket ta rufashi dashi, kiss tayi mishi a goshi sannan ta sauka akan gadon, gaban mirror taje ta ɗauko stool ta zauna tana kallon kanta a madubi, wasu zafafan hawaye suna zubo mata suna wanke kyakkyawan fuskanta, cikin rawan murya ta motsa ɗan karamin bakinta tace "manal anya ke mutum ce?"
kara kallon kanta tayi ta kasa koda kyafta ido ta cikin madubin tace "manal meyasa?"
wani irin mari ta wanke fuskanta dashi, kallon shatin hanunta daya fito akan fuskanta take fuskan ya koma jajur, kara marin kanta tayi daga nan ta fara bawa kanta kyawawan maruka tana kuka, saida taga fuskanta ya kumbura yayi jajur sannan ta kalli bakinta da gefen yake jini tace "ba zan iya ranuwa da Abdool ba, wallahi ba zan iya ba, zan iya yin komai akanshi kuma a shirye nake nayi komai akanshi koda kuwa kowa zai mutu koda nice zan mutu"
a hankali ta mike daga kan stool ɗin ta koma kan gadon ta kwanta ta rungumeshi ta rufe ido.
*You can start making your payment, our free pages is about to finish, duhu da haske complete is 400 via 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, send your evidence of payment via 08144818849 may Allah bless you and ease your payment Ameen*
_Jiddah Ce...._
managarciya