Ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Sokoto ya rasu da shekara 62
Ɗan Majalisar Tarayyar mai wakiltar Isa da Sabon Birni daga jihar Sokoto a Najeriya , Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu.
Honarabul Danbuga - wanda ɗan jam'iyyar APC ne - ya rasu cikin daren jiya sakamakon gajeruwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekara 62 a duniya.
Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni ta kudu, Aminu Almustapha Boza ne ya tabbatarwa da BBC rasuwar marigayin.
"Za a tafi da shi Sokoto domin yi masa jana'iza kamar yadda addinin muslinci ya tanada,"in ji Honarabul Boza
Margayin ya rike shugaban Karamar hukumar Sabon Birni kafin ya zama Dan majalisa, yana da tasiri sosai a Siyasar Karamar hukumar Sabon Birni da jiha Baki daya.
managarciya