Akalla shaguna 50 sun kone a kasuwar Kara ta Sakkwato
An samu tashin gobara a kasuwar Kara ta jihar Sakkwato in da shaguna kusan 50 suka kone bayan tashin wutar a cikin daren Jumu’a, dukiya mai yawa ce ta salwanta, sai dai ba a samu hasarar rayuwa ba.
Gefen masu nika(markade) ne wutar ta cinye gaba daya a kasuwar kan haka shugaban kungiyar masu sana’ar a jiha Yakubu Bello ya zanta da wakilinmu bayan samun nasara kashe wutar a ranar Assabar.
Shugaba Yakubu ya ce abu ne da Allah ya kawo domin an tashi aiki kowa na gidansa aka kira waya wuta ta kama a Kasuwa, har zuwa yanzu ba mu san sanadin gobarar ba domin har aka kashe wutar babu wutar lantarki, kuma kowa ya kashe injiminsa kafin rufe shago.
"Mun yi hasara sosai akalla shago 45 zuwa 50 suka kone, injinun nika manya kusan 100 ne gobarar ta lakume, gaba daya injin 132 aka yi hasara.
"Muna kira ga gwamnati ta tallafa mana, masu wannan sana'ar a cikin kasuwar sun kai mutane 500 kuma matasa sun fi yawa," a cewar shugaban kungiya.
Aminu Mainika Gandu yana cikin wadan da shagonsa ya kone ya ce sun yi hasara sosai wutar ta fara ne a 11:30 na dare da aka kira shi ya zo wuta ta kama a kasuwar ko da ya zo misalin 12 na dare komai ya kone a gefen nasu a kasuwar ta Kara.
"Ko sifana ta injin ba wanda ya fita da ita, kwarai muke godiya da ma'aikatan kashe gobara sun yi kokari saosai wurin dakile bazuwar wutar zuwa wasu sassan kasuwar, sun yi tsaye har wutar ta mutu."
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya jajantawa mutanen da suka samu hasara a wutar da ta faru ya roki Allah ya mayar musu da alheri.
Gwamnatin Sakkwato ta yi alkawalin taiamakawa 'yan kasuwar da suka samu wannan ibtila'i.
Mataimakin Gwamnan jiha Alhaji Idris Muhammad Gobir ya bayar da sanarwar Gwamnati za ta kafa kwamitin da duba hasara da sanadin gobarar da aka yi.
Mataimakin gwamnan a lokacin da ya ziyarci kasuwar a Lahadi ya ce kwamitin da za a samar zai duba hanyoyin da za a bi domin kaucewa faruwar gobarar a gaba.
managarciya