Farinciki ya mamaye mutanen da ke kan iyakokin kasar Nijar da Nijeriya bayan da gwamnatin Nijar ta bude bodar ta da Nijeriya sati daya bayan da kasar Nijeriya ta bude iyakokinta tare da umarta jami'an tsaron kan iyakoki su dawo aiki a wurarensu.
A jumu'ar data gabata da kasar Nijar ta bude bodar mutanen Kwanni a Nijar da Illela a Nijeriya sun yi murna ganin tirka tirka da ke tsakanin ECOWAS da ta sa aka rufe bodar a watan Agusta na 2023 bayan da sojoji suka hambarar da mulkin dimukuradiyya ta kawo karshe.
Jihohin Nijar da lamarin rufe bodar ya shafa sun hada da Diffa,Maradi,Tahoua,Dosso da Zinder (Maradi) kenan.
Mazauni a garin Kwanni Isufu Zangwai ya ce ba lokacin rabuwa ba ne a yanzu domin dukkan kasashen na bukatar juna a wannan yanayi na matsin tattalin arziki.
Zangwai ya ce mutanen Nijar da Nijeriya abu guda ne kasuwanci da addini da aure da sauransu dukkansu babu bambanci, ga auratayya tsakaninsu.
Malam Nuhu Sama'ila a Kwanni yake zaune a kasar Nijar ya ce an bude boda ne a ranar Jumu'a da karfe 12 na dare, ya yi fatar hakan zai sa bunkasar tattalin arzikinsu, fahimtar juna dake tsakanin kasashen ta dawo.
Ya ce bude bodar zai taimakawa kasashen a harkokin kasuwanci da cigaban da ake yi.
Malam Kabiru Auwalu mazauni a garin Illela ya ce bude bodar da aka yi ya sa mun farinciki sai dai muna bukatar a bude mana boda a rika shige da fice da kayan masarufi kamar baya, wannan budewar ta ECOWAS ce muna son a yi ta Nijeriya don haka ne kawai zai samar saukin farashin kayan masarufi a yankinmu.
Ya ce gwamnatin Nijeriya yakamata ta bude bodar kasa bayan wannan ta ECOWAS domin Nijeriya ba ta iya wadatar da kanta da abinci da sauran kayan masarufi.
Bello Umar Illela ya ce gwargwadon hali lamurra suna dawowa daidai a harkokin hulda a tsakanin iyakokin kasashen biyu daman matsalar tsaro ce ke gurgunta abubuwa a gefen domin rufe boda a hukumance ne aka yi ta ba a shiga ko fita amma 'yan kasuwa na harkokin a boyayyar hanya ta daji ba in da hukuma ta tanadar ba.
" Biyar doka ita ce tafi amma saboda wasu bara gurbi da ke takura mutane sai su bi daji, duk da har yanzu ba a aminta a rika shigo da shinkafa da sauran abubuwa ba yakamata a yi yanda talaka zai samu sauki, matsalar tsaro ta hana noma in an gyara faduwar darajar naira su ne za su kawo bunkasa a harkokin kasuwancin boda".
Ya ce a yanzu kasar Nijar sun yi odar abincinsu kuma sun kayyade farashi a kasar shinkafar su tafi ta Nijeriya sauki.
Kabiru Haruna ya ce da gwamnati za ta gyara harkar tsaro a kuma dawo da darajar naira mu dake kan iyaka za mu yi farinciki sosai don bunkasar kasuwancinmu ya dawo, bayan bude boda abin da kawai muke nema a gwamnati ta duba wasan nan abubuwan biyu dana gaya maka a farko.
Shugaban karamar hukumar mulkin Illela a jihar Sakkwato Sahabi Isah Wakili ya bayyana murnarsa ga bude bodar da aka yi domin hakan zai taimakawa al'ummarsa.
Sahabi Wakili ya ce tsakanin Illela da Kwanni abu daya ne zuri'a ce guda za ka samu Dan sarautar Illela mahaifiyarsa daga Kwanni aka dauko ta, kasuwanci iri daya ake yi ana ban gishiri na baka Manda.
"Bude bodar zai taimaka sosai in aka dunke barakar da ke tsakanin ECOWAS da Nijar, duk bude bodar ana bukatarta duk da ba wadda za a bari a rika shigo da kayan masarufi ba ce yanda ake yi kafin gwamnatin baya."
Shugaban ya ce in ka cire wadanda ke amfana a rufe bodar 'yan kasuwa na son harkar kasuwanci ta dawo a tsakanin kasashen biyu.