Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma Ya Rasu

Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma Ya Rasu
Abba Sayyadi Ruma
 

Allah ya yi wa tsohon ministan noma, Abba Sayyadi Ruma rasuwa a yau Laraba, a  Landan, Jaridar Katsina Post ta samu labarin rasuwar Alhaji Abba Sayyadi Ruma a yau bayan gajeruwar rashin lafiya.

 

Majiyar mu ta shaida mana cewa Alhaji Abba Sayyadi ya rasu a wata asibiti da ke a birnin Landan bayan ya ziyarci asibitin domin a duba lafiyarshi.

 
Abba Sayyadi Ruma wanda aka haifa a March 13, 1962, wanda ya riƙe muƙamin sakataren Gwamnatin jihar Katsina daga bisani ya zama Ministan Noma da kula da albarkatun ruwan Nigeria a lokacin Marigayi Ummaru Musa Yar'adua.
 
Marigayin shi ne wanda ya assasa Makarantar Koyon kiyon lafiya da ke a ƙaramar hukumar Batsari da ke Katsina, mai suna Cherish College of Health Sciences.
 
Daga Zaharaddeen Gandu