Yadda ƴanbindiga suka yi garkuwa da kusan mutum hamsin a Zamfara
A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mazauna garuruwan Banga da Gidan Giji da sauran su da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, na ci gaba da barin garuruwan nasu sakamakon jerin hare-haren da ƴanbindiga ke ci gaba da kai musu.
BBC Hausa ta rawaito cewa a farkon makon nan ƴanfashin dajin sun kashe aƙalla mutum biyu tare da yin garkuwa da ƙarin wasu hamsin, waɗanda suka haɗa da maza da mata, inda suka buƙaci sai an biya su kuɗin fansa kafin su sako su.
Mazauna garuruwan Banga da Gidan Giji dai sun ce maharan da suka kai musu hari sun mamaye garinsu, tare da karin wasu garuruwa da dama wanda hakan ya tilastawa wasu tserewa saboda kaucewa harin yan bindigar.
Sun ce galibin ƴanbindigar na haye kan Babura dauke da muggan makamai, inda duk sanda suka zo, sai sun halaka mutane, tare da tafiya da mai tsautsayi.
"Sun addabe mun a wannna yankunan namu, akwai harin da suka kawo mana nan garin Banga, sun zo sun tarar da yara a ƙofar gida, sun ɗauke mutum hamsin sannan suka halaka mana mutum biyu. Jami'an mu na tsaro na Vigilantee sun yi iyakar ƙoƙarinsu, don badan ɗauki ba dadin da suka yi da su ba, da mutanen da ƴanbindiga za su dauka da sun fi haka, in ji wani mazaunan yankin.
Haka kuma ya ce kawo yanzu ƴanbindigar sun nemi da su basu naira miliyan ɗari a matsayin kudin fansar ƴanuwansu da suka yi garkuwa da su.
Sai dai har yanzu gwamantin jihar ta Zamfara ba ta kai ga cewa komai ba kan lamarin, duk kuwa da ƙoƙarin da BBC ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Suleiman Bala amma hakan bai samu, duk da kiran waya da gajeren sakon da aka aika masa.
Ko a baya bayan nan a wani rahoton da kamfanin Beacon Security Intelligence mai nazari kan matsalar tsaro a Najeriya da yankin sahel ya fitar kan rashin tsaro a watan Maris da kuma watanni uku na shekarar 2025, ya nuna cewar a watan nan na Maris, jihar Zamfara ce a matsayi na biyu na jihohin da aka fi halaka mutane sakamakon ayyukan yanbindigar, inda aka kashe mutum 179 a watan Maris, ƙasa da mutum 302 da aka kashe a jihar cikin watan Fabarairu.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohi a Najeirya da ke fama da mastalar tsaro, baya ga maƙotanta Kastina, da Kaduna, da Sokoto, da Kebbi.
Sai dai a lokuta da dama duk da cewar hukumomin tsaron Najeiryar na cewar suna samun galaba kan yaƙi da ƴanbindigar, da halaka wasu daga cikin manyansu, har yanzu yan bindigar na cigaba da kai hare hare da garkuwa da mutane,a yankunan.
managarciya