Ɗan Majalisar Dokokin Ya Mutu a Wurin Yaƙin Neman Zaɓen APC  a Jos 

Ɗan Majalisar Dokokin Ya Mutu a Wurin Yaƙin Neman Zaɓen APC  a Jos 

Dan majalisar dokokin jihar Legas, Hon Sobur Olayiwola Olawale ya fadi ya mutu a garin Jos na jihar Filato.

Dan majalisar yana da lakabin ‘Omititi.’

Olawale ya kasance a Jos inda ya halarci taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC.

An ce ya rasu ne a hanyarsa ta komawa Legas, amma har yanzu yana Jos, kamar yadda majiya mai tushe ta bayyanawa Yola 24

An haifi marigayi Olawale a shekarar 1964. Ya wakilci mazabar Mushin II a majalisar dokokin jiha.

A ranar Juma’ar da ta gabata, dan majalisar ya ta ya shugaban majalisar, Mudashiru Obasa bikin cika shekaru 50, inda marigayi dan majalisar ya buga wasa  a matsayin mai tsaron gida.

Mutuwar tasa ta jefa majalisar dokokin jihar cikin makoki.

Omititi ya bar mata daya da ‘ya’ya uku.

Har yanzu dai majalisar dokokin jihar Legas ba ta fitar da wata sanarwa kan rasuwarsa ba.