Ribadu ya nemi Naja’atu ta bashi hakuri kuma ta janye kalaman ta a kan sa

Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Malam Nuhu Ribadu, ya nemi Hajiya Naja'atu Muhammad ta ba shi hakuri a bainar jama’a tare da janye kalaman ta a wani bidiyon TikTok da ya ce ya na da mummunar manufa.
Daily Trust ta rawaito cewa a cikin bidiyon TikTok ɗin, Hajiya Naja'atu Muhammad ta zargi Ribadu da yin aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, bayan ya soke shi sau da dama a lokacin da ya ke Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
A cikin wata wasiƙa ta hannun lauyansa, Dr Ahmed Raji, SAN, Ribadu ya bayyana cewa, a fili ko a sirrance, bai taɓa sukar Tinubu ba.
Ya kuma ce illar da ikirarin bidiyon ya haifar ba za a iya misalta ta ba.
A bidiyon dai an jiyo Naja'atu na zargin cewa, Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin Gwamnan da ke kan gaba wajen cin hanci a lokacin da ya ke gwamnan Legas shi kuma Ribadu ke rike da shugabancin EFCC.