Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Fadi Amfanin 'Qur'anic Festival' ga Najeriya

Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Fadi Amfanin 'Qur'anic Festival' ga Najeriya

Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta bayyana dalilan goyon bayanta ga 'Qur'anic festival' da aka shirya yi a Abuja, ranar 22 Fabrairu, 2025. Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bayyana cewa taron ya na matuka muhimmanci. 
A labarin da ya kebanta da jaridar Daily Trust, Sakataren Majalisar NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa bikin ba ya da wata manufa sai dai haɗa kan al’ummar Musulmi domin ci gaban ƙasa. 
Farfesa Oloyede ya ce tunanin bikin ba daga wata ƙungiya guda ɗaya ya fito ba, amma wasu ƙungiyoyin Musulunci sun kawo ra’ayin ne ga majalisar, kuma an rungumi shirin. Sakataren Majalisar ya ce: “Ra’ayin ya fito ne daga ƙungiyoyin Musulunci, sannan Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya ta amince da cewa abu ne mai kyau a yi, wannan ya sa muka zama ɓangare na wannan al’amari wanda bikin ya shafi haɗa kan Musulmi." 
Wani jami’in majalisar NSCIA ya ce 'Qur'anic festival' wani bangare ne na nuna kyakkyawan al’adun al’ummar Musulmi na ƙasar nan game da ilimin Alkur’ani. Har ila yau, bikin na da nufin haɗa Musulmi a ƙarƙashin inuwa ɗaya domin nuna baiwar ilimin Alkur’ani da kuma inganta haɗin kai da zaman lafiya a ƙasar. Jami'in ya kara da cewa: “Mutane akalla 50,000 da suka haɗa da mahaddata, masu rubutu, masu karatun Alkur’ani da masu zanen kaligrafi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da duniya za su halarci bikin,” in ji jami’in.