'Yan Banga Sun Hallaka Mahara 47 a jijar Neja
'Yan Banga Sun Hallaka Mahara a jijar Neja
Rahotanni da muke samu ya nuna cewa, 'yan banga sun hallaka mahara 47 a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Wakilin mu ya nakalto mana cewar maharan da ke kan mashuna sun shigo karamar hukumar ne sakamakon rashin abinci da suke fama da shi sakamakon rufe wasu kasuwannin kauyuka da gwamnatocin jahohin Zamfara da Katsina suka yi, wanda hakan yasa maharan kwararowa makotan jahohi dan samun abinci.
Da yake bayyana ma wakilin mu wani daga cikin 'yan bangar da ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce yanzu matakan da suke dauka duk wani baƙon hauren da ya shigo jihar nan da nufin ta'addanci za su kawar da shi.
"Mun samu rahoton shigowar su, sai muka tare hanyar da zasu ratso, inda muka yi masu kwanton ɓauna, muka bude masu wuta, wasun da dama mun aika su barzahu, wasu kuma mun kama su da hannu, dukkansu akwai alamar galabaita na rashin abinci a tare da su".
Ƙungiyar 'yan bangar bisa jagorancin Kwamanda Nasiru Manta, ta alwashin murkushe maharan da ke shigowa jihar da yin ta'addanci.
Ya cigaba da cewar sabon rundunar mu da gwamnatin jiha ta kafa mun samu horo daga rundunar 'yan sanda ta jiha, yanzu muna aiki kafada da kafada da rundunar tsaron hadin guiwar 'yan sanda da sojoji dan kawar da 'yan ta'adda a jihar nan.
Wasu rahotanni sun ce maharan tamanin da uku sun tafi barzahu, amma a hakikani wadanda aka lissafa gawar mutum arba'in da bakwai ne, sai dai saboda harsasan da suka yiwa da daman su illa jimlar na iya kai tamanin din ko fiye da hakan.
Yankunan kananan hukumomin Munya, Rafi da Shiroro da ke makotaka da jahohin Zamfara, Katsina da Kaduna nan ne kusan mashigar maharan da kan fito wadannan jahohin dan shigowa jihar Neja dan yin ta'addanci ga mutanen karkara.
A cikin satin da ya gabata dai, jihar Neja ta sanya dokar rufe kasuwannin dabbobi masu ci ranakun sati a duk fadin jihar. Dokar ba ta tsaya nan ba, ta shelanta cewar babu wata motar daukar shanu da za ta ratso jihar sai tana da takardar shaidar hakkin inda aka fito da shanun da kuma inda za a kai su.
Haka gwamnatin ta haramta sayar da man fetur a cikin jarkuna, sannan duk wani mai mota ba zai sha man fetur da ya wuce naira dubu goma ba, haka masu yankar katako ko motocin dakon katako gwamnatin ta haramta masu cigaba da aiki a fadin jihar.
Zuwa yanzu dai da aka hana sana'ar kabu-kabu, masu mashunan hawa an kayyade masu lokacin zurga-zurga daga karfe shida na safe zuwa shida na yamma har da masu sana'ar keke-napep da aka amince su cigaba da sana'ar dokar wa'adin hawa mashuna ta shafe su.
Managarciya ta ƙoƙarin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Neja DSP Wasiu Abiodun amma abin ya ci tura.
managarciya