ZA'A  KADDAMAR DA KWAMITIN APC NA JAHOHI DOMIN TARON ƘASA

ZA'A  KADDAMAR DA KWAMITIN APC NA JAHOHI DOMIN TARON ƘASA
 

 

Kwamitin riko na Jam'iyar APC ƙarƙashin Jagorancin Gwamnan Yobe, Honarabul  Mai Mala Buni ya bayyana yau Alhamis 03/02/2022 a matsayin ranar da za'a ƙaddamar da Kwamitin Jam'iyar APC na Jahohin Najeriya wato (State Executive Committees) domin gudanar da taron Ƙasa a cikin watan nan.

 

Wannan Kaddamarwar tana cikin tsare-tsaren gudanar da taron Jam'iyar na Ƙasa, da zai gudana a Ofishin Jam'iyar APC na Ƙasa dake Abuja (Muhammdu Buhari House).

 
A cikin zaman shugabannin rikon ba'a kai matsayar saka Jahohin da ke suke da matsalolin cikin gida ba wannan yayi sanadin rarrabuwar Shugabanci a lokacin da aka  gudanar da zabe a bangare biyu ba cikin watan 10 a shekarar da ta gaba ta.
 
Kaddamawar za ta haifar da  damuwa ga Jahohin irinsu Enugu, Kwara, Ogun, Akwa-Ibom, Delta, Kano, Osun, Oyo, Bauchi dakuma Zamfara,  domin an samu rarrabuwa da ta kai aka yi zabe bangare daban-daban.
 
Kwamitin na Mutun 13, ya samu halartar mutane 10 ne. Sai dai sun bayyana ranar Alhamis a matsayin ranar da zasu sake zama domin duba akan matsalolin Jahohi masu matsalar rarrabuwa.
 
Taron na Kaddamawar dai zai cigaba da gudana kamar yanda aka tsara cikin jadawalin shirin Taron 26/02/2022.
 
ABUBAKAR S. LIMANCHI
(Sarkin yakin Shehi)
On new Media.