Abdullahi Hassan Na Karawa PDP Tagomashi a Jihar Sakkwato

Abdullahi Hassan Na Karawa PDP Tagomashi a Jihar Sakkwato

 

Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa Honarabul Abdullahi Mu'azu Hassan yana karawa jam'iyar PDP tagomashi a jihar Sakkwato ganin yanda yake ta fadi tashin ganin ta samu nasara domin cigaban al'umma ta hanyar samun kyakkyawan jagoranci.

Abdullahi Hassan wanda mutanen jiha ke kira MAI MALALE suna ne da ya bi shi kan aikin alherin da ya shimfida na cigaban karamar kumar Sakkwato ta Arewa a lokacin da yake jagoranci, hakan ya sanya mutane suke da amanna matukar ka ganshi a cikin tafiya abu ne da zai amfani jama'a ta hanyar cigabansu.
PDP a jihar Sakkwato ta samu sa'a sosai da har Abdullahi Hassan ya amince zai yi tafiyar siyasa a cikinta domin samar da cigaba a fannonin rayuwar al'umma. Tun sanda ya karbi wannan tafiyar bai zauna ba, bai huta ba har sai ya ga an samu nasara a dukkan matakan kujerun da PDP ke nema a jihar Sakkwato.

Da yawan mutane matasa a jihar Sakkwato sun aminta za su yi tafiyar PDP a zaben 2023 saboda yakinin da suke da shi Abdullahi Hassan karkashin gwamnatin Malam Sa'idu Umar ba za a bar su baya ba domin a kowane lokaci cigabansu ne ya sanyawa gaba musamman a haujin ilmi da tarbiya da samar da aikin yi.

"Tun da aka kafa PDP ban taba yin ta ba kuma ban yi tsammanin shigarta ba, amma tun sanda Abdullahi Hassan ya jagoranci Sakkwato ta Arewa na ga dimbin alherin da ya samar a fannin kiyon lafiya da gyara muhalli da samar da aikin yi na kudiri aniyar duk tafiyar da yake yi a siyasa ita nake yi, hakan ya sanya ni dan PDP ne cikakke dake fatar samun nasarar Malam Ubandoma" a cewar Muhammad Yusuf Tudun Wada.