2023: Jam'iyyar PDP Mai Hamayya A Najeriya Ta Kama Hanyar Wargajewa A Jihar Kebbi

2023: Jam'iyyar PDP Mai Hamayya A Najeriya Ta Kama Hanyar Wargajewa A Jihar Kebbi

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Alamu na cigaba da nuna cewa wankin hula yana neman kai jam'iyyar PDP rana a jihar Kebbi a dai-dai lokacin da ake cigaba da tunkarar zabukan gama gari na shekara 2023: 

Kafin wannan lokaci yan watanni kalilan da suka gabata masu sharhi akan al'amuran siyasa a jihar Kebbi sun bayyana cewa har yanzu tsukuni wata kare ba dangane da rikici-rikicin jam'iyyar PDP da kayi a jihar Kebbi, 

Wannan na zuwa ne bayan wani hukunci da kotun daukaka kara a Jihar Sokoto ta yanke na hana tsohon gwamnan jihar Kebbi Sanata Adamu Aliero da tsohon jagoran majalisar dattawa Sanata Yahaya Abdullahi yin takarar kujerun Sanata a zaben 2023: 

Rikicin jam'iyyar PDP a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na zuwa ne bayan komawa jam'iyyar PDP da Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abdullahi suka yi bayan da jam'iyyar ta riga ta kammala zabukan fitar da gwani, 

A hukuncin da alkalan kotun daukaka kara su uku yanke wanda mai shari'a Muhammad Danjuma ya karanta kotun ta yi watsi da daukaka karar inda ta tabbatar da hukuncin kotu na farko, 

Amma kuma Sanata Adamu Aliero ya bayyana cewa bai aminta  da hukuncin ba inda ya bayyana cewa zai kara daukaka zuwa kotu ta gaba, 

Inda shi kuma Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa ya hankura.

Kan haka ana ganin jam'iyar ta doshi hanyar samun matsala ganin yanda jigoginta da za su iya girgiza siyasar jiha a PDP ba za su yi takara ba, da alamu jikinsu zai yi sanyi a harkar siyasar jihar Kebbi.