2023: Al'ummar Bade/Jakusko Sun Raba Gardama

2023: Al'ummar Bade/Jakusko Sun Raba Gardama

Daga Muhammad Maitela.

Masu hikimar magana sun ce: Jummu'ar da zata yi kyau tun daga Laraba ake tantanceta. Haka kuma, "Ba a jayayyar bushiya da mai buzu (agalemi)". Saboda a tarihin siyasar jihar Yobe ba a taba samun dan siyasar da jama'a suka hada kansu wajen tara kudaden aljihunsu domin sayen fam da hidima ga dan takara ba sai ta kan Hon. Sani Ahmed Kaitafi aka fara. Sannan shi ne matashin tilo wanda jama'a suka yi tsayin daka a kansa wajen cewa dolen-dole ko ta halin yaya sai sun tilasta shi ya fito takarar kujerar majalisar wakilai. Domin ya wakilce su a mazabar Bade/Jakusko a zaben 2023 mai zuwa. Saboda haka ya kafa tarihin da shi kadai ya samu wannan tagomashi a tsakanin yan siyasar jihar Yobe.

Haka ta la'akari da dandazon al'ummar da suka yi fitowar dango; kwan su da kwarkwata, inda jama'a suka nuna wa duniya cewa lalle da gaske suke a matsayin nuna kauna da cikakken goyon bayan su ga dansu, kuma matashin dan siyasa wanda tauraruwarsa ke haskawa a sararin samaniyar jihar Yobe, Hon. Sani Ahmed Kaitafi. Wanda a karshen wannan mako (ranar Asabar) da ya gabata ne, a sa'ilin da ya zo gabatar da kansa ga shugabanin jam'iyyar APC a matakin mazaba gundumomi, kana da kananan hukumomin Bade da Jakusko tare da bai wa al'ummar yankin cewa ya shirya domin ci gaba da hidimta musu kamar yadda ya saba- domin yin takarar kujerar majalisar wakilai, kamar yadda suka bukata. 

Bugu da kari, wannan ziyara ce wadda ta shiga kundin tarihi, kuma ta bude sabon shafi na alkiblar siyasa yankin kuma ta kara fito da al'amarin sarari da kore shakkun da ya tabbatar cewa lokaci ne na matashi sabon jini, dan siyasa wanda ya dauki al'ummar sa a gadon bayansa tare da ganin kima da muhimmanci. Ya sake tabbatar da cewa zamani ne wanda al'umma su ka gaji da ragwagen wakilan da suka gaza sauke nauyin da aka dora musu, saboda haka bari su jagoranci sauya alkiblarsu da kansu ta hanyar zabawa kansu mafita da kansu, musamman a karkashin manyan dattawan da al'umma ta shaida da dattaku- shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Lawan tare da Hazikin Gwamnan jihar Yobe, limamin sulhu, Hon. Mai Mala Buni, wadanda kullum burinsu shi ne samun matasa makamantan su Sani Ahmed Kaitafi a harkokin siyasa domin su kasance shugabanin gobe. 

Masu hikima sun ce barewa bata gudu danta ya yi sassarfa, Hon. Kaitafi ya na daga cikin hazikan matasan da al'ummar jihar Yobe ke alfahari dasu, kuma masu basira ta musamman, wadanda kowace al'umma ke bugun kirji da kasancewarsu mamaya-gurbin shugabanin ta. Kana kuma haka abin yake a zukatan wadannan kwararrun shugabanin siyasar jihar Yobe da na ambata farko da ma kasa baki daya, saboda sun koya kuma sun haddace sanin makamar aikin gudanar da shugabancin al'umma daga kowane mataki. Sannan sanin kowa ne cewa kuli-yaumin babban burin Gwamna Buni shi ne gina matasa domin kasancewarsu makomar kowace kasa- gina matasa shi ne kyakkyawan ginin da zai yi tazgaro ba, sakaci kan haka babbar matsala ce ga ci gaban kasa.

Kuma muna iya cewa wannan shi ne kyakkyawan burin da Sanata Lawan da Gwamna Buni suka dade suna dakon kasncewar sa, a matsayin su na iyayen al'umma kuma masu kishin ci gaban al'umma ta hanyar gina matasan da zasu gajesu bisa kyakkyawar turba. Wanda ana iya cewa tun daga wannan rana ce, Sani Ahmed Kaitafi ya fassara mafarkin da wadannan shugabanin ke fata ga al'ummar Bade da Jakusko, jihar Yobe da Nijeriya baki daya. Kuma abin da zai tabbatar hakan shi ne duba da yadda kowanen su ke tarairaya da jan matasa a jikin su. Kuma irin yadda suka ga wannan dan zakin ya girma, musamman gamsuwar da zukatan jama'a suka bayyana na hakikanin gaskiyar daidaiton kauna tsakanin su da Hon. Kaitafi, abin ya burge matuka tare da Allah san-barka. Babu bukatar dogon sharhi ga duk mutumin da ya halarci wannan taron ko idonsa suka gane masa ta kafafen yada labarai da na sada zumunta, zai kara yakini cewa Allah ne kadai ke hada wa mutum zukatan jama'a ba kudi ko wani abin duniya ba. 

Bugu da kari kuma, masana sun tabbatar da cewa Allah ne kadai ya isa ya hada zukata wuri guda ko ya tara wa mutum zukatan dubbai ko miliyoyin jama'a, kuma su kaunace shi, kamar yadda a ranar Allah ya hada dubban-dubatan al'ummar zuwa ga kaunar Hon. Sani Ahmed Kaitafi. Sannan duk wanda ya kalli wannan taron, ya san akwai kyakkyawar fata da annashuwan da ya bayyana mai cike da amincin da ke tsakanin matashin dan siyasa da jama'ar Bade/Jakusko, kuma wannan ya tabbatar da cewa bashi da madadi bisa dogon lokacin da ya dauka wajen sadaukar da duk abin da ya mallaka na lokaci, tunani da dukiya wajen ganin al'ummar wadannan kananan hukumomi a Bade da Jakusko daga aljihun shi, saboda a wannan lokaci ba ya rike da wata kujera ko ofis da aka zabe shi, amma bai gushe ba yana ci gaba da hidimta wa al'ummar. Wanda hakan ya sa jama'a yankin shi suka yi masa abin da ba a taba yi wa wani makamancin shi ba a tarihin siyasar Yobe. 

A hannu guda kuma, ko shakka babu duk wanda ya zauna da Hon. Kaitafi zai gaya maka cewa Allah ya azurta shi da zuciya mai kyau, tausayi, hangen nesa tare da dattaku- baya ga karancin shekarun shi. Masu hikima sun tabbatar da cewa, a kan hangi siffofin shugabanci ga mutum, a lokuta da dama tun yana a shekarun yarinta. Sannan kuma wadannan halaye da siffofin shugabancin sun hada da hakuri, tausayi, bajinta da jajircewa, hangen nesa tare da dattaku, kyauta da karimci. 

Mutanen da suka yi mu'amalar yau da kullum da Sani Ahmed Kaitafi sun shaide shi da mutuntaka, karimci da halin dattaku, baya ga kyauta da jinkai ga masu karamin karfi (ana yi masa kirari da mai hannu duka dama). Har wala yau, jama'ar yankin Bade da Jakusko da sauran wasu yankunan jihar Yobe kowane lokaci suna tuna ayyukan alherin da ya aiwatar ga jama'ar sa, wadanda suka shafi kowane bangaren rayuwa; harkokin ilimi, kiyon lafiya, ayyukan yi da yaki da zaman kashe wando. Ya taimaki manoma da talafin kayan noma, gina masallatan Jummu'a, gina rijiyoyin burtsatse a yankunan karkara da birane domin inganta rayuwar jama'a.

Duk wanda ya nazarci rayuwar manyan yan siyasarmu a jihar Yobe, karfin fada aji da suke dashi dangane da gudanar da mulkin jihar Yobe da ma a kasa Nijeriya baki daya; Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Snata Lawan da Alhaji Tijjani Musa Tumsa, ya san cwa shukan da suka yi ya karfin gaske kuma zai ji a ransa cewa hankulansu zai kwanta cike da alfaharin cewa sun samar da wadanda zasu ci gaba da gudanar da kyawawan ayyukan da suka shimfida wa jama'a. 

A bangaren Hon. Sani Ahmed Kaitafi, tsawon lokacin da ya dauka tare da wadannan masu gidan nashi, tare da suran abokan huldar yau da kullum; duk da Dan Adam tara yake, ba a taba jin kansu da masu gidansa ba, kuma babu wata matsala da ta taba shiga tsakanin su face alheri da biyayya cikin girmamawa tsakanin shi dasu. Bari wannan batu, hatta abokanai da sauran jama'ar unguwa da gari, na kasa dashi, babu abin da yake tsakanin shi da kowa sai fatan alheri tare da Ala-san barka ga rayuwar sa. Bugu da kari, kullum zancen sa shi ne; ta wace hanya zai bi don ya taimaki wani ko ya dasa wani mutum domin ya amfani kansa kuma al'umma ta mora.

Baya ga wacan babbar inuwar mahaifi (Eng. Ahmed Kaitafi), wanda kusan kowa ya san nagarta da dattakunsa a mahaifarsa, hadi da ta wadannan manyan jiga-jigai a jihar Yobe da Nijeriya, halayen mutuntaka da suka bayyana na Sani Ahmed Kaitafi, suna daya daga cikin kinshikin da ya ja hankalin al'ummar mazabar Bade da Jakusko wajen kiran sa ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya. Saboda sun fahimci cewa abubuwa guda uku suna da muhimmanci ace mutum ya tara su a rayuwa; wadanda sune cikamakin samun babban rabo ga Dan Adam, mutum ya samu iyaye na kwarai, iyayen gida madauakak tare da halaye nagari, wanda Allah ya tara masa. Wadanda kowane daya babban arziki ne a sha'anin tafiyar da mulki ko wakiltar al'umma kuma rashin su tazgaro ne ga rayuwa. 

Har wala yau, duk da yake shi Hon. Sani Ahmed Kaitafi bai nemi wannan takara ba, amma jama'a suka yi tsayin daka ta hanyar dattawan siyasar yankin kan ya zo ya wakilce su. Kuma hakan yana daga cikin dalilin da yasa al'ummar wannan yankin suka bukaci Hon. Kaitafi ya fito takarar majalisar wakilai tare da saya masa fam- domin huce takaicin da suke dashi na rashin ingantaccen wakilcin da suka dade suna fuskanta. Sannan kuma abu na farko suna da yakinin cewa Sanata Ahmed Lawan, Gwamna Buni da uwar jam'iyyar APC a jihar Yobe zasu duba halin da yankin ya dade a ciki tare da mutunta zabin al'umma, musamman a matsayin hakan shi ne ginshikin mulkin dimukuradiyya da smun mulki nagari, kana kuma kasancewar karamar hukumar Bade ta dauki kimanin sama da shekaru 12 ba ta rike kujerar ba- ta na hannun Jakusko. Duk da zance na gaskiya shi ne, wannan mazabar majalisar wakilai ta tarayya da ke wannan yankin ta na bukatar canji nagari, musamman idan an kwatamta shi da takwarorin sa a wasu jihohi. 

Kananan hukumomin Bade da Jakusko suna daga cikin yankin da matsalar tsaron Boko Haram ta shafa a fakaice, musamman ta tudadar yan gudun hijira da sauran abubuwan da matsalar ta haifar, sannan yanki ne wanda Allah ya albarkanta da zama kan gabar kogin Yobe, hakan dama ce ga mazauna yankin wajen bunkasa ayyukan noma, kiyo, kamun kifi da sauran albarkatun da ake dasu. Amma sakamakon rashin ingantaccen wakilci a matakin tarayya ya jawo an samu koma baya, saboda gazawar wakilin nagari, al'amarin da ya dada zaburar da kaimin jama'ar Bade da Jakusko wajen samun hazikin wakilin da ya san hanya- sakamakon da ya nuna Hon. Kaitafi ne zai iya aikin, domin tun kafin a zabe shi ya saba; balle kuma ya samu cikakkiyar dama.

Kowace shekara gwamnatin tarayya ta na ware biliyoyin naira domin ayyukan raya mazabun da yan majalisar dattawa da na wakilai a kowane lungu da sakon kasar nan, sai dai kash, ga dukan alamu na Bade da Jakusko sun kasa kai banten su. Wanda ba domin ayyukan raya mazabu da Sanata Ahmed Lawan yake aiwatar wa ba, da yankin ya samu gagarumin gibi ta wannan fannin.

Saboda haka ne ya sanya masu raji da kishin Bade/Jakusko, suka fi mayar da hankali wajen zakulo hazikin mutum mai kishi da bai wa al'umma muhimmanci, kare mutunci da martabar da suka gada kaka da kakanni, kuma a tsarin dimukuradiyya Sani Ahmed Kaitafi ya cancanci shugabanci saboda jama'a shi suka nuna suna bukatar ya wakilce su. Sannan duk wanda ya san ciyon kansa, ba zai taba wasa da diyaucinsa ba- domin 'kwai' a baka yafi kaza a akurki. Kuma 'aci' ba a sayar ba; zakara yafi doki amfani. Sai dai kuma, abin da ya kamata Bade/Jakusko ya kamata su duba shi be: ba a cizon mumini sau biyu a rami daya. Bugu da kari, mai rabon shan duka baya jin kwaba.