Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.
Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar koli kan harkokin addinin musulunci a Najeriya ta ba da sanarwar yau Alhamis 03/2/2022 ita ce daya ga watan Rajab na shekara 1443 bayan Hijirar Annabi Muhammad S.A.W daga Makka zuwa Madina.
Watan Rajab shi ne wata na bakwai a kirgen watannin musulunci, a yankin Hausa ana cewa watan Azumin Tsofaffi, Malammai sun tabbatar da wannan watan yana cikin watanni hudu masu masu Alfarma da falala, kamar yadda Farfesa mansur Ibrahim Sakkwato mni, yayi karin bayani akan muhimmancin watan.
"Watan Rajab zai kama daga faduwar rana yau laraba (daren alhamis).
"Watan Rajab na cikin watanni masu alfarma da daraja wadan da Allah ya ce: "Ka da ku zalunci kawunanku a cikin su. Taubah:36"
"Da'ar Allah da sabon sa duk suna kara girma a cikin wannan wata. Saboda haka mu kula da kanmu.
ze: large;">"Ya Allah! Ka nuna mana karshen wannan watan cikin aminci da lafiya. Ka sa muna ganin Sha'aban da Ramadhan a bayan sa, ka sauwake mana ibada ka kawar mana da aikin Shaidan," a cewar Mansur Sokoto.