Za Mu Ɗauko Sojojin Haya Su Yaƙi 'Yan Ta'adda -- El-rufa'i

Za Mu Ɗauko Sojojin Haya Su Yaƙi 'Yan Ta'adda -- El-rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi barazanar kawo sojojin haya daga kasashen waje domin yaƙar ƴan ta’addan da ke ta'addanci a dazuzzukan Jihar Kaduna, idan gwamnatin tarayya, karkashin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta gaza magance ta’addancin.

El-Rufai, wanda ya zanta da ‘yan jarida jim kadan bayan bayyana wa shugaban kasa kashe-kashen da aka yi a jihar Kaduna da suka hada da harin bam da aka kai ranar Litinin a layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara tare da sace wasu mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba. 
 
Da yake magana da Hausa, El-Rufai ya ce: “Na je na gana da shugaban kasa, kuma na rantse da Allah, idan ba a dauki mataki ba, mu gwamnoni za mu dauki matakin kare rayukan al’ummarmu.

"Idan ta kama mu ɗauko sojojin haya na kasashen waje su zo su yi aikin, za mu yi hakan ne don magance wadannan kalubale."

Sai dai kuma El-Rufai, wanda ya ce shugaban kasar ya tabbatar masa da cewa za a dauki matakin kawo karshen ta’addanci nan da ‘yan watanni masu zuwa, ya bayyana cewa hanya mafi dacewa da za a magance ta’addanci gaba ɗaya ita ce sojojin Najeriya su yi luguden bama-bamai a ɗaukacin maɓoyar ƴan ta'adda a cikin dazuka.
 
Da yake magana kan harin da aka kai a ranar Litinin a layin dogo, ya ce: “Sun zo a shirye kuma sun dade suna shiri kuma sun san taragon da za su kai hari, shine na manyan mutane kuma sunkwashi ma kwasa su ka tafi da su.

“Kuma na dade ina cewa dazuzzukan da wadannan ‘yan fashin ke buya, lokaci ya yi da za mu je can mu jefa bama-bamai duka. A kashe duk wanda ke cikin dajin.

Sai dai idan ba a yi haka ba, wannan matsalar za ta dore kuma tana iya ruguza Najeriya baki daya.