A Tallafawa Mabukata Da Abinci A Watan Ramadan Musamman A Halinda Ake Ciki
Daga Ibrahim Hamisu, Kano.
Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation Amb Auwal Muhd Danlarabawa ne yayi wannan Kira ga Gwamnati da daukacin dukkan al'umma Dan a ciyar da Mabukata a watan na Ramadana
Amb Auwal Muhd Danlarabawa yace Yana da kyau Gwamnati ta ciyar da masu Azumi da dafaffen abinci har ma da raba Danye ga Mabukata duba ga halin da al'ummar ke ciki a wannan lokaci, hakan zai taimaka sosai a samu damar yin ibada tare da yiwa kasa addua.
Danlarabawa, ya Kara da yin Kira ga masu hali da su duba yanayin da ake ciki su rubanya Tallafin da suke bayarwa ga Mabukata hakan zai taimaka kwarai da gaske Kuma zai Sanya kauna a tsakanin su bayan Dinbin lada da zasu samu Daga Allah subhanahu wataala.
Karshe yayi addu'ar samun zaman lafiya a kasa da Kuma jinjinawa kafafen yada labarai bisa gudunmawa da suke bayarwa a kowanne lokaci na zaburar da al'umma dan su ciyar a watan na Ramadana.
managarciya