Gwamnan Kebbi ya baiwa kungiyar kiristoci miliyan 18 su biya bashi

Gwamnan Kebbi ya baiwa kungiyar kiristoci miliyan 18 su biya bashi
Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya ba da tallafi kudi miliyan 18 ga kungiyar kiristocin Nijeriya(CAN) reshen jihar Kebbi ya ba su kudin ne domin su biya wasu basuksuka da suka hada da ziyarar wajen bauta da suke tafiya.
Gwamna ya sanar da hakan a lokacin da yake karɓar shugaban kungiyar kiristocin Rabaran Ayuba Y Kanta a ziyarar ban girma da suka kawo a gidan Gwamnatin jiha a ranar Alhamis.
Haka ma Gwamnan ya ba da kyautar filaye ga kungiyar domin su yi makabarta, ya kuma yi masu alkawali cigaba da tallafa musu a ƙoƙarin da suke da shi na gina sakatariya ta jiha.
Da farko shugaban tawagar Rabaran Ayuba Y Kanta ya godewa gwamna kan shigo da su a cikin gwamnati.
"Ka baiwa kiristoci mukaman siyasa da suka gamsu da su, hakan ya nuna yadda kake tafiyar da al'ummar ka a gwamnati ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba."