Buhari Zai Hana Amfani Da Kalanzir Da Iccen Girki A Nijeriya

Buhari Zai Hana Amfani Da Kalanzir Da Iccen Girki A Nijeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta hana amfani da kalanzir da iccen girki a Nijeriya nan da shekarar 2030.

Buhari ya bayyana gwamnati za ta yi kokari ta hana amfani da su ta maye gurbinsu da gas domin ganin ta magance matsalar gurbatar yanayi da ake fama da shi.

Ya ce, “Gwamnatin Najeriya na sane cewa yawan dogaro da makamashi mai fitar hayaki na jefa kasar cikin barazana a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin daina amfani da shi a matsayin kashin bayan tattalin arzikinsu.”

Shugaba Buhari ya bayyana cewa komawa amfani da gas din girki zai rage gurbacewar iska da kashi 22 cikin 100 a Najeriya zuwa shekara ta 2030, ya kuma taimaka wajen rage sauyin yanayi a fadin duniya.

Ya kara da cewa zuwa lokacin za a yawaita amfani da bas din haya a matsayin babbar hanyar sufuri a Najeriya kuma za a hana kona bolar gona da nufin takaita gurbacewar iska a fadin kasar.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake zantawar da Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ta bidiyo a ranar Juma’a.

Tun a shekarar 2012 Gwamnatin Tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren mai suka fara aikin samar da dokar hana amfani da kananzir da icen girki da nufin maye gurbinsu da gas din girki.

Buhari ya bayyana wa Mista Biden cewa Najeriya ta yi sabbin gyare-gyare ga daftarin dokar da ta gabatar wa taron duniya kan magance sauyin yanayi domin dacewa da zamani.