Wani mutum ya yanka kakansa da baffan sa don yin tsafi
Wani matashi da ake kira Alfa Ahmed, ya yanka kakansa da dan'uwan mahaifinsa a garin Ibadan na jihar Oyo bisa zargin neman kudi ta hanyar tsafi.
Binciken da jaridar The Punch ta yi ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a bayan kasuwar Apete da ke karamar hukumar Ido a ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce Kakan mutumin Kurma ne kafin faruwar lamarin.
Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa majiyarmu cewa " Wanda ake zargin mai suna Alfa Ahmed yayi amfani da yanayin kakan nasa saboda mutumin kurma ne, shima kanin baban nasa bashi da lafiya yayin da lamarin ya faru".
Ana zargin matashin ya shirya amfani da sassan jikinsu ne wajen yin tsafi.
Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, tuni an fara bincike kuma za a yi bayani nan gaba kadan.
managarciya