Yaya Da Ƙanen Tambuwal Sun Bar PDP Sun Koma APC Tare Da Almajiran Zawiya

Yaya Da Ƙanen Tambuwal Sun Bar PDP Sun Koma APC Tare Da Almajiran Zawiya


 
Yaya da ƙanen Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal sun bar jam'iyarsa ta PDP sun koma APC tare da almajiran Zawiyyar dake cikin garin Tambuwal dake jihar Sakkwato.
'Yan uwan na Gwamna Injiniya Kabiru Moyi da Alhaji Habibu Waziri Tambuwal ganin hotonsu tare da dan takarar gwamnan jam'iyar APC ya sanya aka ta yada zancen barin jam'iyarsu.
Shugaban jam'iyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Isah Sadik Acida ya tabbatarwa wakilinmu 'yan uwan Gwamna sun dawo jam'iyarsu kamar yadda aka ga  sun yi zama da dan takarar gwamnansu.
Ya ce "Kabiru Moyi sama da shekara daya muna huldar siyasa da shi da kaina na kai shi gidan Sarkin Yamma tun a lokacin yake tare da mu, ganinsu da ka yi tare da dan takarar gwamnanmu Ahmad Aliyu magana ce ta siyasa sun dawo jam'iyarmu ta APC," a cewar Acida.
Ɗaya daga cikin makusantan Kabiru Moyi ya ce yana ganin ya bar PDP ne domin Gwamna bai taimake shi ba.
Fitar Habibu Waziri tafi ban mamaki ganin yanda yake makusanci ga Tambuwal ga shi kuma babban Darakta(DG)  a gwamnati, ga kuma zumunta dan wa da kane suke, duk da wadannan ya jefar da  tafiyar dan uwansa ta siyasa. Sauyin shekar tasa ya sa almajiran Zawiyyarsu suka bi shi zuwa APCn dukansu kamar yadda wata majiyar ta tabbatar.
Yunkurin jin ta bakin Kabiru da Habibu kan dalilansu na sauya sheka lamarin ya ci tura.