Kotu Ta Tabbatar Da Zaben Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu
A hukuncin da alkalan uku suka gabatar dukansu sun amince da magana guda jagoransu Haruna Mishelia ya ce masu Kara sun kasa tabbatar da zarge-zarge shidda suke kalubanta a gaban kotu.
Ya ce korafin masu Kara kan zargin Ahmad Aliyu da Gobir bai kamata su yi takarar ba domin sun gabatar da takardun bugi, ga matsalar suna da magudin zabe da Kuma sabawa dokokin zabe.
Mshelia ya ce masu Karar sun kasa tabbatar da abubuwan da suke korafi kansu kamar yadda doka ta tanadar Kashi 70 na shedun da suka gabatar ba su shafi Karar ba lamari ne da ya shafi zaben majalisar dokokin jiha Wanda a rana daya aka gudanar da zaben.
Alkalin ya yi watsi da Karar domin rashin cancantarta a tsarin doka.
managarciya