Mi Ya Sanya Bafarawa Cikin Tsaka Mai Wuya?

Bafarawa ya godewa mahalarta taron da aka gudanar a dakin taro na kasa da kasa dake Kasarawa, wanda aka gudanar domin sanin halin da jam'iya take da matakan da ake dauka don samun nasarar jam'iya. Taron Gwamnan jiha Aminu Waziri Tambuwal ya jagorance shi in da ya yi bayani sosai kan shiraruwan gwamnatinsa da warware wasu korafe-korafe da ake yi game da gwamnatinsa.

Mi Ya Sanya Bafarawa Cikin Tsaka Mai Wuya?
Bafarawa


An ruwaito cewa a wurin taron masu ruwa da tsaki da jam'iyar PDP reshen jihar Sakkwato  ta kira a satin nan tsohon Gwamnan Sakkwato  Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce ya shiga tsaka mai wuya, domin yasan dadi da ciyon kujerar Gwamna.
Bafarawa a jawabin da ya gabatar ya baiwa Gwamnan jihar Sakkwato shawarwarin da za su inganta mulkinsa domin samun nasarar tafiyarsu ta PDP.
Majiyar da ta shedawa Managarciya kalmomin Bafarawa ta ce ya yi kalmomin ne cikin mutuntawa da bin hanyoyin da za a fahimci gyara ne ake son a kawo tafiyar ta PDP ya ce Gwamnan ya jingine maganar a yabe shi a yanzu don ba za a yabe sa ba sai bayan ya bar kujerar gwamna don haka ya saurari masu sukarsa don gyara in aka kasa.
Bafarawa ya godewa mahalarta taron da aka gudanar a dakin taro na kasa da kasa dake Kasarawa, wanda aka gudanar domin sanin halin da jam'iya take da matakan da ake dauka don samun nasarar jam'iya.
Taron Gwamnan jiha Aminu Waziri Tambuwal ya jagorance shi in da ya yi bayani sosai kan shiraruwan gwamnatinsa da warware wasu korafe-korafe da ake yi game da gwamnatinsa.